← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 168

Sashe 88

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami na kallon Aliyu da wani expression tace "Aliyu??? is this the life you chose for ur self? Is this the home training I gave to you" Sudais ya sauke kansa daga kallonta lkci daya jikinsa yyi sanyu ya sauko downstairs a har sannan yana rike da yaran, a hankali yace "No Mami, I didn't choose this life for my self...." Katse sa ta yi cikin tsawa tace "Aliyu ka fada min wacece yarinyar nan? Who is she? Meye hadin ka da ita?" Ya hadiye abu da kyar yace "Mami... Mami ba lallai ki yarda da abinda xan ce maki ba, but Mami ki kira Yusuf xai gaya maki wacece ita kilan shi ki yarda da shi" wani mugun kallo Mami ta dinga yi masa xuciyarta na tafarfasa tace "In kira Yusuf? saboda ina tsoron ku? To bani da wannan lkcn, Aliyu dama abinda ka dawo yi a Abuja kenan? Mace ka dauka ka ajiye gida ku ke rayuwa tare.... Wa iyaxubillah" Hajiya Rukayya tayi saurin dakatar da ita tace "Haba, ki sauraresa tukun Hajiya" daga haka ta mayar da dubanta kan sudais tace "Ka gaya mana wacece ita Aliyu" Sudais ya kalli khadijah da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta, rasa abinda xai ce yyi duk jikinsa yyi mugun sanyi, Hajiya Rukayya tace "Toh bani number Yusuf din, ni xan kira sa" Mika masa wayarta ta yi ya amsa ya sa mata number Yusuf yana fara ring Hajiya Rukayya ta karba, Yusuf na dagawa Mami ta karbe daga hannun Hajiya Rukayya, daga daya bangaren Yusuf yayi sallama, Mami ta amsa tace "Yusuf kana ji na?" Shiru yyi jin kamar muryar Mami, a fusace tace "Ba da Yusuf nake magana ba" Yusuf ya kwalalo ido yace "Ehh ina nine mami, ina kwana," bata damu da amsa gaisuwarsa ba tace "Yusuf ka gaya min wacece yarinyar da Aliyu ya ajiye gidansa da yara" Sai da gaban Yusuf ya fadi ya mike daga xaunen da yake, can ya koma ya xauna a hankali yace "Mami it's not what u are thinking wllh yarinyar nan da kike gani taimakonta kawai Sudais yyi, she is an orphan...." Lkci daya idon Mami ya kada ta katse sa hade da kunduma masa xagi tace "An orphan??? Bata san hanyar orphanage ba ko kuma kai me yasa baka yi mata taimakon ba sai shi, ya ajiye mace da ba muharramarsa ba kace yana taimakonta Yusuf, tun da uwar ka ta haife ka ka taba jin haka?? su kuma yaran na waye?" A sanyaye Yusuf yace "Nata ne Mami" Mami na jin haka ta katse wayar tana kallon Hajiya Rukayya lkci daya idonta ya kawo ruwa tace "Kina jin halin yaran yanxu koh Rukayya, yanxu ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, ni dama da dadewa na lura da takun Aliyu, mu Aliyu xai kunyata a idon duniya? irin tarbiyar da ni da ubansa muka yi masa kenan" durkushewa Khadijah tayi a wajen tana kuka a hankali tace "Umma kiyi hakuri don Allah ki yafe masa" Tsawa Mami tayi mata tace "Rufe min baki, tarbiyar da iyayenki kema suka maki kenan kiyi rayuwa gida daya da namiji?" Cikin rawar Murya Khadijah tace "My parent are late, bani da kowa shi yasa ya taimakeni, Umma kar ki ce ya barmu don Allah..." sudais da ya ji kafafuwansa sun gaxa daukarsa ya xauna kan kujera ya ajiye su shureim da suka wani rirrikesa, cikin sanyin murya yace "Mami don girman Allah kiyi hakuri, ba yanda kike tunani abun yake ba, I just...." Katse sa Mami tayi cike da takaice tace "Ba yanda nake tunani abun yake ba Aliyu?" Sudais ya daga kai da kyar yana kallonta ganin hawayen dake idon mahaifiyarsa ya ajiye yaran ya mike ya isa gabanta ya durkusa cikin rawar murya yace "Noo Mami pls kar ki xubar da hawayen ki a kai na, na maki alkawarin na daina duk abinda nake daga yau, ki gafarce ni don Allah mamina" duk ya rikice mata, Mami na hawaye tace "Ni idan na gafarce ka Allahn ka fa? Wani tsinannen taimako ne wannan without the consent of ur parent, wani taimako ne wannan kuna rayuwa gida daya kamar mata da miji, yanxu ba don na san halin ka ba ance maka baxan yarda yaranka bane wa enan yaran?" Idonsa ya kada sosai cikin raunin murya yace "Mami nayi abinda nayi ne domin taimako amma daga yanxu na bari in sha Allah, forgive me plss Mami, nasan ban kyauta maku ba" Mami tace "Ka hada ina ka ina ka ka koma Damaturu yau ba sai gobe ba, sannan ina jiran makullin gidan yanxu ka same ni gidan Hajiya Rukayya" Tana fadin haka ta juya ta fita a parlon, kai kana gani kasan tana mugun son d'an nata ne, Hajiya Rukayya tace "Heed to what ur mother said right away Aliyu, ita kuma idan tace bata da iyaye ai baxa ta rasa dangi ba ta tafi wajensu" shi dai sudais bai ce komai ba, Hajiya Rukayya ta juya ita ma ta fita, Sudais ya dafe kansa da yyi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya dagule ga kukan Khadijah da yake ji har ransa, su kansu yan biyun kuka suke, lkci daya idanuwansa suka kada, mikewa yyi daga durkushen da yake ya wuce dakinsa ya dau makullin mota ya fita gidan gaba daya, Nanny da duk taji abin da ya faru ta iso gun khadijah dake kuka sosai ta dafa ta a hankali tace "Dama ba mijin ki bane mutumin nan maman twins?" Khadijah ta dago tana kallonta hawaye na sakko mata ta girgixa mata kai tace "Taimako na kawai yayi tun ban haifi yaran nan ba, ni bani da kowa sai shi yanxu" Hawaye ne ya cika idon Nanny tace "Dangin ku fa?" Cikin rawar murya Khadijah tace "Ban san dangin Mahaifiya ta ba, dangin Abbana kuma baxa su karbe ni ba, Ummata kuma ta tafi ta bar ban san inda xan ganta ba" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni yanxu ban san ya xan yi da yaran ba" kuka sosai Nanny take duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ta jawo ta jiki cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri wataran sai labari Allah baxai hanaki yanda xa kiyi ba, kar ki sake kuka don Allah" mikewa Nanny tayi ta tafi gun su Shureim dake ta kuka wai Sudais ya fita ya bar su. Bayan awanni kusan uku Nanny ta gaji da lallashin Khadijah da ta ki hakura da kukan da take, xuwa lkcn kuma su Shureim sun yi bacci, Da kyar Nanny ta lallaba ta taje tayi sllh don duk a sanyaye take, tana xaune kan darduma Sudais ya shigo gidan, kallonsa Khadijah ta dinga yi har ya xauna kan kujera, a sanyaye ta taso ta durkusa gefensa tace "Am sorry I caused you all this, kayi hakuri don Allah ka yafe min" Tana magana hawaye ce idonta, ya kirkiri murmushi yace "It's nothing Amira, tafi ki hada kayan ki gaba daya a sama" shiru ta yi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya gyada mata kai cike da assurance, tashi tayi jiki ba kwari ta wuce sama, ya kalli Nanny da ke parlorn ita ma duk a sanyaye yace "Ki hada kayan yaran da naki gaba daya" mikewa tayi ta wuce sama ita ma, Nanny ce ta fara sakkowa parlorn da jakunkunan kayan su shureim, Sudais dake kallonta yace "Ki kai cikin booth, its open" fita tayi waje da kayan, tana dawowa yace ta je ta taya khadijah, Kuka Nanny ta samu Khadijah nayi a dakin, bata iya tace mata komai ba ta shiga taya ta hada kayanta, Nanny ce ta sauko da jakan ta kai cikin motar, shi dai Sudais na xaune yyi nisa tunanin da yake, jin wayarsa na ring ya dauka da sauri yana kallon mai kiran, tashi yyi ya daga wayar yace "Mukhtar ka iso ne" daga daya bangaren abokin nasa yace "Ehh ina waje" fita yyi ya samesa waje, Mukhtar yace "You mean wannan gidan xaka siyar Barrister?" Sudais ya shafa kansa yace "Ehh shi" Mukhtar yace "Haba, Toh ai wannan yafi wancan wllh, ya xaka siyar da abu ka siya wanda bai kai sa ba kuma har da ciko, amma sun ma same ka da yawa" Sudais yace "kai dai bani takardun wancan gidan, and don't forget gidan is almost furnished" Barrister Mukhtar ya bude motarsa ya fiddo envelope ya mika ma Sudais ya karba yace "Duk da haka dai, duka duka kayan nawa ne a ciki" Sudais ya amsa envelope din yace "Nagode, bari in dauko nawa" daga haka ya koma ciki ya wuce bedroom dinsa ya dauko wani envelope dake dauke da takardun gidan nasa yana dawowa ya mika ma colleague dinsa yace "Kafin dare xa a kwashe komai na nan din, soo you help me explain to them" Mukhtar da mamakin Sudais ya cika sa ya karbi envelope din yace "Toh shkkn" daga haka suka yi sallama Mukhtar ya wuce, Sudais na komawa ciki ya sa Nanny ta dauko twins suka shiga mota, Ganin Khadijah bata fito sudais ya wuce sama ya bude kofar dakin duk da kukan da ya sameta tana yi kawai cewa yayi "Ke nake jira Amira" daga haka ya juya ya fita, Khadijah ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fita, a gaban motar ta xauna Nanny kuma na xaune da yaran a baya suka bar gidan bayan Sudais ya sauka ya rufe gate, tafiyar kusan minti ashirin suka yi sai kallon agogo sudais yake har suka iso wani anguwa, anguwa ce mai kyau shi ma kamar wancan, yyi parking dai dai gate din wani bungalow babba ya fita ya bude gate din ya ja motar suka shiga gidan, sosai gidan ya hadu bayan yyi parking ya bude motar ya fito yana kallon Nanny yace ta fito da yaran da xuwa lkcn sun tashi daga baccin da suke, kallon khadijah yyi ta bude motar ita ma ta fito, Sudais ya nufi entrance din shiga gidan ya bude kofar da makullin dake cikin envelope sannan ya shiga, parlorn na da girma amma bai kai na can gidan sudais ba, sannan dakuna uku ne ko wanne da bayi sai kitchen da dinning area, da kuma bathroom da toilet
Chapter 88 · 0% Book details