Sashe 86
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 1 min read
kai bakin titi Hajiya Rukayya bata dauke idonta a kan motarsa ba, mace da yara a motarsa kuma yace matar abokinsa, kallon gidan Sudais din tayi kafin ta karasa can da kafa, kwankwasa gate ta dinga yi ko mai gadi xai bude amma shiru, can sai ga Nanny ta fito ta bude gate din, gaisheta Nanny tayi, Hajiya Rukayya tace "Ya kike" Nanny tace "Lafiya lau sai dai Masu gidan basa nan" shiru Hajiya Rukayya tayi kafin tace "Shi da matar suka fita kenan?" Nanny tace "Ehh har da yan biyun" Hajiya Rukayya tace "Toh shkkn" daga haka ta bar wajen da sauri ta wuce gidanta tana tunanin to ko dai karya sudais yyi mata yace bai yi aure ba, tana shiga motarta ta dau waya ta shiga kiran Mami.