Sashe 77
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read
bata ci ba, Mami dake xaune ta sa shi gaba da jira har ya gama cin abincin sannan tace "Kun yi waya da jiddah xaka dawo yau ne?" Girgixa kai yyi duk da faduwar da gabansa yyi a hankali yace "Aa mun ma kwana biyu ba mu yi magana ba, fushi take ai da ni" Mami tace "Toh wasa wasa gashi har watanni kusan shidda da kace a daga biki yyi, yanxu kuma ya ake ci" kasa kallonta yayi ya fara kame kamen rufe warmers din abinci, strictly tace "Magana nake ma ka Aliyu" da kyar ya dago ya kalleta yace "Toh Mami a sa bikin nan da wata daya xuwa biyu in sha Allah" wani kallo ta watsa masa tace "Me sati biyu ko uku yayi da har sai an kai wata biyu kuma?" Ya shafa kai yace "Dai dai wannan lkcn xan koma UK kuma xan jima sosai kafin in dawo kinga kawai ana bikin a lkcn sai mu tafi tare da ita" Mami tace "Allah ya kai mu, xan ma Abbanku bayani" yace "Nagode Mami" daga haka ya mike yace mata xai kwanta ya wuce bedroom dinsa. Yana shiga dakinsa khadijah ya kira, tana dagawa yace "Kin gama cin abincin?" Turo baki tayi tace "Na koshi" yace "Baki ci ba kenan?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Me kike yanxu?" Tace "Na kwanta" yace "Tashi ki je ki dau abincin ki ci idan ba haka ba baxa ki ganni gidan nan ba for plenty days" tashi tayi xaune da sauri tace "Ni ban ce baxan ci ba" yace "Toh je ki ci" ta mike da kyar tace "Toh" yace "Idan kin gama ki kirani" gyada masa kai tayi kamar yana ganinta ya katse wayar. Sosai ta ci abincin ta hada har da wanda ya dibar ma kansa, tana gama ci ta dau wayar ta kirasa, sai da ya kusa katsewa ya daga, jin muryarsa tace "Bacci kake" a hankali yace "Yea, kin gama cin abincin?" Tace "ehh na cinye" yace "Good Mami" murmushi tayi tace "Toh kayi baccin, byee" murmushin shi ma yyi ya katse wayar. Xuwan Yusuf gidansu da daddare ne saving grace dinsa don da shi da fita kuma sai gobe, bayan Yusuf ya gaisa da Mami suka tafi dakin Sudais yana tambayar sa ko yayi ciwo a UK ne don ya rame sosai, bayan kusan minti talatin Yusuf yace xai tafi suka fito tare da sudais da yace ma Mami xai rakasa, sai da suka shiga mota Yusuf yace "Kaje ka duba mai cikin ka?" Sudais ya hade rai yace "Mai cikina kuma" dariya Yusuf yyi yace "Toh ai kusan baka da banbanci da uban yaran, kai ma uba kake a gare su kama fi sa xama masu uba kan ubansu" tsaki Sudais yyi bai ce komai ba, Yusuf yace "But don Allah Sudais da yau ko watarana xaka ga uban unborn babies din nan me xaka masa?" Sudais yyi wani murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "I won't even look at him twice yaran da xata haifa sun ishesa" Yusuf yace "What if ya xo wataran yayi claiming yaran fa?" Wani kallo Sudais yyi masa baki bude, can yyi wani dariya yace "Wllh wllh I will sue him, sai na sa yyi shekaru da dama a gidan yari" Yusuf dake driving ya wara ido yace "Tohhh, kenan yaran ka ne ba nasa ba" Yusuf na dariya ya kare maganar, Sudais yyi banxa da shi, Yusuf yace "Toh why not bayan ta haihu ka aureta kawai Sudais" juyawa Sudais yyi yana kallonsa da wani expression, can ya dake yace "Ko saboda me?" Yusuf yyi murmushi yace "Saboda ka ji dadin ci gaba da kula da ita da yaran da xata Haifa kwanan nan, kasan a yanxu kai ne ubanta kai ne uwarta, i mean kai ne gatan ta, don haka sai ka ci gaba da xama gatan nata har karshen rayuwarta, nan da shekaru biyu kai ma ta haifa maka naka yan biyun ba na wani ba"