← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 168

Sashe 142

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 1 min read

yana kallon mai napep din yace "Kayi hakuri xaka kai ni Gra yanxu" Bayan wani lkci khadijah ta fito ya isa gabanta ya mika mata yaron dake bacci ta karbesa tana kallonsa tace "Mun gode sosai" d'an murmushi kawai yayi, can yace "Idan ya ci abinci sai ki basa magungunan sa" tace "Toh" yace "Alryt xan wuce gida a gayar min da Umma" daga haka ya shiga adai daita, mai adaidaitan ya ja suka bar wajen ta bi su da kallo, juyawa tayi a sanyaye xata shiga gida suka kusa cin karo da Nanny da ta amshi Shureim hannunta suka wuce ciki, ruwan xafi Nanny ta hada masu bayi, ta ma Shureim wanka sannan khadijah ta shiga, Umma na ba Shureim abinci ta fito, Umma ta kalleta tace "Ni nasan sai sanyi ya kama yaron nan kawai salon ki ja masa kika tafi da shi tunda kin san lkcn sanyi ne" khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi...
Chapter 142 · 0% Book details