← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 168

Sashe 66

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read

jin yunwa yanxu" Yace "But you need to take something" shayi yasa Nurse ta hado mata mara xafi, ganin Cup din shayin kadai ya dinga tada mata xuciya har da hawayenta, hankali tashe tace "I said am nt hungry plss" Yusuf dai na tsaye kusa da window yana kallon su, Sudais ya karbi shayin ya hade rai ya mika mata yace "Collect it now, ina ruwan wani da rashin jin yunwar ki" Karba tayi ta runtse ido ta rike breath dinta ta kai baki amma ta ki sha, can ta bude ido a hankali tana kallon sa kamar xata yi kuka, taga yanda ya hade rai yana kallonta, kauda fuskarta tayi tace "Don Allah kayi hakuri Allah baxan iya sha ba amai xan yi" yace "Sha kiyi aman" bata ce komai ba kuma bata sha ba, ta kalli Yussuf taga ya rungume hannu yana kallon su kawai, Nurse din tace "Ki daure ki sha kin ji yan mata" runtse ido ta kara yi bata ce mata komai ba, wani tsawa da ya tsorata ta Sudais ya mata yace "Wa kike tunanin xaki dinga ba wahala" bata san lkcn da ta kai shayin baki ba ta kurba, sauka tayi daga kan gadon da sauri jin amai ya taho mata nurse din tayi saurin karban Cup din hannunta ta ajiye, ta shiga bayi tana amai, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta cire mata hijab ta wanke gun sannan suka fito tana rike da hannunta, bin su Sudais yyi da kallo har ta xaunar da khadijah gefen gado ta kwanta tana maida numfashi, Shi dai Yusuf har lkcn bai ce komai ba, ya karasa gun da nurse din ta ajiye ruwan drip din ya dauka ya fara hadawa, ita ya bar ma ta sa mata sannan ya kalli Sudais yace "Barrister.... I will be on my way now" Sudais ya bi bayansa suka fita. Xa a iya cewa kusan a gidan Sudais ya wuni ranan don da ya fita xai dawo, Nurse din kuma karfe sha biyu ta wuce, duk shigowar da xai yi daki kuma sai Khadijah ta farka daga baccin da take, wani lkcn ya mata sannu, wani lkcn kuma kawai ya juya ya fita. Tun bayan awaran da ta sa ya siyo mata ta samu ta ci kadan bata sake yarda ta ci komai ba don shi dinma damunta yake tayi gashi ta kasa yin aman, Karfe shidda saura ta bude ido jin budewar kofar, shi da Yusuf suka shigo, Yusuf ya mata ya jiki, ta gaishesa, Sudais na kallonta yace "I think Gobe xa mu je can Kaduna..." Sai a snn ta kallesa hnkli tace "Toh" Yusuf yace "Why nt ka bari ta fara samun Lafiya, she's so sick" Sudais ya nufi kofa yace "Noo, she's leaving tomorrow, for how long am I going to keep her here?" sai kuma ya juyo yace "Or is she going to stay here for ever? You knw presently I will be bringing a woman in here...." Daga haka ya fita, Yusuf ya bi sa da ido, can ya kalle Khadijah yace "What's ur name?" A hankali tace "Khadijah" yace "Khadijah are you sure you are nt lying about ur self" hawaye ne ya cika idonta tana girgixa masa kai tace "To God who made me, I didnt lie." Yau din ma nurse din ce ta kwana gidan tare da Khadijah, karfe bakwai da yan mintuna na safe sudais ya shigo gidan, parlor ya xauna bayan ya ajiye flask din hannunsa suka gaisa da nurse din yace "Don Allah ki sa ta shirya anytime soon xa mu kama hanya..." Ruwan xafi nurse din ta sa ma khadijah tayi wanka, ta fito bayan ta yi wankan tana rawan sanyi, nurse din ta ajiye mata daya daga kayan da sudais ya siyo mata dake cikin leda da lotion sannan ta fita, da kyar khadijah ta daure ta tashi ta shirya ta sa Hijab, sai sannan nurse din ta dawo tana kallonta tace "Ki fito yana jiran ki" daga haka ta fita khadijah ta mike a hankali ta bi bayanta, cup din kunun da sudais ya sa aka siyo mata nurse din ta dauka ta bata, amsa tayi tana kallon cikin cup din, can ta dago a hankali ta kalli sudais dake kallonta ta sauke idonta tace "Ina kwana?" Yace "How you feeling?" Ta gyada kai tace "Da sauki." A hankali ta fara shan kunun tana tsoron kar tayi amai, cikin ikon Allah bata ji Aman ba, ta ajiye kusan Rabin cup tace ya isheta, mikewa yyi yace "Ina jiran ku a waje, you help me lock d door pls ga makulli a jiki" ya fadi hakan yana kallon nurse sannan ya juya ya fita, Khadijah ta bi sa da ido yana sanye cikin bakar suit da wando sai farar T-shirt da necktie banda kyalli bbu abinda cover shoe din kafarsa ke yi, nurse din ta kai flask da kunun cup din kitchen sannan ta fito tana kallon khadijah tace "Toh tashi muje" dafa kujera tayi ta mike nurse din na gaba ta bi bayanta har suka fita nurse din ta rufe kofar da makulli ta cire sannan ta tafi gun motarsa Khadijah na bin ta. Yana daga cikin motar ta mika masa ya karba yace "Shigo in rage maki hanya madam" nurse din tace "Toh" ita ta shiga gaban motar khadijah ta shiga baya, sai bayan sun fita gidan ya fito daga motar ya rufe gidan sannan ya koma ya ja motar suka bar layin, dai dai wani junction nurse din ta sauka tana masa godiya, kudin mota ta bata sannan ya ci gaba da tukinsa. Tun da suka fara tafiya khadijah ke jin xuciyarta ke tashi duk ta xama restless, yana lura da ita ta madubi bai dai ce komai ba, bayan wani lkci tace "Amai nake ji plss" yana kallonta ta madubi yace "Amai??" Toshe bakin ta yyi da hannunta da sauri, ya gangara gefen titi ta bude motar da sauri ta sauka ta dinga kwarara amai bakin hanyan, fitowa yyi ya tsaya jikin mota ya rungume hannu yana kallonta, ta gama Aman tana maida numfashi da kyar, bude front seat yyi ya dauko table water ya mika mata ta karba ta wanke bakin ta da fuskarta sannan ta mike kanta a kasa, ya nuna mata front seat yace "Shiga" a hankali ta karasa ta shiga ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga, kasa yyi mata da kujerar ya ci gaba da driving dinsa. Har suka yi nisa sosai a tafiyar bacci take, sudais dake kallonta lkci lkci ya gangara gefen titi yyi parking, suit din jikinsa ya cire ya rufa mata ganin sanyi take ji duk da bai kunna ac ba, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa. Sai da suka shigo traffic a kano ta farka, ya kalleta yace "Xa ki ci wani abu ne?" Da sauri ta girgixa masa kai, yace "Ko xa ki ci apple?" Shiru tayi tana kallon mai hawking apple dake tsaye gefen glass dinsa, ya dau suit dake jikinta ya cire kudi sannan ya mayar ya rufa mata ya sauke glass ya siya apples guda shidda ya ajiye kusa da ita, daya ta dauka ta kai baki a hankali gabanta na faduwa, taji bakin ta ba dadi ta dinga taunan Apple din a hankali tana tsoron kar ta ji amai, har ta ci rabi bata ji aman ba kafin su bar kano har ta cinye biyu daga nan kuma bacci ya dauketa. Khadijah bata sake farkawa ba sai da suka shigo garin kaduna kusan karfe uku, ganin ta tashi yace "Wani anguwa ne gidansu Aliyun yake?" A hankali tace "GRA" bai ce komai ba ya dinga driving a hankali sbda traffic, cikin minti ashirin suka shigo Gra, khadijah ta dinga yi masa kwatance har suka iso dai dai kofar gidansu Aliyu Sudais ya juya yana kallonta.
Chapter 66 · 0% Book details