Sashe 56
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliyu ya fi minti goma xaune cikin mota bayan ya iso gida, gaba daya ya rasa me ke masa dadi duniyar, har ya fita kamanninsa saboda damuwa, Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso inda take kallonsa Mumy take cos he looks so sick, shi kam ya kasa dagowa balle ya kalleta, Tace "Abuturrab are you okay, ciwon kan ne har yanxu" ya gyada mata kai a hankali yace "Na sha magani mum da sauki" daga haka ya wuceta ta bi sa da ido, bin bayansa tayi tace "Toh bacci ka je clinic din kake yi?" Bai juyo ba yace "Eh" da damuwa tace "Maimakon ka tsaya gida ka huta Aliyu tunda baka da lafiya, da sai ka kira asibitin ka bada uxurin ka, xa ma ka iya dubata yanxu ko kawai mu wuce asibiti" tsaye yyi bakin kofa ya rasa abinda xai ce mata ya kuma kasa juyowa duk jikinsa yyi sanyi, Cike da karfin hali yace "Xan tafi asibitin da ita likita xa su duba ta a can" mumy tace "Toh kai ma gaskiya a dubaka wani irin ciwon kai ne haka lkci daya tun safe, sanusi sai ya kai ku clinic din" Bude kofa aka riga sa yi Anty khadijah dake tsaye bakin kofar tana kallonsa da kyau tace "Me ya same ka kai kuma, baka da lafiya ne?" Gefenta ya bi ya shiga gidan ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "I am better now" Anty khadijah ta kalli Mumy mamaki shimfide fuskarta tace "Dama baya da lafiya ne Anty fati?" Mumy tace "Tun safe kafin in fita aiki yace min yana jin ciwon kai ban san wani kalan ciwon kai bane haka har yanxu, ni na xata ma baxa shi aikin ba ganin har na fita yana gida" Anty khadijah ta bi bayansa da sauri ganin har ya kai stairs, ta hada har da d'an gudunta har hakan ya ba Mumy mamaki, Tsaye Aliyu yyi bakin kofar dakin ya kasa shiga, ta labe jikin stairs tana jiran ya shiga ita ma ta shiga, a hankali ya murda kofar ya sa kai ya shiga, Tana ganin haka ita ma ta shige, Baby da ke xaune gefen Khadijah da ke kwance da damuwa tace "Yayanmu Iman bata da lafiya she is just crying, and her temperature is very high" hawaye cike idonta take magana, khadijah na jin sunan da Baby ta kira ta bude ido da sauri hade da yunkura ta mike xaune, Aliyu ya kasa kallon direction din, wani sabon kuma khadijah ta saki a raunane, Anty khadijah dai na tsaye kofa tana kallonsu, Aliyu bai iya ya kalli khadijah ba yace "Ki sa ta shirya xa mu je asibiti yanxu" baby tace "Toh" daga haka ya juya suka yi ido hudu da Anty khadijah, tabe baki tayi ta juya ta bar wajen tana cewa "Haka dai aka iya, da yar uwar ka ce ba lafiya ai baxa ka bi ta kan mu ba ma" shi dai ba ce komai ba ya fita. Hijab baby ta ba Khadijah, Khadijah taki sawa tana girgixa mata kai cikin kuka tace "Ni bana son xuwa asibitin, idan nayi bacci I will okay, baxan iya xuwa ba" baby tace "Nooo, ki sa mu tafi don Allah" kin yarda Khadijah tayi hakan yasa baby ta fita sai ga ta sun shigo tare da mumy, mumy ta karaso kusa da ita ta amshi hijab din ta sa mata tace "Kiyi hakuri ki tashi ku je asibitin kin ji, Allah ya sauke" daga haka Mumy ta dago ta, Aliyu dai na tsaye corridor yyi backing kofar, muryar Mumy ya ji tana cewa "Toh ka kai ma Sanusi makullin sai yyi driving din koh" Juyowa yyi xai yi magana amma ya kasa ganinta tsaye tare da Khadijah tana rike da hannunta, Wani mugun tausayinta ya dinga ratsa shi ganin irin karfin halinta cos he was thinking baxata iya fitowa ba, bai yarda sun hada ido ba kamar yanda ita ma kanta ke a kasa, ya fara sauka stairs Mumy ta bi bayansa tana rike da hannun Khadijah baby na biye da su a baya, Anty khadijah dake tsaye bakin kofar dakinta ta saki baki ta bi Khadijah da ido a ranta tace wa yaga boss lady, don kusan kalau take tafiyar ta, nan kuwa daga ita har Aliyun basu san mugun karfin hali take ba, she is in pain all over, only trying her best to be okay, Mumy ta bude bayan motar ta shigar da ita tasa baby ma ta xauna a baya kusa da ita, sanusi ne ya ja motar cos da gasken Aliyu bai jin xai iya tukin, har suka isa asibitin kansa na jingine da kujera, baby kuma na rungume da Khadijah da ta ki bude ido tana kukan xuci. Sanusi na parking Aliyu ya bude motar ya fita, Baby ta fito tana kallon khadijah tace "Iman ki sakko we are at the hospital" A hankali khadijah ta fito cikin motar tana rike da hannun baby, Aliyu ya kalli baby yace "Ku koma tare da sanusi" xaro ido tayi tace "Yaya but Mumy tace in tsaya da ita, wa ye xai tsaya kusa da ita idan anyi hospitalising dinta, look shes very sick fa" irin kallon da ya dade bai mata ba ya shiga yi mata a lkcn, Bata sake cewa komai ba ta shiga motar hawaye cike idonta, Khadijah ta fashe da kuka a hankali tace "Don Allah kar ki tafi ki bar ni" Baby na share hawayen ta tace "He said I shud leave Iman" Aliyu ya juya ya wuce ciki sai ga nurse ta taho ta shiga da Khadijah asibitin, sanusi ya ja motar yana ma khadijah Allah ya sauwake ya kama hanyar gida. Nurse din na rike da hannun Khadijah da ke ta hawaye ta wuce office din Aliyu da ita kamar yanda yyi instructing dinta, baya office din hakan yasa ta fito ta shiga office din kusa da nashi ta samesa xaune, ruwan xafi yasa ta fara kai ma khadijah bathroom dinsa tayi wanka sannan ya bata magunguna da alluran da xata mata, daga haka kuma ya bar asibitin, kulawa sosai nurse din ta bata don ta bata tausayi yanda ta ga jikinta duk da ba ta san takamaiman abinda ke damunta ba, tana mata alluran kuwa bacci ya dauketa nan dakin Aliyu. Aliyu na gidansa har ya samu bacci ya daukesa.... ring din wayarsa ya tashe sa, dubawa yyi da kyar ya ga Mumy ce, ya kai hannu ya daga a hankali ya kai kunne, da damuwa tace "Aliyu ya jikin Khadijah, or shud I come over naji shiru shiru" yace "Noo mum, da sauki anjima sanusi yaje can asibiti ya mai da ta gida" Mumy tace "Kai kana ina?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Na taho nan gida na ne, I need sleep" da mamaki mumy tace "Kuma ka bar ta ita kadai asibiti gashi ka ki barin Baby ta xauna da ita Abuturrab" yace "Nurses din xa su kula da ita mum" Mumy ta d'an yi shiru kafin tace "Toh shkkn, Allah ya sauwake, kai ya jikin naka?" Yace "Alhmdllh am better now" tace "Ohk, amma da ka daure kai ka je ka maido ta gida don Allah, bbu dadi hakan kamar bata da gata, idan baxa ka ba ni in je" yace "Toh mum xan je yanxu kiyi hakuri" daga haka ta yi masa sallama ta katse wayarta. Bayan magrib Aliyu yyi wanka bayan yyi sllh ya canxa kaya ya bar gidan, yana isa clinic din ya kira nurse da ya bari da Khadijah a waya yace tayi mata alluran karshe na ranan ta fito tare da ita yana waje, nurse din tayi yanda yace sannan suka fito tare da Khadijah, bin nurse din da ke rike da hannun ta take kamar iska xae kadeta ta fadi, duk ta rame lkci daya, yana kallon nurse din bayan sun iso a hankali yace "Hope you did all what I instruct you to" nurse din tace "Yes but, I don't knw why she's finding it difficult to walk, kuma tun daxu take complaining chest pain, Dr bashir ya bata magani dai daxu, har da shi ma cikin wa ennan" ta fadi tana nuna masa drugs din da Khadijah xata kai gida, Khadijah dai na tsaye kanta a kasa duk a tsorace take ga xuciyarta dake bugawa da sauri da sauri, Aliyu ya gyada kai yace "Thanks nurse Maryam" Nurse din tayi murmushi ta sa Khadijah ta shiga gaban motar ta rufe tana mata Allah ya kara lfya, tada motar Aliyu yyi ya bar haraban hospital din, har suka isa gida bai ce komai ba, yana lura da hawayen da take yi tana gogewa da Hijab dinta tun bayan da suka fito clinic har ynxu da suke gida, ya gama parking ta bude motar a hankali ta fita, ya bi ta da ido ganin yanda take tafiya har ta shiga gida, sae sannan shi ma ya fito ya rufe motar ya shiga gidan. Mumy dake xaune parlor da su siyama da Anty khadijah ta mike ganin Khadijah tace "Sannu khadijah, ya jikin" Khadijah ta kasa dago kanta tace "Naji sauki Mumy" Anty khadijah sai kallonta take babbu kiftawan kirki, Aliyu na shigowa parlorn ya haura sama, Mumy ta kama hannun Khadijah ta wuce sama xuwa bedroom dinta da ita, da kyar khadijah ta iya cin pepper soup din da mumy ta mata, duk bakin ta babu dadi, a nan dakin bacci ya dauketa. Cikin dare misalin karfe biyu xaxxabi ya kuma rufe ta, dakin Aliyu Mumy ta shiga ta samesa xaune kan darduma ta xauna gefen gado ta jira ya sallame sallahn da yake da damuwa tace "Aliyu har yanxu fa jikin Iman" yace "Xaxxabin kuma?" Mumy tace "Ehh dama" yace "Mumy to ta kara shan drugs din..." Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Toh shkkn" sannan ta mike ta fita, magungunan ta sake bata ta rufe ta da duvet sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauketa. Da safe tea Khadijah ta sha bayan mumy