Sashe 118
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 2 min read
ya ki, haka umma ta tafi ta bar sa. Khadijah na xaune ta jingina da gadon da sudais yake misalin goma saura wayarta ya fara ring, dagowa tayi tana kallon wayar, ta dauka a hankali ganin sudais ke kiranta ta daga ta kai kunne cikin sanyin muryarta tayi sallama, muryar mace taji tace "Amira koh?" Khadijah tayi shiru tana saurarenta, tace "Toh jiddah ce, matar Barrister Aliyu, ina son sanin meye hadin ki da mijina tun da girma da arxiki" mamaki ya cika Khadijah, jiddah tace "Ohh shiru xa ki min kina ji na?" Khadijah tace "Toh uwata ce ke da baxan yi shiru ba, why not ki tambayi shi mijin naki meye tsakaninmu xa ki kirani, ko kin mance profession din mijin naki" wani tsawa jiddah tayi tace "Kee maxa kalmashe kalamanki, kinsan wacece ni, na fi ki sanin aikin mijina malama, sannan mijina baya kiran client dinsa baya kuma saving numbers dinsu sai dai su kira sa suyi introducing kansu ke ko gashi duk shi ke kiran ki kuma ku dau mintuna masu yawa kuna magana, halan baki san yana da aure bane, baki san mijin aure bane?" Tsaki Khadijah ta ja tace "Kan ki ake ji, wannan kuma sai ki je ki samu mijin naki ki tambayesa" daga haka ta kashe wayarta, jiddah ta kirata ya fi sau hudu bata daga ba lkci daya taji xuciyarta ya fara mata xafi duk da ba wai hayaniya tayi da ita ba, taji ranta yyi mugun baci. Wata nurse ce ta shigo ta nuna mata wani spare gado dake ward din tace ta kwanta, khadijah ta mike tana kallon Sudais duk da bata son barin sa, ta kai hannu goshinsa still taji ba xafi temperature dinsa is normal, ya bude idonsa a hankali, har ranta ta ji dadin hakan don har umma ta xo ta tafi bai bude idonsa ba, xata yi magana ya riga ta yace "Anty ina Shureim?" Tace "Yana waje tare da uncle" ya bata fuska yace "Me yasa ya tafi?" Ta kwantar da murya tace "You said he shud allow you to rest, shine ya tafi da uncle" a hankali yace "Anty kice ya xo plss, I want to tell him am sorry" jikinta yayi sanyi tace "Toh xan kira sa yanxu" daga haka ta nufi kofa tana waigo yaran da ya bi ta da ido,