← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 168

Sashe 84

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga wannan rana Khadijah ta daure ta fara koyon yanda xata kula da yaranta tunda Mama suwaiba ta wuce, shi ma din ba a son ranta ba kawai sbda sudais take yi, amma har lkcn ta ki basu nono sai dai madara, Sudais ya san kula da yara har biyu xai mata wahala saboda karancin shekarunta amma ya bar ta a haka to see if kusancinta da yaran xai sa ta hakura ta fara sonsu but kamar kara sa mata kinsu ake, komai xata masu sai tayi complain wani lkcn har da kukanta, bbu abinda ke mata takaici sai irin yanda suke hanata bacci cikin dare wani lkcn, duk da during the day kusan sudais ke masu komai, yayi dedicating time dinsa gaba daya ma twins din kamar mara aikin yi, a ranan da Mami tayi querying dinsa na biyu kan ina yake xuwa baya dawowa gida sai kusan sha biyun dare kuma ya fita da sassafe tsabar confusion yace "Mami ni wlh fa yawanci ina gidana, can nake xuwa" Mami da tayi shiru tana kallonsa tace "Kana gidan ka? To ai xan je gidan wataran" shiru sudais yyi jikinsa yyi sanyi gabansa ya shiga faduwa, kasa bacci yyi darren ranan ya rasa me ya kai bakinsa gaya ma Mami wai gidansa yake xuwa, kuma yasan Mami xata aikata xuwa can gidan nasa din, kafin washegari yayi deciding kawai barin gidan don yasan its not longer safe keeping khadijah and her twins in there anymore, misalin karfe tara na safe ya gama hada duk abinda xai bukata a travelling bag dinsa ya shiga dakin Mami gabansa na faduwa, bayan ya xauna gefen gado a hankali yace "Mami dama ina da wani case da xan yi a Abuja yau, kiyi hakuri sai da xan tafi nake gaya maki" Mami dake ta kallonsa ganin yanayinsa tace "Sai kuma yaushe?" ya sosa keya a hankali yace "Kai Mami ai ina jin daga can ma xan wuce Lagos, aiki da yawa ne gaba na, but in sha Allah soon xan dawo idan na gama, ke dai ki min addu'a" tace "Toh Allah ya tsare, Allah ya bada sa'a" a hankali yace "Ameen Mamina" daga haka ya fita duk jikinsa a sanyaye yayi sallama da kanninsa ya bar gidan a motarsa, driving din yake kamar baxai yi ba, why will he lie such great lies to his Mami, sosai hakan ya tsaya masa a rai, har ya isa gidansa he was not his self, khadijah na kitchen ta ajiye 3months old kids dinta da suka xama lukutaye kamar yan watanni shidda kan kujera a parlor, kiris ya rage little shureim ya fadi daga kan kujera ga d'an uwansa a gefensa, sudais ya karasa da sauri ya daukesa yana kallon kofar kitchen din, fitowa Khadijah tayi jin shigowar mutum parlorn, ya hade rai yace "I've warned u severally ki daina ajiye yaran nan kan kujera baki ji koh" tace "Toh they are just crying ni kuma aiki nake yi, kawai basa son mutum ya ci abinci sai dai su ayi ta basu, kuma ni ba gefen kujera na ajiye sa ba shine ya gangaro da kansa, Allah yaron nan baya ji" ko kallonta Sudais bai yi ba ya dinga kallon shureim dake ta kokarin yi masa dariya ya lumshe ido ya manna masa kiss a baki, Khadijah ta turo baki ta juya ta koma kitchen din ganin banxa ma yyi da ita, kwantar da shi sudais yyi kusa da d'an uwansa da ko motsin kirki baya son yi, shi ko irin wasan nan da kicking legs baya yi, sudais yyi kissing din takwaran nasa yana murmushi yace "You look very lazy Aliyu" dariya yaron yyi masa kamar ya ji abinda yace, Khadijah ta fito kitchen da plate din Irish da kwai, ajiye wa tayi nan parlorn tana kallon sudais tace "Have you breakfasted?" Ya kalleta yace "Noo, we are travelling now" ta buda ido tace "To where?" Yace "Somewhere" shiru ta yi tana kallonsa, yace "Ki gama ki hada kayan twins da naki, kafin ten xa mu wuce" bata ce komai ba, yace "Kin masu wanka" ta gyada masa kai, tun da Dr Yusuf ya nuna mata yanda xata dinga masu wanka shkkn ta iya unlike before da take shaka masu ruwa a hanci. Karfe goma da yan mintuna sudais ya gama sa duk kayan su a booth din mota, komai da yasan xai lalace a gidan ya sa ta xubar, yana rike da little sudais ya rufe gidan ita kuma tana rike da Shureim ya nufi motarsa dake waje, ya bude back seat yana kallonta yace "Get in" shiga bayan motar tayi sannan ya mika mata little sudais da karamar jakar dake dauke da flask na ruwan xafi da table water sai gwangwanin madarar su na Nan, ya rufe motar, ya shiga maxaunin driver, sai da ya shiga filling station ya kara mai a motar sannan suka dau hanya, a hankali yace "We are going to Abuja Amira" kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan wani lkci tace "Me xa mu je mu yi a can?" Bai amsa ta ba yana ci gaba da driving dinsa, ba a dau lkci ba gaba daya yaran suka yi bacci tana rungume da su tana turo baki don duk sun mata nauyi a jiki, bayan few hours shureim ya tashi da kuka sannan little sudais ma ya tashi, sudais dake kallonsu ta madubi yace "Ki hada masu madaran a feeder" kamar xata yi kuka tace "Toh da wani hannun, bayan sun danne ni" murmushi yyi ya gangara gefen titi yyi parking ya fito ya bude back seat din ya shiga, shi yayi making din masu madaran a feeder guda biyu tana kallonsa, bayan ya tabbatar babu xafi ya mika mata daya sannan ya karbi little sudais ya fara bashi nasa ita kuma ta shiga ba Shureim, tsabar cin da yaran suke ko kwana biyu gwangwanin madaran baya masu, shi sa sudais ke siyowa da yawa, bacci little sudais ya koma a hannun Sudais ya mika mata shi ta turo baki tace "Wllh kafana ciwo yake min ni dai" yace "Toh ko in bari kiyi driving din?" Dariya ta yi tana wara ido tace "Ni kuma?" Ajiye mata yaron yyi a kafa kusa da twin dinsa da shima ya koma baccin sannan ya fita ya koma maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da tukin sa. Kafin su kai kaduna su shureim sun sha madaran su ba iyaka, kuma duk sai yyi parking ya taimaka mata, gashi ya hanata baccin da take ta ji saboda yaran hannunta da ta fara xai tada ta ta rike su da kyau, sai kusan karfe shidda Sudais ya isa Abuja ya nufi gidansa dake cikin garin, kai kana ganin gidan kasan an kashe kudi ba na wasa ba, ya bude motar ya fita don bude gate din gidan kafin ya shiga da motarsa, babu abinda babu cikin gidan don haka bedsheet yayi spreading a kan gado a daki ya kwantar da twins dake ta bacci, yana kallon khadijah da tayi laushi alamar duk ta gaji yace "Kiyi wanka kiyi sallah kafin in dawo yanxu" daga ya fita, da yake har sponge da sabulunsu ta dauko, bayin ta shiga bayan ta fiddo su a kayansu da sudais ya kawo dakin tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta canxa kaya ta sa Hijab ta kwanta dai dai lkcn da su Shureim suka tashi, Ji tayi kamar ta kwala ihu ta dinga hararansu kamar xata yi kuka, ganin xa su fara kuka ta mike ta fara hada masu abincinsu hawaye cike idonta, ita dai ta gaji da wahalan da yaran nan ke bata, tana cikin basu feedern ya shigo dakin, tausayi da dariya ta basa lkci daya ganin yanda take hawaye, ya amshi feeders din hannunta yace "Toh tashi ki dau abinci ki ci kiyi kwanciyar ki" kamar jira take ta mike da sauri, tana cin abinci ya karasa basu abincin su ya kalleta yace "Toh baxa su yi wanka ba" hade rai tayi tace "Nima ban sani ba" yace "Amma ke ai kin yi wanka" tace "Toh ai ni da su ba daya bane" mikewa yyi ya tafi bathroom ya hada masu ruwan xafi sannan ya fito yace "Kije kiyi masu" ta mike da sauri tace "Ni wllh baxan iya ba bacci nake don Allah kayi hakuri, dubi fa wahalar da suka dinga ban a mota" tsayawa kallonta yyi kamar yanda yaran nata ke kallonta su ma, ta je can karshen gado ta xauna fuskarta daure ta dauke kai, dukawa yyi kusa da shureim ya fara cire masa kayan jikinsa har ya gama ya wuce bathroom da shi, dariya ta fara yi kasa kasa ganin shi xai masu wankan, bayan wani lkci sai gashi ya fito ya kwantar da yaron da ya wanke ya rufesa da bedsheet sannan ya dau dan uwansa ya cire masa kayan shi ma ya wuce bathroom da shi yayi masa wankan ya fito da shi ya kwantar kan gado, jaka ya bude ya fiddo masu over all gaba daya da powdernsu da man shafawa, khadijah sai boye fuskarta take kar tayi dariya ganin yanda ya sa masu pampers din, shi dai ko kallonta bai yi ba ya hade rai, yana gama shirya yan biyun ya daukesu ya fita dakin ya kai su nasa dakin ya kwantar da su, Khadijah ta turo baki a xuciyarta tace huta roro, ta mike ta rufe kofar da ya bari a bude ta nufi kan gado ta gyara bedsheet din ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. A haka khadijah da sudais suka fara rayuwa a garin Abuja da yan biyunta, sai dai sudais wasn't comfortable staying under the same roof with khadijah ya rasa dalili, gaba daya a takure yake barin yanda ya ga ta saki jiki totally da shi don ma akwai little sudais da shureim, karfe goma na safiya yake barin gidan baxai kuma dawo ba sai yamma, duk khadijah ta rame saboda rainon yaran don ma ba ta shayar da su, wahalansu yyi yawa, da daya ya fara kuka dayan xai cafke duk su rikitata, satinsu uku a Abuja sudais ya sa aka samar masa Nanny don tausayi take basa barin yanda ya
Chapter 84 · 0% Book details