Sashe 85
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga ta rame, kamar kar Nanny ta xo lkci daya khadijah ta watsar da lamarin yaran gaba daya ya koma nanny ce ke masu komai ita sai dai tayi girki tayi bacci, abinda sudais ya guda kenan tun farko but saboda tausayinta da yake kawai ya kyaleta, nanny na xuwa gidan da kwana biyar sudais ya tafi damaturu don duba su Mami don Allah ma yasan yana kewar mahaifiyar tasa, kwana biyu yyi a can ya dawo Abuja bayan ya sanar ma Mami yawancin aikinsa yanxu a Abuja yake yi, ta yi masa addu'a da fatan alkhairi. karfe uku saura na yamma sudais ya shigo gidansa na Abuja, sai dai a waje yyi parking don ya gaji da yawa, babu kowa parlorn sai Ac dake ta aiki da kamshin dake tashi, ya haura sama ya bude kofar Nanny da yan biyu a hankali, suna xaune cikin keken koyan xamansu sai wasa take masu da abun jikin keken suna ta dariya gaba daya, sosai matar ke son su don yaran akwai shiga rai, Nannyn baxata wuce shekara talatin da biyar ba, tana ganin Sudais ta mike tace "Sannu da dawowa yallabai" yace "Sannu" ya karasa cikin dakin yana kallon cute yaran dake ta kallonsa, kyawawan karshe ne yan biyun ga manyan idanuwa ga su farare kal kamar larabawa, da wuya mutum ya kallesu bai kara kallonsu ba, ya rasa ne yasa khadijah ta ki sonsu har ynxu, daukansu yayi one by one yayi kissing dinsu suna masa dariya ya ajiye su ya fita dakin, bude kofar dakin da Khadijah take yyi, ya ganta kwance daga ita sai yar doguwar riga tana bacci, ya kusa minti biyu tsaye yana kallonta kafin ya rufe mata kofar ya wuce nasa dakin, wanka yyi ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya gabatar da sallahn azahar sannan ya kwanta, Nanny ce ta shiga dakin Khadijah ganin har kusan la'asar ba ta fito ba alamar bata san Sudais ya dawo ba, ita duk tunaninta sudais mijinta ne, cike da natsuwa ta tasheta tace "Yi hakuri na tashe ki madam, yallabai ya dawo" da sauri khadijah ta mike xaune tace "Yaushe?" Nanny tace "Tun daxu" Khadijah tace "Toh" Nanny ta juya ta wuce sannan khadijah ta mike ta tafi bayi ta wanke fuskarta ta fito ta dau Hijab har kasa ta sa ta fita, a hankali ta tura kofar dakin sa ta gansa yyi rub da ciki yana bacci, a hankali ta isa kusa da shi ta durkusa tana kallon kyakkyawan fuskarsa, bude manyan idonsa yyi a hankali, ta koma baya da sauri ta fara kame kame, ya mayar da idonsa ya rufe na kusan minti daya kafin ya bude ya mike xaune, murmushi tayi murya can kasa tace "Sannu da dawowa, baka ce yau xaka dawo ba da ka kira da safe" yace "I was thinking sai gobe xan taho" tace "Ya hanya? Ya su mama" Yace "Alhmdllh, ya twins? duk da nasan kilan duk yau baki gansu ba" sauke idonta tayi daga kallonsa jin yyi shiru ta daga kai suka hada ido, wara mata ido yyi, ta yi murmushi tace "Me xaka ci?" Yace "Komai ma" mikewa tayi tace "Toh bari in yi maka" daga haka ta fita ya koma ya kwanta. A hankali watanni suka dinga ja kamar wasa sai ga shi su shureim sun yi wata bakwai, babu inda basa xuwa da rarrafe, wani shakuwa ne ba na wasa ba tsakaninsu da Sudais, ji yake da su kamar ya hadiye su don so, in har suna wasa a Parlor to suna ganin khadijah suke barin wajen da gudu su tafi gun Nannynsu, sai dai ta tabe baki ko tayi tsaki, har lkcn kamanninsu sak na Aliyu barin hancinsu da idanuwa shi sa take kara jin bata son su, ko ina na gidan kayan wasan su ne, don komai sudais ya gani na yara ko da ya fi karfinsu sai ya siyo masu, dakinsu ya koma kamar na siyar da kayan wasa, yau lahadi sudais na xaune garden shi kadai files a gabansa kana ganinsa kasan aiki yake, lkci daya ya rufe files din gabansa ya lumshe ido, for how long xai ci gaba da ajiye khadijah da yaranta a gidansa, har ransa yake jin baxai iya rabuwa da su ba, but duk ranan da Mami ta gano abinda yake aikatawa yasan that day won't be funny, then meye xai yi da xai kasance da Khadijah da yaranta na har abada With his parent consent, bude ido yyi a hankali ya furta abinda ke ransa a ciki "I shud marry her" girgixa kai yyi ya na murmushi lkci daya abinda Yusuf ya gaya masa one year ago a mota ya fado masa. Khadijah na bedroom ita kadai tana ta jiran jin shigowar sudais amma bai shigo ba, ita kanta bata san me yasa take son ya shigo ba, kuma tasan yana can garden, mikewa tayi ta sa mayafinta ta fita xuwa can din ta tsaya kusa da wani flower yanda baxai ganta ba ta dinga kallonsa, kananun kaya ne jikinsa na 3qtr da shirt da bai yi buttoning ba, tsura ma pen din table dake gabansa ido yyi har lkcn yana tunani, kamar ance ya daga kai suka yi ido hudu da Khadijah, dauke kai tayi da sauri, sai kuma ta jiya ta bar wajen ya bi ta da kallo, murmushi yyi ya na shafa kansa don irin kallon nan da Khadijah ke yi masa ko da yaushe dariya yake ba sa, sau tari ya sha kamata tana kallonsa sai ta fuske, shi din ma yana kallonta amma with swags, kwashe files din gabansa yyi don dama ya gaji ya mike ya wuce ciki yana rike da su, sai da ya fara lekawa dakinsu shureim yaga yanda Nanny ta cika masu kayan wasa a gaba suna ta fama, suna ganinsa suka rarrafo xasu taho gunsa, da sauri ya juya ya bar wajen don bacci yake son yi, a tare suka fara kuka yana tsaye har suka fito corridor nemansa yyi murmushi ya durkusa ya daukesu duk biyun amma da kyar tsabar weight dinsu, ya wuce dakinsa da su, ajiye su yyi kan gado ya kwanta suka haye kansa gaba daya ya lumshe ido yace "Yanxu baxa ku bar ni inyi bacci ba" kamar sun ji mai yace suka fara dariya har da kwantawa jikinsa ya rungumesu gaba daya, ganin da gaske baxa su bar sa yyi baccin ba ya dau waya ya kira Khadijah, tana dagawa yace "Plss ki xo ki dau su Shureim basa son inyi bacci" Khadijah bata ce komai ba ya katse wayar, ta tabe baki ta sa Hijab ta fito ta shiga dakinsa karasawa tayi kusa da gadon suna ganinta suka kankamesa sudais yace "Meye amfanin yaranki na tsoron ki" bata tankasa ba ta kai hannu xata dau little sudais ya fasa ihu dan uwansa na taya sa suka rirrike sudais, murmushi kawai sudais yake yana kallon khadijah da ta hade rai tana kallonsu, fixgo shureim tayi ya fashe da kuka a tsorace har lkcn yaki yarda ya sake sudais. Sudais ya fixgota ita ma har ta fada kansa ya daure fuska yace "Ciwo xa ki ji masa" xata tashi ya ki saketa yana kallonta kamar yanda yaran ta ma ke kallonta, murmushi tayi ta xame kanta ta xauna kasa, murya can kasa sudais yace "Tafi basa son daukan naki" kamar sun ji abinda yace suka kara yin lamo a jikinsa, Khadijah ta mike ta nufi kofa sudais ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya lumshe ido a hankali. A ranan da su Shureim suka cika wata goma Sudais ya sa Nanny ta shirya su kamar dai yanda ya saba duk lahadi xa su fita, yanxu kam babu inda shureim bai xuwa da kafafuwansa banda little Sudais da tashi ma wahala yake masa, kaya iri daya nanny ta sa masu as usual, kwankwasa kofar dakin Khadijah sudais yayi, tana xaune gaban madubi tana rubuta a farar takarda jin an kwankwasa kofa ta dauke takardar da sauri xata boye, dai dai nan ya bude kofar, cukuikuye papernta tayi, ya dinga kallonta yace "What's that" girgixa masa kai tayi ba tare da ta bari ta kallesa ba da sauri tace "Bakomai" yace "Uhn, sure?" Kin cewa komai tayi, yace "Toh ki shirya xan fita da twins sai ki raka mu" ta girgixa kai tace "Baxan je ba" yace "Why?" Sai a sannan ta kallesa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ya d'an yi murmushi ya juya ya fita, bude takardar tayi tana duba abinda ta rubuta, a hankali ta linke ta boye sa sannan ta sa Hijab dinta ta fita, har ya sauka parlor da su little sudais, ya juya ya kalleta yace "Ko d'an kwalliyan ma baxa ki yi ba" tace "Ehh" ya tabe baki ya fita tare da yaran ta bi bayan su, driving yake Khadijah na back seat da twins din shi kuma yana kallonsu ta madubi, horn ya ji an yi ya juya, da mamaki yake kallon matar da ta fito daga wani gida a motar ta kafin ya tsayar da tasa motar ya bude ya fito, ita ma ta sauka tace "Aliyu dama kana Abuja?" Ya kirkiri murmushi yace "Wallahi kuwa Mama, ina yini?" Tace "Lafiya lau Aliyu" lekan bayan motarsa ta dinga yi kafin tace "Kar dai kayi aure Hajiya Khadijah bata gaya min ba naga mace da yara a mota" sosai gabansa ya fadi yace "A'a mama, matar abokina ne da yaranta" Tace "Ayyo wajen ka suka xo?" Yace "A'a ajiye su xan je in yi" shi kansa ya san he just sound stupid, yayi saurin cewa "Amma mama kun dawo ne?" Tace "Noo, na xo yin abu ne yau sati na daya, amma ina jin jibi xan koma" yace "Holland din?" Tace "In sha Allah" yace "Toh Allah kai mu mama" tace "Ameen Aliyu, Allah yayi maku albarka" yana murmushi yace "Ameen" daga haka ya koma motarsa har lkcn gabansa na faduwa, Hajiya Rukayya aminiyar Mami ce don childhood frnds ne ma, ita ce ta sa Mami tayi ma Abba magana ya siya masa gida a layin lkcn anguwar na sabo, ita ma kuma a anguwar take amma sai su yi wata da watanni basa Nigeria da yaranta, har sudais ya