Sashe 90
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khadijah ta shiga hali na damuwa sosai bayan tafiyar sudais, bata da aiki sai na tunani da xubda hawaye bata taba xaton rabuwa da Sudais a lkcn ba, da ba don Nanny dake gidan tana kwantar mata da hankali ba da abun ya mata yawa, gani take kamar sudais xai dawo kullum jiran tsammani take amma shiru wasa wasa har sati biyu, ta rame ba kadan gashi kullum cikin jin ciwo take a kirjinta, ciwon da ta fi shekara bata ji sa ba sai gashi ya dawo mata da karfinsa, hakan yasa Nanny ta tilastata suka shirya suka tafi asibiti don ko baccin kirki bata iya yi da daddare, khadijah bata yi mamakin abinda likita yace game da ciwon da take yawan ji a kirji ba, at anytime xata iya kamuwa da ciwon xuciya, yini biyu tayi asibitin under medication, nanny tayi ta kai kawo da twins xuwa asibitin, da yamma likitan ya sallamesu ya kuma bata shawarari da dama kan abinda ke janyo ciwonta da yanda xata yi preventing tashin ciwon, A hanyarsu ta dawowa cikin Napep da damuwa Nanny tace "Yanxu Mum twins da kike sa ma kanki damuwa haka idan abu ya same ki yaran ki fa? Ko don su baxa ki hakura ki rufa masu asiri ki kwantar da hankalin ki ki rungumi kaddara ba, kar fa ki manta ko wani bawa da irin tasa kaddarar, so why not just accept urs a yanda ya xo maki" Khadijah ta goge hawayen dake xuba idonta a hankali tace "Ban san ya xan yi ba" Nanny ta kwantar da murya tace "Cire komai xa ki yi a ran ki, kiyi facing sabuwar rayuwar da xa ki fara da yaran ki, bawan Allahn nan ya tafi, ya kuma ya maki duk abinda ya kamata kafin ya tafi yanxu the ball is in ur court, sai kiyi abinda ya kamata ki kuma rike addu'a sai komai ya xo maki da sauki, as a mother nake baki shawara Khadijah... For the sake of ur boys ki yi hakuri ki cire ma kan ki damuwa don Allah" a hankali khadijah tace "Toh nagode sosai" suna isa gida Khadijah ta sauka ta ba mai adai daitan kudi, xata karbi shureim hannun Nanny ya makalkaleta ya ki yarda, jikinta yyi sanyi tana kallon yaron, Nanny tayi murmushi ta fito da duk yaran biyu, khadijah ta karasa ta bude gate din sannan suka shiga gidan, ba laifi ta dau shawarar Nanny ganin shi kadai ne mafita a gareta sai dai hakan bai sa fara'arta ya dawo ba, she is always sad, bata taba xaton Sudais xai bar ta so early a rayuwa ba, kusan kullum sai ta yi tunaninsa, magungunan da take sha ya taimaka ya rage mata ciwon xuciyar da take fama da shi duk da baya tasar mata ma sai da daddare taji kamar xata mutu, ba karamin kokari take yi na ganin ta ja su little sudais a jiki ba amma sun ki yarda ko da yaushe cikin gudun ta suke kamar dodo, hakan na kara sa ta shiga damuwa Nanny ta dinga nuna mata a hankali xa su sake da ita kar ta damu, a ranan da yaran suka cika shekara daya a duniya Nanny ta raka Khadijah tayi enrolling kanta a ss1 na wani makaranta dake nan anguwar ta su, idan ba ita ta gaya maka tana da yara har biyu a gida ba in xa a shekara ana gaya maka baxa ka yarda ba, a lkcn kuma shekarunta sha bakwai a duniya, kana ganinta kasan she is a teenager, a hankali khadijah ta fara kokarin yakice tunanin sudais a ranta domin tayi concentrating a karatun ta, idan ta fita tun safe sai hudu take dawowa gida, sannan ga islamiyyar da ta shiga na yamma, hakan yasa still babu wani interaction tsakaninta da yaranta tun da ba xaman gidan take ba, amma har ga Allah yanxu ji tayi tana son abun ta duk da tsoronta da suke ji har lkcn. Haka rayuwa ta ci gaba da kasance ma khadijah har ta gama ss1 lafiya, xuwa lkcn abu uku ne ke damunta a xuciya, Rashin Ummanta, gudun ta da yaranta suke sai kuma ciwon xuciyar da ya sa ta gaba abu kamar wasa kusan ko da yaushe hanyar asibiti take wanda hakan ke sa ta fashin makaranta don ma tana da kokari, Sudais kam ta rufe sa a babin rayuwarta sai dai duk sllh sai tayi masa addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi abinda yyi mata a rayuwarta da yaranta. Yau lahadi suna parlor, Nanny na feeding Sudais da shureim da yanxu shekarun su biyu da yan watanni a duniya indomie ta dafa masu take basu, yaran sun yi wayo sosai babu inda basa xuwa sai dai fa da ka gansu kaga Aliyu barin sudais komai na Abban nasa ya dauko, sau da yawa sai Khadijah tayi ta kallonsu, wani lkcn tayi murmushin takaici, wani lkcn kuma tayi hamdala ga Allah da ya bata yan biyun, Nanny ce ta katse shirun dake tsakaninsu tace "Mum twins to ya xa ayi da cefanen, wa enan ba yarda xa su yi in tafi in bar su ba, kuma wahala kawai xa mu je mu sha idan muka tafi gaba daya" Khadijah ta ajiye novel din hannunta tace "Nanny kawai da wayo xa ki tafi ki bar su" a tare yaron suka kalleta, Nanny ta kyalkyale da dariya tace "Toh ai kin tona, wa yace maki basa ji, sarai sun ji abinda kika ce" murmushi khadijah tayi tana mamakin sharpness din twins din, tuni shureim ya kara matsawa kusa da nanny, Khadijah ta tabe baki tace "Toh bari ni in je" Hijab har kasa ta daura kan kayan jikinta sannan ta dau kudin ta yi ma Nanny sallama tana daga ma boys din hannu ta nufi kofar fita su ma suna daga mata, jikinta yyi sanyi ganin in dai uwa xata fita yaranta sun dingi kuka kenan xa su bi ta, but why is her own case different, ko a jikin yan biyun dake cin Indomie da nanny ke basu har ta fita, to ita bata san kuma ya xata yi yaran nan su saki jiki da ita ba, iyakar kokari tana kokarin kwatanta masu abinda sudais yace Kafin ya bar su amma sun ki sakewa da ita, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa a ranta kuwa tunani take ko dai abinda sudais ya fada kan nonon da bata basu ba gaskiya ne, kenan haushin ta suke ji? Ji tayi da ma basu girma ba ta basu nonon yanxu, tsabar yanda jikinta yyi sanyi bata lura da motar da har ya wuce ta da farko ya fara reverse a hankali yana dawowa ba, tana ankarewa ta dauke kai da sauri hade da tsuke fuska don hakan ma yasa bata son fita, tana mamaki da jin haushin me yasa in dai xata fita sai an tsayar da ita, ita ba wannan ne gabanta ba kuma bata jin xuciyarta xai kara kula wani d'a namiji har ta bar duniya, ganin mai motar ya fito daga motarsa ta bar wajen da sauri tana tafiya fuska daure ba tare da ta damu ta kallesa ba, ji tayi ance "Khadijah?" ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi, ya dinga kallonta kamar me son kara tabbatar da ita ce ko ba ita bace, ita din ma kallonsa take da mamaki, yace "Baki gane ni ba Khadijah?" Jikinta yyi sanyi lkci daya tayi murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tace "Na gane ka, am just trying to be sure ko kai ne ko ba kai bane" ya wara yace "Maa sha Allah, Imagine we met after 3 good years" murmushi ta kuma yi tana kara kallonsa da kyau ganin yyi mata tsayi fiye da yanda ta san sa a da tace "Sure, to ya bayan rabuwa" ya rike chin dinsa yace "Waow kin girma Khadijah, just look at how calm you are now, kin tuna lkcn da kike yawo ba Hijab da jikakken kaya?" dariya ya bata ta rufe fuska tace "Har da tsokana" yace "Am serious, a Abuja dama ku ke?" Tace "Ehh wllh, ya su mama fa" yace "Suna kt, nima ban dade da fara aiki a nan ba, just 7 months back" Khadijah tace "Allah sarki, toh Allah ya taimaka" d'an shiru yyi yana kallonta, kafin a hankali yace "Ko kin yi aure ne Khadijah?" Kallonsa ta tsaya yi ita ma, lkci daya ta samu kanta da girgixa masa kai tace "Aure kuma, A'a ina karatu ne" yyi murmushi yace "That's good, kar in tsaya ina ta tsurutu da matar aure ban sani ba" murmushi kawai khadijah tayi a xuciyarta kuwa mamakin yanda aka yi ya fara magana ta yi don a lkcn da ta san shi da wuya yake magana sai dai danna waya, lkci daya jikinta yyi sanyi tuna abinda yyi mata a lkcn da take walagigi a katsina cikin yunwa, muryarsa ya katse ta yace "Ina xaki yanxu?" Ta kallesa tace "Kasuwa" yace "Toh shiga in yi dropping din ki" d'an xaro ido tayi tace "Kai da ba d'an gari ba?" Yace "Wata na 7 kice min ba d'an gari ba" murmushi tayi tace "Toh naji kai d'an gari ne" yace "Toh shiga muje" motar ta bude tana murmushi ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver suka bar wajen, yana driving yace "So ya rice and stew, and Irish with egg? Kuna nan kuna damawa koh?" Dariya sosai Khadijah tayi ta rufe fuska, yana murmushi yace "Yarinyar nan ta kashe min kudi a lkcn da abincin yan gayu gashi sai Abba ya bani nima lkcn" Khadijah ta dago a hankali tana kallonsa tana murmushi tace "Ae yanxu babu abinda bana ci har tuwo da miyar kuka, da ma kunu da kosai" ya wara ido yace "Da gaske? Anya xan yarda kuwa" ta gyada masa kai tace "Serious..." yace "Hmm that's surprising amma" ta turo baki tace "Baka yarda ba kenan?" yace "Toh ai ban ce komai ba Khadijah" suna isa kasuwa bbu yanda Khadijah bata yi da shi ya tafi ba yace xai jira ta, bbu yanda ta iya haka ta siya abubuwan da tasan xa su bukata a lkcn daga baya sai ta dawo ta siya sauran