Sashe 159
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 3 min read
rikota tayi regaining balance dinta, dai dai lkcn da Shureim ya bude kofa, Saketa Aliyu yyi ya fita parlorn da sauri, Shureim ya sakko yana kallon mum din tasa da tayi stiff inda take yace "Anty what are you looking at" da sauri ta dawo ta fara kame kame, sai kuma tace "Toh ka kai masa makullin mana" waje ya tafi ta karaso cikin parlor da kyar ta xauna, Tana jin ya gama warming mota don ma kar ya biyota ta mike ta fito da sauri, har lkcn xuciyarta bugawa yake, Sosai ta ji dadin ganin Shureim xaune a gaba, ta bude back seat xata shiga Aliyu ya kalli Shureim yace "Kai koma baya sweetheart sai Anty ta xauna gaba" hade rai khadijah tayi tana kallonsa, Shureim ya fito ya dawo baya, Tana masa wani kallo tace "Nima a bayan xan xauna" juyowa Aliyu yyi ya kafeta da idanuwansa, sauke nata tayi da sauri, ta rufe motar ta xaga ta shiga gaba kamar xata yi kuka, har suka fita gidan bata yarda ta kallesa ba, sai bayan da suka hau titi yace "Zaria xa mu je" ba tare da ta kallesa ba tace "To do what?" Yace "Xa mu je gaida Anty khadijah, daga can sai mu biya family house din su iklima tana can" Lkci daya jikin khadijah yayi sanyi sosai, a hankali Aliyu yace "But idan baxa ki shiga ba sai ki tsaya a mota mu shiga ciki da Shureim" Ta girgixa kai tace "A'a xan shiga" almost half of the journey surutun Shureim kadai ne ke tashi a motar, daga karshe khadijah da abun ya isheta ta juya tana masa mugun kallo tace "You keep ur mouth shut.... ka dame ni" Aliyu ya bude ido sosai yace "Ni fa yake ba labari ba ke ba malama" Hararansa tayi tace "Ehh nace ya ishi kunne na, ya dakatar da labarinsa haka" Murmushi Aliyu yayi a hankali yace "Toh Anty..." Ganin sun kusa Zaria a hankali Khadijah tace "Toh baxa mu kai mata komai ba?" Aliyu ya d'an kalleta ya mayar da hankalinsa kan titi sannan yace "Like what?" Tace "Kamar fruits da dai abubuwan da marasa lafiya suke so" Murmushi yayi, bayan sun shiga Zaria yayi parking gun wasu masu siyar da kayan marmari, ya siya mai yawa, ya sa bayan mota ya dawo side din khadijah yace "I think fruits din ma sun isa" Khadijah tace "Toh iklima fah?" Yace "We will get her something idan mun fito" Bata ce komai ba ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da driving. karfe sha daya saura suka isa asbitin da Anty khadijah take a Zaria, Aliyu na gama parking gaban khadijah ya dinga faduwa, ga mugun fargabar da ya ziyarce ta, Aliyu na lura da ita bayan sun fito ya dawo gefenta a hankali yace "You need not to be afraid of anything Iman, relax ur mind, or you stay behind, baxa mu dade ba xamu fito" Ta girgixa kai tace "A'a xan shiga" daga haka ta bude bayan motar ta fiddo fruits din shi kuma yana rike da hannun Shureim suka shiga babban asibitin, har ward din da Anty khadijah take suka tafi, Aliyu ya bude kofar a hankali hade da sallama, shi ya fara shiga tare da Shureim sanann khadijah dake makale a bayansa, ta dade bata yi fargaba irin na lokacin ba, Baby ce xaune ward din tana xuba mata abinci, daga one side kuma Barrister Sudais ne yana xaune saman kujera rike da makullin mota, da alamar dai lokacin suka xo su ma, Aliyu ya dinga kallon Anty khadijah dake kan gado....