← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 168

Sashe 144

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

kofar gida Iman" khadijah ta mike xaune tace "Ohk ga ni fitowa" katse wayar tayi tana kallon Umma tace "Umma ta iso bari in je in shigo da ita" Umma tace "Toh sai kin dawo" mayafinta ta yafa ta fita xuwa kofar gida, fitowa baby tayi daga mota ganinta ta karaso da sauri ta rungumeta tace "Khadijah..." Khadijah tayi murmushi tace "Baby ya su Mumy" Baby tace "Suna gida, sun ce a gaishe ku" Khadijah tace "Ayya, Ina amsawa" Aliyu ya fito daga motar yana kallonta yace "Ina Shureim din?" Tace "Yana ciki" ta kama hannun Baby tace "Mu shiga ciki" Baby ta kalli Aliyu tace "Toh yayanmu nagode sai anjima" khadijah kawai yake kallo yace "Ki kawo min Shureim din mu je gun Mumy su gaisa" ba tare da ta juyo ba tace "Toh" Da fara'a Umma ke ma baby sannu da xuwa, Khadijah ta kama hannun Shureim bayan ta dauko masa takalminsa tana kallon Umma tace "Umma xai je su gaisa da Mumy wai" Umma tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ta fita da shi, Aliyu ya kama hannunsa yana kallonta yace "Gobe xan koma Iman" ta kallesa tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen" har xata tafi ta juyo tace "Amma plss kwana baby xata yi koh?" Yace "Ban sani ba, ki tambayeta" tace "Tohm" daga haka ta wuce ciki bayan tayi ma Shureim dake daga mata hannu murmushi. Khadijah ita kanta bata san xata sake da Baby haka ba, closeness dinsu na da kawai take tunawa da irin halaccin da baby tayi mata a gidansu, hira kawai suke tana ba baby labarin abubuwan da suka faru bayan ta bar gidansu, tun baby na kallonta cike da tausayi har ta fara kuka ba tare da ta san tana yi ba, Khadijah ta xaro ido ta fashe da dariya tace "Kuka Kuma baby, toh an gama labarin" baby na share idonta a sanyaye tace "Don Allah ki ci gaba Iman, mara Imani ne kadai baxai xubda hawaye ba a labarin nan naki..." Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Baby na ci gaba da share hawayenta a sanyaye tace "Ki ci gaba plss Iman" a hankali khadijah ta ci gaba da bata labarin har karshe, kuka kawai baby take khadijah na kallonta, Baby tace "Don Allah Iman ki yafe ma yayana plss" Khadijah tayi murmushi tace "Ba dole in yafe masa ba Baby, na yafe masa tuntuni, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle beings" A hankali baby tace "Allah saka ma barrister" shiru Khadijah tayi tana kallonta, can tayi murmushi a hankali tace "Ai shi xan aura baby" kallonta Baby take da mamaki tace "Yaushe?" Khadijah tace "In less then three weeks ne bikin" A sanyaye baby tace "Shine baki sanar mana ba Iman, haushin mu kike ji har yanxu koh?" Khadijah tace "Ayya ba haka bane, kin ga jiya muka dawo ai, dama nufina idan na dawo in kai ma Mumy kati" Baby tace "Ya Aliyu ya sani?" Girgixa mata kai Khadijah tayi, Baby tace "Toh Allah kai mu lokacin, ya sanya alkhairi, Amma barristern a nan garin yake?" Khadijah tace "Ehh nan yake, ae kin san sa" Baby tace "A'a ban san sa ba" Khadijah tace "Ranan da muka je gidan ku ai tare muka je da shi" Baby tace "Ai su biyu ne ranan" Khadijah tace "Ai anjima xai xo sai ku gaisa" Baby tace "Allah ya kawo sa" khadijah ta dinga lallaba baby ta kwana gidan ganin ta fara cewa yamma yayi, baby tace "Ae ban ce ma Mumy xan kwana ba" khadijah ta marairaice tace "Plss baby, kinga ko frnds bani da, am always lonely, xan ce Umma ta Kira Mumy tace xa ki kwana" Bata sake sauraren baby ba ta fita ta sanar ma Umma sannan ta sa mata number mum din su Aliyu a wayarta ta kira ta, tana sawa ta fita ta dawo dakinta gun baby tana murmushi tace "Toh yanxu Umma xata kirata" Babu yanda baby ta iya haka ta hakura xata kwana gidan. Bayan sun idar da magrib suna xaune daki baby na bata labarin halin da iklima ke ciki duk jikin khadijah yyi mugun sanyi, ringing din wayarta yasa baby tayi shiru, dagawa tayi ganin Barrister ke kiranta bayan sun gaisa yace "Am outside dear" murmushi tayi tace "Toh ae shigowa xaka yi"
Chapter 144 · 0% Book details