Sashe 41
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 3 min read
baby ta ci duka gun Aliyu ko kallon banxa bata sake ma khadijah ba, sai ma note da take bata wani lokacin ta kwafar mata na boko ita dai Mumy bata ce masu kala don kuwa rubutun khadijar ma ya fi na baby kyau, har assignment khadijah na kwatanta yi ma baby, su siyama dama ba wani interacting suke da ita ba, don haka babu ruwansu da ita, A yau da ta cika sati biyu ne mumy na bedroom dinta da yamma Aliyu ya shigo, Gaisheta yyi tace "Halan ka fita nyt duty ne?" Yace "Tun three days back yanxu morning xuwa yamma nake yi" tace "Ohk, kun yi waya da Abbanku" Aliyu ya shafa kansa yace "Ehh ai gobe xai taho in sha Allah" tace "Nima haka yace min daxu" yana fiddo wayarsa a aljihu yace "Wai yaushe Anty xata dawo mumy?" Mumy tace "Toh nima dai ban sani ba wllh, amma jiya da ta kirani kamar akwai damuwa kilan su Iklima na cikin wani hali...." Yace "Toh Mumy wai me yasa iklimar baxata dawo nan gidan ba, su Ahmad maxa ne bbu damuwa sosai amma ita macen da ta dawo nan" Mumy tace "Ai ubansu baxai yarda ba ne matsalan sai dai ta taho da ita ba tare da ya sani ba" Aliyu ya girgixa kai yace "Allah ya kiyaye" mumy tace "Ameen dai" Shiru yyi bai sake cewa komai ba, Mumy tace "Ya aka yi kamar kana son yin magana koh?" Murmushi yyi don sure yasan mum dinsa ta gama karantarsa gaba daya, yana facing dinta yace "Mumy dama ba komai bane a kan Mai sunan Anty ne" tunda khadijah ta shigo gidan bai taba kiran sunanta ba saboda Anty khadijah, Mumy ta kallesa da sauri tace "What about her?" Yace "Noo, kawai mum naga da ki taimaka a sa ta a boko..." Katse sa tayi tana kallonsa da kyau tace "Ko saboda me?" Ya d'an bude ido yace "Noo Mumy naga kawai she isn't an illiterate, its just anyi depriving dinta right dinta ne, from all indications she was born with a silver spoon, you knw... it's just condition mum, ina tausayinta ne wllh, kin dai ga har coaching Baby tana kokarin yi, she is very intelligent, Allah will reward you idan kika taimaka mata mumy" murmushi mumy tayi tace "Kasan me Ali?" Ya girgixa kai da sauri yana kallonta, strictly tace "Abuturrab ko da wasa, I mean ko ba a cikin hankalinka ba, kayi making mistake din ce min kana son yarinyar nan wataran I will show u my other side, because it will and will neva be possible, that is just it" da mugun mamaki yake kallonta, a hankali yace "Sonta kuma mum?" Ta gyada kai tace "Yes" yyi shiru na few seconds kafin yace "Mai ya kawo wannan xancen mumy?" Ta hade rai tace "Kai ka kawo sa, for I see no reason har xaka damu In sa ta makaranta kai ka kawo min ita gidan?" Ya girgixa kai kawai, tace "To be careful, yes xan sa ta makarantar boko amma wllh wllh ko a mafarki ka cire ran akwai aure tsakanin ka da yarinyar nan, period" Ya kalli Mumy a hankali yace "But.. Ko saboda me" strictly Mumy tace "Hakan nake so ya kasance, or are you querying me" yace "Amma mumy ni ai ba ce maki nayi ina son ta ba, boko kadai nace ki sa ta for the sake of Allah, meye ma xai sa kiyi tunanin nan mumy, ni kuma in rasa warce xan ce ina so sai karamar yarinyar nan? Wallahil azim ban taba kawo hakan a raina ba, gaskiya I am nt happy mum" daga haka ya mike ya fita a dakin.