← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 168

Sashe 146

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

gabansa ya mika masa hannu yana murmushi yyi masa sallama, Sudais ya basa hannun shi ma suka gaisa sannan ya kalli khadijah yace "Good evening" tace "Evening ya su Mumy?" Yace "Suna gaishe ki" kallon Shureim yayi yace "Go inside kace baby ta fito ina jiranta yanxu" Shureim ya shiga gidan Aliyu yayi ma Sudais sallama ya koma motarsa yana kallonsu ta ciki, Sudais bai sake cewa komai ba yana jingine da mota har baby ta fito, ta iso gun khadijah tana murmushi tace "Khadijah ni xan koma, ki taya ni yi ma Umma godiya idan kin koma ciki, nagode sosai" Khadijah tace "Toh nima nagode Baby ki gaida min mumy sai na kawo card din, and I will give you a call later" Baby tace "Alryt dear" sallama tayi ma Sudais ta wuce motar Aliyu ta shiga ya tada motar ya bar layin. Ranar Friday kamar yanda khadijah tace ma Baby misalin karfe sha daya ta shirya taje gidansu tare da Shureim don Sudais yace yana da wani case ranan. A hankali ta murda kofar parlorn ta ji a bude, ta shiga hade da sallama, Aliyu ne xaune parlorn tare da Salim yana operating laptop, ya daga kai yana kallonsu, ta sauke idonta ta karaso cikin parlorn, ta gaida Salim sannan ta kalli Aliyu tace "Ina kwana" Yana xaunar da Shureim dake gaishesa kusa da shi yace "Lafiya lau ya gida" tace "Alhmdllh, Mumy fa?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Bata nan, ki jira ta xasu dawo yanxu" tace "Baby fa?" Yace "Tare suka fita" tace "Toh bari in baka sako ka ba Mumy" Ta bude jakarta ta fiddo IV din tana kallonsa ta mika masa, karba yayi idanuwansa a kan content din Invitation card din, a hankali ya dago yana kallonta ko kiftawa babu, bata sake yarda ta kallesa ba tace "You help me deliver it to her plss" daga haka ta sauko da Shureim dake xaune kusa da shi ta juya ta fita daga parlorn yana ce mata shi ta bar sa a gidan, ganin yanda Aliyu yyi still wajen, Salim ya karbi card din don ganin na menene. Gida khadijah ta koma tana ta ma Shureim dake mata kukan bata bar sa gidan ba masifa, tana sauka kan napep din tace "Don uwar ka ba sai ka koma ba tunda gidan dangin uwar ka ne can din" Ta bude jaka ta ba mai napep kudinsa ta wuce ciki abun ta, ya bi ta yana kuka kamar xai tsaga gidan, Ta fi seconds goma tana kallon takalman dake bakin kofar parlorn, can ta bude kofar ta shiga a hankali, Khaleel ta gani xaune parlorn Umma ma na xaune, ta wani hade rai bata sake kallon parlorn ba xata wuce daki Umma tace "Khadijah" tsayawa tayi ta ki juyowa, Jin Umma bata ce komai ba ta juyo a hankali tace "Na'am Umma" Hada ido suka yi da shi, ta sauke idonta tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau" Tana kallon Umma tace "Mun dawo Umma, ba mu sameta ba ma" Umma na kallon Shureim da ya makale bakin kofa yana kuka tace "Shi kuma me ya samesa?" Harara ta balla masa tace "Au kuka kake min har yanxu, nace ka koma gidan koh" a hankali yace "I don't know the road" Umma tace "Me yasa baki bar sa ba" Tace "Mumy fa bata nan, Baby ma bata nan, to ina yake son in bar sa" yana kallonta yace "Wajen Uncle dina mana" Khaleel ya juya yana kallonsa yace "Come over dear" sai a sannan Shureim ya gansa ya taho gun sa da sauri yace "Uncle when did you come?" Khaleel ya xaunar da shi gefensa yace "Today" Murmushi yayi yace "Uncle kun xo da Anty na?" Khaleel ya shafa kansa yace "Sure" tabe baki khadijah tayi ta juya ta wuce daki abun ta, Tana xaune gefen gado tana danna wayarta Umma ta shigo dakin, ta xauna gefen gadon ita ma a hankali tace "Ashe abinda ya faru kenan Khadijah?" Kasa kallonta Khadijah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, sai a sannan ta dinga jin xafin maganganun da Jawahir tayi mata, maganganun suka dinga dawo mata sabo, Umma tace "Ni ban ce kiyi kuka ba, ki share idon ki kije ki samesa ki ji abinda xai gaya maki" cikin rawar murya tace "Ni baxan je ba Umma" Umma tace "Ban isa da ke ba kenan" goge idonta ta dinga yi a hankali ta mike ta dau gyalenta ta fita a sanyaye, tun da ta fito yake kallonta har ta karaso ta xauna kujera ba tare da ta yarda ta kallesa ba, a hankali taji yace "Khadijah" sai a sannan ta daga kai tana kallonsa.
Chapter 146 · 0% Book details