← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 168

Sashe 45

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har bakin daki kyauta ta kawo ma su Anty Khadijah breakfast din, Mumy ta taso ta karba ta dawo ta ajiye ta xauna tana sauraren 'yar uwar ta, Anty Khadijah tace "Toh fa kin ji Anty fati, kuma in sha Allahu da daddaya xan dauke yarana gaba daya a gidan, a kan wani dalili ina raye, dubi yanda iklima ta koma, mata muguwa axxaluma kawai duk ta gama da ubansu, tana neman kashe min 'ya ya ni wllh da ba dan bana ra'ayin Salisu ba da bbu abinda xai hana ni fitar da matar nan in koma gidan" Mumy dake ta kallonta tace "Ta ya?" Anty Khadijah tayi kwafa tace "Lallai kina wasa da ni Anty" Mumy bata sake cewa komai ba sai bin iklima take da ta fito wanka da kallo, Anty Khadijah ta sauka ta shiga hada mata shayi tace "Yi maxa ki shafa mai ki taho kiyi breakfast Pretty" Mumy tace "Toh Allah ya kyauta, Allah kuma ya shiryi masu irin halin ta, Allah ya raya mu tare da yaranmu" Anty Khadijah tace "Ameen fa" Mumy tace "shi yasa na ke nuna maki masu aikin nan ki rabu da su lafiya, tsakaninki da su gaisuwar mutunci wani hantara da nuna isa duk ba shi bane" dakatar da ita Anty Khadijah tayi da hannu ta daure fuska tace "A'a kar ki fara Anty kar ki bata min, dangin uwa ko na uba da xan dinga gaisuwar mutunci da su su rainani, ni ba gashi yarana basu ji ba basu gani ba ana walakantasu suna wahala, don haka ki kyaleni nayi ma kowa ma haka" Mumy ta tabe baki tace "Ka ji xancen banxan, to ai wannan a rubuce yake duk abinda kayi ma 'ya yan wasu sai an ma naka abinda nake ta nuna maki kenan kin ki gane wa" rai bace Anty Khadijah ta mike tana kallon Mumy tace "Ni dama tun da dadewa nasan ba so nake kike ba kawai kina xaune ne da ni dole don 6are ma sun fi ni k'ima a idon ki, Anty fati dole ne sai na xama so dangi kamar ki? Me ya hada ni da 'ya yan wasu? Don Allah ki kyaleni in yi rayuwata yanda nake so, ke kije can kiyi ta kwashe kwashen mutane har sai kin kwaso warce xata fiddo ki a inuwar da kike ta tura ki rana, muna nan da ke kuma" Tashi Mumy tayi ta nufi kofa bata sake tanka ta ba, Anty Khadijah ta bi ta da harara tace "Ke so dangi... To mutanen nan su ne xasu raba ki da farin cikin ki idan ba ki yi hankali ba" Saleem dake ta xaune a dakin bai tofa nasa ba tun daxu ya girgixa kai bayan fitar Mumy, Anty Khadijah tace "Kai ka ji fa saleem, dole ne sai na ja mutane gantalallu da xa su daura min wahala a rayuwa a jiki? In ji da yarana da kai na mana, Ita taga xata iya ne halinmu ba daya ba kuma baxai taba xuwa daya ba in dai a kan wannan ne, gwara ta kyaleni, kuma duk shegen da bai gallaza ma 'ya yana ba bai haifu cikin uwarsa ba... Mutum ne idan ban son sa ban son sa har abada babu me canxa min ra'ayi" Saleem yace "Ni Anty ban san me yasa Mumy take haka ba wllh, yau wannan gobe wancan, dubi fa kwanaki da kyar ta mayar da fitsararriyar yarinyar nan kauyensu ga shi yanxu ta jajibo wata ita wannan har boko naga an sa ta saboda matsayi" Anty Khadijah ta juyo tana facing dinsa a hankali tace "Wani bokon?" Saleem yace "Essence wllh" kasa rufe baki Anty Khadijah tayi tana kallon Saleem xuciyarta na bugawa, can ta nufi kofa fuuu ta fita, k'asa ta sauka gun kyauta, Kyauta dake ta aiki a kitchen tana wake wake tayi shiru ganinta ta risina tace "Har kin samu fitowa Hajiya" Anty Khadijah bata saurareta ba da wani expression tace "Kyauta ina yar uwar ki mai aiki nan" kyauta tayi kasa da kai tace "Toh Hajiya, jiya madam ta sa a kai ta makarantar bokon su baby, yanxu haka ma tana can" Anty Khadijah ta saki salati bata sake saurarenta ba fuuu ta wuce sama ta bude dakin Mumy, daga bakin kofa tana huci tace "Anty ita mai aikin kika saka a makarantar su siyama?" Mumy ta daga mata hannu tace "Khadijah ki tafi ki ban waje kar ki sake bata min rai don Allah, da kudin ki na sa ta bokon ko da ajiyar da kika bani?" Wani murmushi Anty Khadijah tayi tace "Ko daya, amma wllh kinyi making babban mistake a rayuwar ki, ita mai aikin kika sa a boko koh? Tam Allah ya taimaka, aje xuwa" daga haka ta fice daga dakin, parlor ta koma ta xaune tana girgixa kafa xuciyarta na kuna, can ta dau wayarta ta shiga kiran Aliyu, Aliyu dake xaune office ya dinga kallon wayar ganin mai kiransa har ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne hade da sallama, ko amsa sallamar bata yi ba cikin daga murya tace "Yanxu Aliyu kana gidan nan ka bari Anty ta sa mai aikin nan a makarantar da ku kayi?" Tabe baki yyi bai ce komai ba har lkcn wayar na kare kunnensa, tace "Ko da yake its a mistake ma kiran ka da nayi don duk bakin ku daya da Anty, kai ne ma munafukin... amma ina son ka sani wllh ta dauko ma kanta dala ba gammo ne, sai tayi mugun da ta sanin sake ma 6are da take yi kwanan nan ba sai an dade ba, sai ta xo ta sameni har daki tace Ashe abinda kike yawan gaya min gaskiya ne Khadijah, ni kuma a lokacin xan mata dariya, kai kuma ka ci gaba da biye ma gurgayen shawarar da take yi da kai har kai sai ya shafa muna nan baxa a dade ba in sha Allah, ita yarinyar da ku ka sa a makarantar sai ta ma sharrin da har jikoki baxa ka mance ba, sai ta goga ka bak'i a idon duniya" daga haka ta katse wayarta, Aliyu ya tabe a baki a xuciyarsa yace Allah ya shirye ki, daga haka ya ajiye wayar ya ci gaba da abinda yake. Da yamma bayan su Khadijah sun dawo tana bathroom ta shiga wanka kyauta kuma na fiddo mata kayan da xata sa sai ga Anty Khadijah ta shigo dakin 'yar ta Iklima na biye da ita a baya, Ko rufe kofar bata yi ba tana ma kyauta matsiyacin kallo tace "Ina tsinanniyar take?" Kyauta ta rasa abun cewa ta fara kame kame sai ga Khadijah ta fito daure da towel, kin karasowa dakin ta yi ganin Anty Khadijah, kai kana ganinta kasan tayi mugun tsorata, Anty Khadijah ta karasa ta fixgota da karfi tace "Kina da gadon mutanen gidan nan ne da kika yarda suka sa ki a boko?" hawaye ya cika idon Khadijah cikin rawar murya tace "Ki yi hakuri Anty" kife ta tayi da tafin hannunta da karfi ta gwara kanta da bango tana hade hakoranta tace "Sai kin lalata tsafin da kika shigo mana gidan nan da har aka sa ki a boko don kaza kazan ki" Khadijah ta rike kanta tana kuka sosai tana kallon kyauta da ta tsaya a gefe idonta ya kada, dukanta Anty khadijah ta dinga ta ko ina tana cewa "Barin gidan nan ya kama Ki don kaza kazan ki" Muryar mumy suka ji tana cewa "Zo nan Khadijah" Anty Khadijah ta dago tana huci tuni Mumy ta juya ta bar wajen, Rankwashi ta kuma kai mata ta sake gwareta da bango tace "Da bakin ki xaki ce masu baki son makarantar idan ba haka ba in kashe ki, kuma ki kama hanyar kauyen ku" daga haka ta fita dakin fuskarta a murtuke, sama ta iske mumy a tsaye, mumy na kallonta rai a bace tace "Khadijah idan har baxa ki iya xama da ni da mutanen dake tare da ni ba ki tattara ki bar min gidana nan ba da dadewa ba, ai ban hanaki xaman gidan mijin ki ba, a kan wani dalili duk xaki bi ki takura ma bayin Allah a gida, ina fa sane da duk abinda kike ba wai ban sani ba, ina ruwanki da bokon da na sa ta? Kudin ki ne ko kudin wani naki, ki fita harkata a gidan nan wallahi, banda mugunta yayi maki katutu me yarinyar ta maki xaki je kina dukanta haka alhalin daxu kika gama nuna rashin jin dadin ki a kan yanda ake treating din naki yaran a gidan ubansu, wlh na fara gajiya dake da halinki, komai na harkan gidana ki cire idonki a kai ki jira idan kina naki gidan in kin so yan Adam ma su kwanta ki dinga tattakesu wannan matsalar ki amma baki isa ba a gidana tunda ba tsoronki nake ba, lastly bbu ruwanki da wannan yarinyar Khadijah, tsakanina da ke daban tsakanina da ita daban, ki yi ta kanki a gidan nan" daga haka mumy ta shige dakinta. Anty Khadijah tayi kuka har ta gode Allah, har ta hada kayanta da na 'yar xa ta bar gidan wata xuciyar tace mata wato ma kenan yarinyar har ta isa da xaki bar mata gidan, ki tafi saboda ita, Inaa ai sai dai Ita ta bar maki, kyale Anty fati kawai kina xaune xata xo ta sameki, tunanin hakan yasa ta hakura da tafiyar duk da ba wai tasan inda xata bane, a ranta kuwa jin tsanar Khadijah take fiye da komai a duniya har kishiyarta ta kuma dau kudirin sai ta 6ata ta gun Mumy da kowa na gidan kafin a koreta. Tun da Aliyu ya dawo misalin karfe biyar yake xaune dinning, bai damu da rashin amsa gaisuwarsa da Anty Khadijah da ke xaune parlorn tayi ba, ya gama cin abinci ya hau danna laptop, iklima sai kai koma take a parlorn sun hada ido ya fi a kirga bata gaishesa ba shi ma bai ce mata komai ba, dinning taje ta dau ruwa suka sake hada ido ya hade rai yace "Sai na fasa idanuwan nan da kike kallona da shi a wajen, a gidan ku ba a koya maki gaisuwa
Chapter 45 · 0% Book details