Sashe 103
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 3 min read
Khaleel ya fara ajiye jawahir a kofar gidansu, yana lura ranta bai so ba ta bude motar ta fita da kyar ma ta dau ledan siyayyar da tayi kamar baxa ta dauka ba, ko sallama bata yi masa ba ta dai daga ma su sudais dake kallonta hannu ta wuce ciki abun ta, ya lumshe ido ya bude sannan yyi reverse ya bar layin, yana isa kofar gidansu khadijah ya bude motar ya fito sannan ya bude back seat yana kallonsu sudais da suka yi jigum kamar xa su shige jikin uwarsu, yyi murmushi yace "Toh ku fito" da taimakonsa suka sauko kasa ya basu ledojin yace su shiga ciki, Khadijah xata fito khaleel ya dakatar da ita, sudais dake lekanta yace "Uncle Anty bata sakko ba" khaleel ya shafa kansa yace "Xata sakko yanxu ku shiga ku kai ma Umma chocolates din ku ta ajiye maku" yaran suka wuce ciki suna yi suna waiwayowa, khaleel ya shiga motar yana kallonta da damuwa yace "Ki gaya min plss me ya sa ki kuka khadijah, is it me?" Girgixa masa kai tayi a sanyaye wasu hawayen na gangarowa idonta, ya kasa daurewa ya rungumeta yace "No plss I don't want to see you cry, it hurt me, don Allah ki gaya min meye matsalar ki, me ya sa ki kuka a supermarket?" Tayi lamo jikinsa taji ta kasa kukan kuma, duk kamshin sa ya cika ta, murya can kasa yace "Khadijah" a hankali tace "Uhn" yace "Kukan me kike yi?" Ta lumshe ido cikin sanyin murya tace "Sudais" still khaleel yyi na kusan 10 seconds kafin ya dake cike da karfin hali yace "What about him?" Har lkcn idonta a lumshe tace "I saw him" dagota khaleel yyi da sauri yana kallonta at first a bit shock, sai kuma ya hade rai yace "Where?" Ta ki kallon kwayar idonsa tace "A inda muka je shopping" da kyar ta ci gaba wasu hawaye na taruwa idonta tace "He shunned me, he pretend he don't knw me...." Kasa ci gaba tayi ta fara kuka a hankali, khaleel ya lumshe ido, jin ta a jikinsa kuma yasa tayi shiru, a hankali yace "Khadijah..." Cikin sanyin murya tace "Na'am" dai dai kunnenta yace "forget about sudais plss, forget him...." Sai kuma yyi shiru, Khadijah taji kamar an xare mata radadin da take ji a xuciya, taji ta samu relieve, hankalinta ya kwanta fiye da xaton ta, murya can kasa tace "Toh, nagode" ji yayi kamar yyi kissing dinta but yyi controlling kansa bai yi hakan ba, har lkcn idonsa a lumshe yace "I... I know I love you from day 3 of our encounter....." Duk da yanda gaban Khadijah yyi mugun faduwa don bbu Wanda ya taba fadi mata wannan Kalmar duk tsawon rayuwarta hakan bai hanata fara tunanin me ya faru a rana ta uku da suka fara haduwa da khaleel a UK ba.