Sashe 82
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read
dakin ya bar gidan gaba daya, turo baki tayi ta kwanta can nesa da yaran, a xuciyarta tace to ita ta iya rainansu ne, kawai su yi ta kuka kamar ana mintsilinsu baxa su yi shiru ba. As usual yau ma da daddare hangame baki Khadijah tayi tana bacci suka tashi suna kuka kamar ko da yaushe mama suwaiba ta xo ta kwashe su ta tafi dakinta tana girgixa kai. Washegari da safe Sudais ya dawo gidan, dubu Hamsin ya kawo ma mama suwaiba yace ta tafi kawai, duk da mama suwaiba ita ta fara bukatan hakan amma sai ta ji ba dadi, ta fara tausayin yaran, Sudais yace "kar ki damu mama idan taga babu kowa gidan xata dinga kula da abun ta, kiyi tafiyar ki kawai" Mama suwaiba tace "Toh shkkn, Allah yasa ta gane" Sudais yace "Ameen, amma mama kar ki tafi kina jin haushinta don Allah, ba laifinta bane but xata daina in sha Allah" shiru mama suwaiba ta yi shiru tana tunanin to ko dai iskokai gare ta, can tace "Toh shkkn, Allah ya shiryeta ya yaye mata abinda ke damunta, amma xa mu iya sallama da ita in roketa gafara idan na taba saba mata" Sudais yyi murmushi yace "Toh ki shiga ku yi sallaman mama" mama suwaiba ta shiga ta tada Khadijah nan tace mata xata tafi, Khadijah dake ta kallonta da mamaki tace "Ina xaki Anty?" Mama suwaiba tace "Kauyen mu mana" Khadijah ta xaro ido tace "Toh yaran fa?" Sakin baki mama suwaiba tayi tana kallonta a xuciyarta tace Lallai gaskiyarsa bata da lafiya, a fili kuwa tace "Toh anjima ai xan dawo" daga haka ta fita, suka yi sallama da Sudais bayan ta hada kayanta ta wuce cike da kewan Khadijah da yan biyun. Sudais ya dau yaran ya kai su can dakin da Khadijah take, har lkcn tana xaune, yana shigowa da damuwa tace "Toh wa xai dinga kula da yaran yanxu?" Yana mata wani kallo yace "Uwarsu" daga haka ya fita yana kallon wayarsa dake ring, ganin Mami ke kiransa ya d'an yi jim kafin ya daga, tace "Aliyu ka dawo gida yanxu ina neman ka" bata jira yace komai ba ta katse wayar ya koma dakin Khadijah yace "Xan je gida yanxu" kamar xata yi kuka tace "idan suka fara kuka fa? Ni ya xan yi?" Yace "Sai ku yi tare" daga haka ya fita ta fashe da kuka a hankali tana kallon yaran. Karfi Sha daya saura Sudais ya isa gida, bai yi mamakin ganin set din akwatunan da su Anty Maryam suka kai gidan su jiddah ba a parlor, ba Mami kadai ba yau har Abbansa na xaune parlor da kanninsa gaba daya, Kasa xaunawa yyi ya duka murya can kasa yana kallon kayan yace "Ga ni Mami" Mami tace "Kayan da kace dama su dawo da su ne suka kawo daxu shi yasa na kira ka, sai ka fada mana daga nan kuma ina xa a kai kayan?" Sudais ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, muryar Abbansa ya ji yana cewa "Aliyu duk shekaru na a garin nan kai ma ka taso kaga cewar lafiya nake xaune ban taba samun matsala da kowa ba, to ta dalilin ka ma baxan samu matsala da kowa ba domin kuwa kayi kadan, don haka kar ka sake xuwa min da xancen aure ko yanxu ko ba yanxu ba, dama idan ba dauko ma kai dala ba gamo ba ma har nawa kake Aliyu??" Abba ya kalli Mami da ta hade rai yace "Dubesa fa he is just 27 ne ko 28 ya ishe mutane aure gashi ya xo yana wawanci da sokwanci, ke kina ganin haka ma kisan baxa ayi abun kirki ba Idan aka masa auren, get out my frnd" Sudais ya sauke ajiyar xuciya a hankali ya mike ya bar wajen, Mami tace "Fadan kenan Abba?" Abba yace "Toh me xan ce masa, idan akwai wanda kika san xai yi aure soon kawai ki bada kayan gudunmawa, am nt in support of Aliyu getting married now, ya jira idan yayi 30" daga haka Abba ya mike ya bar parlon, murmushi kawai sudais yake shi kadai a daki, Anty Maryam ta shigo tace "Hankalin ka ya kwanta yanxu?" Da sauri yace "Wallahi Anty" Can nesa da Twins din khadijah ta xauna tana ta kallon yanda suke ta motsi, tsoronta daya ya xata yi da su idan suka fara kuka, kamar sun san tunanin da take taji daya ya fara kuka, Tashi tayi da sauri ta dau waya ta shiga kiran sudais, ya fito daga wanka kenan ya dau wayar ya katse ya kirata, kamar xata yi kuka tace "Wallahi gasu nan xasu fara" yace "Xa su fara me?" Tace "Kuka" murmushi yayi yana ci gaba da goge gashin kansa yace "Toh kiyi breastfeeding dinsu" xaro ido tayi tace "A'a ni dai madara Anty take basu" Yace "Toh sai ki basu madaran ai" hawaye ya cika idonta tace "Yaushe Anty xata dawo toh?" Yace "Ta tafi kenan ai" xaro ido tayi ta juya tana kallon yaran, kamar yasan abinda tayi yyi murmushi ya katse wayar ya fara shiryawa. Haka nan Khadijah ta dinga fama da yaran suna kuka tana kuka, gashi tana ta basu madaran basa sha, nan ko tun madarar safe da Mama suwaiba ta hada masu ne take basu, tun daga bakin kofa sudais ke jin kukan yaran ya shigo da sauri, tana ganinsa ta mike ta fashe da kuka tace "Ni dai don Allah ka tafi da su kar ka sake tafiya ka bar su" ko kallonta bai yi ba ya kwace feeder din hannunta bude baki yyi yana kallonta yace "Amira" tana goge idonta tace "Na'am" ya hade rai yace "Tunda kike kin taba shan shayi me sanyi, me yasa ke muguwa ce" kallonsa kawai ta tsaya yi, yyi tsaki ya dau dayan feeder din ma ya fita xuwa kitchen ya xubar da madarar ya xuba na xafi ya hada wani yyi diluting da ruwan gora ya dawo dakin, daukan little sudais yyi ya mika mata daya feeder yace "Ki dauki Muhd ki basa" ta turo baki ta karba ta dau yaran ta fara basa, tsit yaran suka yi gaba daya, bayan wani lkci ya juya yana kallon khadijah dake kallonsa, sauke idonta tayi da sauri, ya kwace feeder hannunta ganin a hancin d'an yaron ta saita yace "Kallon meye kike min xa ki xuba ma yaro madara a hanci" ta hade rai tace "Ai kai ma naga ka kalleni" shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya kwantar da little Sudais da har ya fara bacci ya karbi Muhd din hannunta a hankali yace "We will call him shureim" daga ido yyi yaga kallonsa take still, turo baki tayi ta dauke kai ta boye fuskarta jikin gado, yyi murmushi ya na ci gaba da ba shureim sauran madaran, har ya kwantar da yaron bata dago ba, ya tsura ma dogon gashinta ido dai dai lkcn da ta dago a hankali yyi saurin dauke kansa tace "Ae na kama ka"