Sashe 110
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read
Baby ta durkushe dakin tana kuka sosai tace "Mumy Anty Khadijah ce na ga tana xuba snipper a cikin indomien yaran da nake dafawa" Aliyu ya xaro ido yace "Snipper??" Da sauri ya nufi kofa mumy tayi maxa ta dakatar da shi, ya juyo hankali tashe yana kallonta, Mumy na kallon Baby tace "Ta gan ki?" Girgixa kai baby tayi tana hawaye, Mumy ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tace "Je ki dauko yaran ki kawo su nan, kar ki ce mata komai" Aliyu sai kallon mumy yake xuciyarsa na bugawa, Mumy ta kallesa tana kkrin goge hawayen idonta tace "Kar ka ce mata komai, let pretend we don't knw... Don't say anything Aliyu" Baby ta dawo dakin da su sudais mumy ta daura su kan gadon tana kallonsu a sanyaye, ta dubi Baby tace "Tafi ki xubar da indomie din, kar ki ce mata komai kin ji, ae basu da hakkinta don hka bbu abinda ta isa tayi masu wanda Allah bai masu ba" Baby ta fita dakin a sanyaye hawaye ya ko tsaya mata, ganin abun take kamar a movie, ynxu da bata dawo ba haka xata dau indomien ta ba yaran su ci su mutu?? Anya Anty khadijah na da conscience kuwa, me yan yaran suka mata, Aliyu kam ya kasa cewa komai, Mumy ta dinga share hawayen dake ta xubo mata, me tayi ma khadijah ta mayar mata da family dinta haka, dama laifi ne idan ka jawo naka ya xauna tare da kai?? Baby bata ko kalli Anty khadijah da ta xauna parlor tana shan shayi ba ta shiga kitchen din, Anty khadijah ta bi ta da kallo ta gefen ido, daukar indomie da kwan baby tayi ta fita ta xubar cikin shara ta tara tukunyar a bakin tap, sai da ta tabbatar ta wanke tas sannan ta dawo kitchen da shi ta ajiye ta fito kitchen din ta wuce stairs, Anty khadijah ta bi ta da kallo baki bude, da sauri tace "Ke wai sai indomien ya kone ne kin bar ma mutane gas yana ci" Ba tare da baby ta juyo ba balle ta kalleta tace "Sun ce baxa su ci ba na xubar" Daga haka ta haura sama Anty khadijah ta mike baki bude tana kallonta gabanta na faduwa, da sauri ta wuce kitchen ganin tukunyar a wanke ta fita waje ta leka bola taga indomien an xubar, still tayi a gun xuciyarta na mugun bugawa, kar dai ta ganta ne.... Jiki a sanyaye ta dawo cikin gidan tana adduar Allah yasa dai ko ta ganta kar ta gaya ma Mumy, Mumy da kanta ta sakko ta shiga kitchen din da ruwan gora biyu a hannunta, ta dumama ruwan sannan ta wuce sama da shi a cup don tana da kayan shayi a dakinta, Anty khadijah ta bi ta da kallo a sanyaye, shikenan kila baby ta gaya mata kenan, da sauri ta fita da wayar ta tafi can baya xata yi kira, nan daki mumy ta hada ma yan biyun tea ta basu Aliyu dai na xaune dakin yana kallon innocent kids din, baby da har sannan jikinta yake a sanyaye tana tsaye dakin ita ma. Duk da yanda Umma ta so bin Khadijah da khaleel xuwa gidan Aliyu kamar yanda khaleel yace kasa furta hakan tayi saboda kunya, Nanny ta dai raka Khadijah har bakin motar khaleel ta koma ciki, khaleel ya din ga kallon khadijah ganin yanda ta fada saboda kuka ta bude front seat a hankali ta shiga kanta a kasa, tausayinta ya ji har ransa ya tada motar ja suka bar layin, sai da suka hau saman titi a hankali yace "But you promised not to cry again Khadijah" da sauri ta kallesa da idanuwanta da suka rine tace "I didn't cry again, ai na riga na maka alkawari, wllh ban kara ba" a hankli yace "Toh naji dadi, kin dai san sunan anguwar su Aliyun koh?" Kai ta gyada masa, yace "Ina ne?" Tace "GRA" yace "Ai biyu ne Gra din, new or old?" Ta buda hannu a sanyaye alamar bata sani ba, wayarsa ce ya fara ring ganin me kiransa ya gangara gefen titi ya daga kiran tare da yin sallama, bayan sun gaisa da mai kiran nasa yace "Salman dama plss am asking... Can you connect me to a lawyer that you knw is just perfect, ni ba xaman Nigeria nake ba so I don't really knw, there is this case that I need one for... I don't want to talk about it to my family shi yasa I decided to contact you" Sai kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bayan wani lkci ya shafa lallausan gashin kansa yace "Sure... Ina jira, thanks much" daga haka ya katse wayar, ya juya ya kalleta ta dauke kai da sauri, d'an shiru yyi kafin yyi murmushi yace "Frnd dina ne, xae hada ni da lawyer yanxu, I think it's better we sue him, kulasa ayi hayaniya ba yi da fa'ida, and xai iya kai yaran wani gun, so ynxu two cases xa ayi da shi, 1st na rape... Sai kuma na biyu ya dawo rana daya yana claiming yaran da bai ma san kin dau cikinsu ba saboda rashin kunya...." Ita dai Khadijah ba ta ce komai ba, yace "So bari in jira xae turo min number Wani barrister da xanyi contacting yanxu" a hankali khadijah tace "Toh nagode, Allah...." Fingers dinsa ya daura bakinsa a hankali yana kallon kwayar idonta, ba shiri ta sauke idonta tayi shiru ta samu kanta da yin murmushi, text ne ya shigo wayarsa ya dauka yana kallon number da sunan barristern da Salman ya turo masa, dialing number yyi yana ganin ya shiga ya kai kunne, Sai da aka daga sannan Khaleel yyi sallama cikin cool voice dinsa, jin an amsa yace "Barrister barka da yamma" daga daya bangaren aka amsa masa da barka dai... Khaleel yace "You are speaking with Dr Ayman, plss ina son assigning din ka ne kan wani case, hope i won't inconvenience you..." Barristern ya amsa masa da "Sure, but na baro office yanxu" Khaleel yace "Waow.. So yanxu ya xa mu yi, and we need to talk today barrister" Barristern yace "Okay mu hadu eatry yanxu don ban shiga gida ba" Khaleel yace "Maa sha Allah ina godiya for ur time barrister" sunan eatry din Barristern ya gaya masa daga haka suka yi sallama, Khaleel ya katse wayar yana kallon khadijah yace "So mu je mu samesa eatry din yanxu koh" kai kawai ta gyada masa ya tada motar ya nufi eatry din, khadijah tayi nisa tunanin da take, gaba daya ji take kamar tayi shekara da shekaru rabonta da lovely twins dinta, bata taba tunanin tana son su har haka ba sai ynxu, ta ji ta kara tsanar Aliyu fiye da komai na rayuwar ta, she hate him with passion... kallonta kawai khaleel yake bayan ya gama parking cikin babban eatry din, a hankali ya kai hannunsa kan nata, lkci daya ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, yyi kasa da murya yace "Thinking about ur twins?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta tana kallonsa a sanyaye, ya girgixa mata kai yace "You've broke the promise" da sauri ta goge idonta tayi murmushi cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri" murmushin yyi shima ya fiddo handkerchief dinsa ya mika mata, ta karba a sanyaye tana goge idonta, kamshin handkerchief din ya kara kwantar mata da hankali, ganin bata maido masa ba ya bude motar ya fita ita ma ta fito ya rufe motar, yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin eatry din.