← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 168

Sashe 157

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read

din har suka hau saman titi, kamar ana tilastata tace "Wani pharmacy?" Gaya mata yyi idanuwansa a kan titi, kira'ar sheikh Sudais kadai ke tashi a motar in a very low tone, yace "Who taught you how to drive" Bata ce komai ba har suka iso pharmacy din, sai a sannan ta kallesa a takaice tace "A Good Samaritan taught me" Bai ko kalleta ba ya bude motar yayi wucewarsa, ta bi sa da wani kallo, Shureim yace "Anty, Uncle ba shi da lafiya koh" Bata ce masa komai ba, Bayan kusan minti goma Aliyu ya fito rike da ledan drugs ya shiga motar, ganin hanyar da ta dauka, yana kallonta da kyau yace "Ina xa ki je?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Xan je gida in dauko ma Shureim wears dinsa" "Noo, mu wuce gida, xan je da kaina in amso masa ba sai kin je ba" A hankali take ta tafiya da motar shi dai bai kara ce mata komai ba, can ta turo baki ta dau hanyar gida... Tana gama parking ya bude motar ya fita ya bude back seat ya fiddo Shureim suka wuce ciki ta bi su da kallo, Babu kowa parlorn da ta shigo, ta ajiye makullin hannunta ta wuce kitchen, Cup din tea ta hada ta fito ta haura sama, bude kofar dakinsa tayi ta gansa xaune yana ballar drugs shureim sai surutu yake masa, ta ajiye masa shayin gabansa ta fita, dakinta ta shiga ta kwanta, Bata san lkcn da bacci ya dauketa ba kawai taji hannu a fuskarta ta bude ido a hankali, lkci daya ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace "What?" yace "Kin yi baki downstairs" Ta d'an buda ido tace "Su wa?" Ya mike yace "Suna jiran ki" daga haka ya nufi kofa tace "Shine baxa ka turo Shureim sai ka xo kana wani taba min fuska" har ya fita bai juyo ba balle yace komai, tashi tayi ta gyara daurin dankwalinta ta bi bayansa, Tsaye tayi stairs din karshe tana kallonta ko kiftawa babu. Suka hada ido da Khaleel dake jujjuya makullin motar hannunsa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ta karasa shigowa parlorn kanta a kasa, haka kawai taji wani mugun kunyarsa take ji, ta xauna kan kujera taki kallon Jawahir, Khaleel yace "Good afternoon khadijah" Ba ta dago ba tace "Ina yini" ya d'an yi murmushi yace "Lafiya lau, how are you" Bata ce komai ba, Jawahir tace "Ya gidan khadijah" sai a sannan khadijah ta kalleta, Jawahir ta sauke idonta a hankali, Khadijah tace "Alhmdllh" Khaleel yace "Ta ce in kawo ta ku gaisa...." Khadijah tace "Toh nagode" Jawahir tayi kasa da murya tace "Khadijah I am sorry about what transpired between us recently, kiyi hakuri ki yafe min" D'an murmushi khadijah tayi tace "Ae ya wuce" Aliyu ya dawo parlorn ya wuce Fridge ya dauko masu drinks ya ajiye, Khaleel dake ta kallonsa ganin ramar da yayi yyi yar dariya bai dai ce komai ba, Murmushi Aliyu yyi yana shafa kansa, Khaleel yace "Ina Shureim?" Aliyu ya xauna kujera yace "He slept off minutes ago" Khaleel yace "Alryt then, dama madam na kawo, I think we will be on our way now, but before then Ina son xa muyi magana da kai..." Aliyu ya mike yace "Alright" a tare suka fita parlorn, Jawahir ta dawo kusa da khadijah tace "Da gaske kin hakura khadijah?" Khadijah na wasa da xoben finger dinta tace "Sure ya wuce" Shiru Jawahir tayi a ranta tana imagining abinda su Ummanta suka ce, khadijah ta dago suka hada ido, murmushin karfin hali khadijah tayi ta sauke idonta kasa, haka suka ta xaune shiru a parlorn har Aliyu ya dawo yana kallon Jawahir yace "Yana jiran ki waje Madam" Mikewa tayi ta ma Khadijah sallama shi ma tayi masa sanann ta fita, Khadijah ta tashi tana tabe baki ta wuce sama ya bi ta da kallon gefen ido. Da daddare ta fito wanka tana shafe shafenta Aliyu ya shigo dakin, ta xaro ido tace "Noo!! you can't just come in without...." Kashe wutan dakin yayi ta xaro ido sauran maganan suka makale, yana daga inda yake a tsaye yace "Drugs da kika amsa hannun Shureim daxu, where is it?" Tace "Ka tafi xan kawo maka" a d'an fusace tayi maganan, yayi murmushi ya tako a nutse har inda take, duk da duhun dakin hakan bai hanata ganinsa ba ta dinga komawa baya a tsorace tace "Aliyu meye haka..." Xata gudu ya rikota sai jin ta tayi jikinsa, lkci daya jikinta ya dau rawa ta dinga kokarin kwace kanta amma yaki saketa, Babu abinda ke mata yawo a memory dinta sai incident din Shekaru bakwai da suka wuce, lumshe ido yyi jin yanda ko ina na jikinta ke rawa, murya can kasa yace "Ki gaya min abinda ke xuciyar ki game da ni Iman.... Tell me what u are thinking of me" Ta fashe da kuka tace "I beg you ka sake ni, you are making me...." Bai bari ta kai karshe ba ya hade bakinsu..... Bai xame ko ina da ita ba sai kan gado, ta kwace bakinta jikinta na bari tace "Nooo plss Aliyu, wllh ka bari bana so.... Kana son xuciya na ya fara min ciwo ko" Murya can kasa yace "I will cure it..." Toshe bakinta yayi jin xata fara masa ihu, Sallamar Shureim bakin kofar dakin ya sa shi saketa da sauri, da ta samu ta sauka kan gadon bata xarce ko Ina ba sai bayi ta rufe kofar jikinta na 6ari, Aliyu ya mike tsaye yana kallon kofar ya kunna wutan dakin sannan ya bude, Wayarsa Shureim ya mika masa yace "Uncle Mumy tana kiran ka tun daxu" Ya amshi wayar yace "Are you done with the game?" Girgixa masa kai yayi Aliyu ya kullo mata kofarta yana rike da hannun yaron suka koma dakinsa, Xaunawa yayi gefen gado yayi dialing number Mumy, bayan ta dauka suka gaisa tace "Ya Iman da Shureim?" Yace "Suna lafiya mumy" tace "Maa Sha Allah, Aliyu if it's okay by you gobe ku shirya don Allah ku je Zaria duba Anty khadijah, duk da ina jin nan da kwana biyu xa a sallameta, Amma ya kamata ku je can din Koh" yace "In sha Allah Mumy" Mumy tace "In ji dai ba matsala" ya lumshe ido ya bude don har sannan bai gama dawowa daidai ba yace "Babu Mumy ga Shureim ku gaisa" daga haka ya mika ma shureim waya ya mike ya shiga bathroom. kasa bacci yayi gaba daya daren ranan sai juye juye yake, a bangaren khadijah kuwa da kyar bacci ya dauketa don duk a tsorace yake duk da ta sa ma dakin makulli....
Chapter 157 · 0% Book details