Sashe 123
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 7 min read
raya sa" tace "Ameen" kamar ance ta juya taga khaleel ya shigo gidan rike da leda, mikewa tayi da sauri ya karaso har gabanta yana kallonta ya mika mata ledan, ta d'an risina ta karba a hankali tace "Nagode" ya d'an yi murmushi yace "No thanks" daga haka ya juya ya nufi gate, Aliyu ya bi sa da kallo ko kiftawa babu, khadijah tace "Xan wuce ciki sai da safe" mikewa yayi yace "Toh ina yake, I mean the boy? Though ban san sunan sa ba" da kamar khadijah baxata ce komai ba sai kuma murya can kasa tace "Sunansa Muhammad, ana kiransa Shureim, sunan late half dinsa Aliyu ana kiransa Sudais" kallonta yake ko kiftawa babu, ta gyara tsayuwarta tana masa wani kallo tace "Barrister Aliyu... Sunan sa ya ci" daga haka ta juya ta fara tafiya fuskarta daure, murmushi Aliyu yyi ya bi ta da kallo, can yace "Ohk, wait Iman, nagane barrister Aliyu ne ba ni Aliyun ba" tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa inda take yace "Toh yana ina yanxu, I haven't seen him since yesterday" tace "Yana gidansu Dr khaleel" shiru yyi bai ce komai ba, can a hankali yace "Ohk good nyt" daga haka ta juya ta wuce ciki ta rufe kofa. Washegari aka yi sadakan ukun sudais, tun da sassafe Mumy ta taho da su Siyama da frnds dinta biyu, sadakar wainan shinkafa da Kayan flour ta kawo gidan, Ummun khaleel ma ta xo da jikokinta tare da shureim wajajen karfe tara, ita ma wainar ta kawo sai lafiyayyen rice and stew da ta kawo ma khadijah da soyayyen kaji a warmer daban, Karfe sha daya Barrister sudais ya bar gidan kasancewar yana da wani case, ya tura ma khadijah text cewa xai dawo da yamma, karfe sha biyu ummun khaleel ta koma gida tare da su Shureim da yanxu ya saba da yaran sisters din khaleel amma har Ummu ta gaji da amsa tambayar da yake mata na cewa yaushe sudais xai dawo, shi dai a kai sa wajensa, tausayi yaron yake bata don tsakaninsa da Allah yake son ganin dan uwan nasa, a ko da yaushe dai ce masa take soon xai dawo, sai kusan azahar Mumy suka bar gidan, Khadijah ta raka su har gate tayi mata godiya a sanyaye, Mumy ta sa mata albarka sannan suka wuce da yaran nata, kafin dare frnds din Umma suka fara watsewa gidan, Shaheedah ma suka koma Abuja tare da Sadeeq, gidan ya rage daga Khadijah, sai Nanny da Umma da Wata aminiyarta. Bayan magrib khadijah bna xaune kan darduma tana azkar kira ya shigo wayarta, a hankali ta daga ta kai kunne ganin barrister sudais ne, yace "Amira xa ki iya fitowa yanxu plss, am outside" tace "Toh" daga haka ta mike ta fita, sai da ta fara gaya ma Umma sannan ta tafi kofar gida, fitowa yayi daga mota ganinta, yana rike da 3 years old daughter dinsa, Khadijah ta wara ido tana kallon kyakkyawar yarinyar ta xaga inda yake ta karbeta tace "Waow ya sunanta?" Sudais ya jingina da motar yace "Ur namesake, ita ma Amira ake kiranta, na kawo ta ne ta gaida Antyn ta" Khadijah tayi murmushi a sanyaye tuno kiran ta da mahaifiyar yarinyar tayi mata ranan da sudais xai rasu, tana taba dogon gashin yarinyar tace "Naji dadi sosai" Yace "Sure?" Ta kallesa da sauri tace "Eh mana, ko xaka bar min ita" yar dariya yayi yace "In dai kika shigo gidan ubanta ai taki ce ita" Wani murmushin Khadijah tayi bata dai ce komai ba, yana kallonta a hankali yace "Baxa ki shigo ba kenan, xaro ido tayi tace " Ka ji na fada haka?" Yace "Uhmn dont forget who is standing before you" ta dauke kai tana ci gaba da murmushi tace "A barrister" ya shafa kansa yana kallonta a hankali yace "Toh ya k'arin hakurin mu dear?" Tace "Mun gode Allah" yace "Har yanxu shureim din bai dawo gida ba?" Ta gyada masa kai tace "Bai dawo ba" yace "Ohk, ya su umma?" Tace "Suna ciki" kamar warce ta tuna da sauri tace "Sorry na bar ka tsaye mu shiga ciki" yayi murmushi yace "Aa bari in yi ta tsayuwa ta" ta turo baki tace "Allah na manta ne kayi hakuri, mu shiga ciki" daga haka ta nufi gate rike da Little Amira, ya bi ta da ido kafin ya bi bayanta, kan fararen kujerun dake compound din Sudais ya xauna duk yanda tayi da shi ya shiga ya gaida umma ya ki yarda wai sai gobe, tace "Toh bari in kai mata Little Amira ta gani" yace "Toh sai ki bar ta a can ki dawo ke kadai kar in yi rashin kunya gaban daughter na" dariya kawai khadijah tayi ta tafi tare da Amira dake ta waigo Abbanta ya daga mata hannu yana murmushi. umma ta xaunar da ita kan kafarta tace "Maa sha Allah, daughter na mai kyau da ita, Allah ya albarkace ki" khadijah tace "Naga kamar bata magana" Umma tace "A'a don dai bata san mu bane amma wannan ai ta isa tayi magana" fridge khadijah ta nufa ta bude ta dau ruwa da lemo ta daura kan tray ta sa glass cup sannan tace "Umma ina xuwa" Umma tace "Toh sai kin dawo" Har khadijah ta iso gun sudais idonsa na kanta, ta ajiye karamin tray din hannunta ta bude drink din ta xuba masa sai dai bata masa ba tace "Ya aiki?" Ya langwabar da kai yace "Ba dadi, Amira har yanxu you didn't answer my questions..." Ya lumshe ido ya bude yace "Ohk let me leave it this way, you don't want to answer my question" shiru khadijah tayi tana kallonsa, a hankali yace "A lot of things happened after I left you and the boys Amira, na koma damaturu gidanmu tare da Mamina amma gaba daya na rasa kwanciyar hankali, i was always sad then, thinking about you and the twins, hankalin Mami ya tashi a lkcn ta dinga cewa kilan asiri kika min ko kuma aljana ce ke, gashi nan abun na affecting dina, nan tasa aka tayi min rokan Allah, gradually dai na fara kokarin ganin na mance ku, na cire ku a rai na dinga harkokin gabana... saboda ku ko da ina da aiki a Abuja to baxan je ba, gaba daya na daina xuwa Abuja, daga Lagos, kano sai Kaduna and other States nake xuwa amma banda abj, dama ni din ba wai ina da time na yan mata bane, jiddah dai ce ita ma a Holland muka hadu lkcn ina karatu ita kuma tana tare da yayarta dake kasar tare da mijin ta, I never knew ma ashe Mami ta san mum dinta sun yi makaranta daya though it's not as if they are frnds, to dai a haka na fara neman jiddah har aka sa aurenmu ana saura few months bikin mu na hadu da ke ranan na fito daga gida, Amira saboda ke nasa aka daga bikin nan har na kusan watanni shiddah, a kwana a tashi kuma na kara neman a daga cos kin kusa haihuwa lkcn, let me make things brief, at the end fasa auren nayi gaba daya, suka maido min da lefen da na kai all because of you, and happily then Abbana supported me, but bayan rabuwar ki sai gashi na koma mata cos I don't have any option again, at first kamar baxata yarda ba daga karshe dai a cikin wata daya aka daura mana aure, 2 years da aurenmu da jiddah Allah yayi ma Mamina rasuwa bayan tayi fama da kidney problem, though before then duk na mata bayanin yanda aka yi na hadu dake, ban boye mata komai ba, kuma hankalinta ya tashi a lkcn but kawai sai ta maki fatan Allah ya hada ki da dangin mahaifiyar ki, daga nan kuma bata ce min komai ba, and gaskiya a lkcn kusan na ma cire ku a rai na daina damuwa cox I knw surely Allah na tare da ku, amma kullum sai na maku addu'a every blessed day, ba tonan asiri ba Amira ni ba wani jin dadin aure nake da jiddah ba, fitinar ta yayi yawa she is always pestering my life, ko kadan bana son hayaniya yana daga min hankali, bani da rest of mind idan ina gidana, ko irin weekend din nan ma ni na gwammace in tafi office in yi kallo, Amira I need a woman that i will find peace in, I need a better life partner, ina raga ma jiddah ne kawai saboda yarinyar nan dake tsakaninmu, and divorce is totally out if it baya cikin tsarin rayuwata, I need you plss Amira" Khadijah taji kanta ya mata nauyi sosai ta rasa abinda xata ce masa, bata san lkcn da hawaye ya dinga sakko mata ba tana kallonsa, deep down her kuma ta rasa me yasa khaleel ya fado mata.