← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 168

Sashe 37

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe hudu duk yaran gidan suka gama shirin tafiya islamiyya, kyauta ta hada socks dinsu gaba daya da Uniform din autar Mumy da ake kira da Baby saboda sunan Anty khadijah gareta xata wanke, kallon khadijah dake tsaye kanta tayi tace "Toh ni dai kin tsaya min kamar soldier ki tafi can dinning area ki kwaso duk plates din wajen, saura kar kiyi a hankali" khadijah tace "Toh" sannan ta wuce ciki, bbu kowa dinning area din sai plates da shinkafa da aka yi littering a wajen, Khadijah na ganin Anty khadijah a parlor xaune tana gyara ma Baby Hijab tayi saurin dauke kanta ta shiga hade plates din waje daya, muryar daya daga yan matan parlorn taji tana cewa "Anty wacece wancan yarinyar wai?" Anty khadijah ta tabe baki tace "The new housemaid" Baby ta xaro ido tace "Anty is kyauta going?" Anty khadijah tace "Noo she is not" Baby ta sauke ajiyar xuciya tace "Better... coz I don't think i like that girl, she can look for Africa as a whole" horn da driver yake yasa Siyama da Aneesah suka mike rike da jakar islamiyyarsu suka ma Anty khadijah sallama suka fita, Anty khadijah tace "She's not even worth talking to, don hka bbu ruwanki da ita yar aikin gidan ce kin ji takwara" baby tace "Sure" khadijah ta turo baki tana kallonsu, baby ta harareta ta fice daga parlorn, khadijah ta ki daukan komai a dinning din ta fita gun kyauta da gudu tana kumbure kumbure, kyauta tace "Ina kwanukan?" Ta fashe da kuka tace "Anty mai girki kinga yarinyar nan har da neman tsokanana koh, shine har da ce min I can look for Africa where as she was the one looking at me, kuma Anty mai ihu tace mata ni house girl ce" Kyauta ta tabe baki ta nuna mata wani dakali tace "Tafi can ki xauna, ni dai ba ruwana idan kina kallon yan gidan nan sai su dake ki ma su daki banxa nima ba kyaleni suka yi ba gwara babyn ma a cikinsu, idan ba iskanci ba... Ba aikin aka kawo ki kiyi ba har xa ki ji haushi don an ce maki house girl?" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, kyauta ta gama wankin ta tafi ta kwaso plates din ta gyara dinning din, khadijah ta hada ma kayan wanke wanken can bakin tap kar ta jika kitchen din ita kuma ta shiga girka dinner, da ta leka sai ta ga kamar ba a wanke wanken, daga karshe fixgota tayi bakin tap din ta turata waje daya ta shiga wanke wanken tana bala'i, khadijah ta toshe baki kar tayi dariya jin har da kiranta lazy ass, har kusan magrib khadijah na kusa da kyauta a kitchen komai kyauta ta sauke kan wuta sai ta ba buda mata hannu xata d'an d'ana tun kyauta na mata da mugunta tana konata da cokalin miya har ta gaji ta kyaleta sai ta xuba mata a d'an karamin plate, kyauta ta samu wani roba ta xuba duk pepper soup din da tayi mai yawa a ciki bata yi gigin ba khadijah ba tace "Tafi ki leka su waye a parlor" khadijah ta dawo tace "Ba kowa Anty mai girki" kyauta ta fita da sauri ta bude dakinsu ta ajiye masu bayan kofa sannan ta dawo ta jera komai kan dinning bayan ta ba khadijah na su Usman mai gadi ta kai masu, Kyauta na gama tsaftace kitchen suka wuce daki da Khadijah, sai a sannan ta xauna ta fixgo khadijah tace "Ke bakya sallah ne hala?" Khadijah tace "Ina yi amma bani da Hijab yanxu" turata bayi kyauta tayi tace "Ni ina da shi ai" Khadijah na xaune kan dankwalin da kyauta ta shimfida mata ta yi sllh tana ta kallon kyauta dake addu'a ta idar da sallahn ita ma, Muryar Mumy kyauta taji ta shafe addu'ar ta mike da sauri ta fita khadijah ma ta bi bayanta da sauri, Mumy tace "Ki xuba ma Aliyu abincin xai wuce aiki yanxu, ku kun ci abincin?" Kyauta tayi kasa da kai tace "Xan xuba masa yanxu Hajiya, mu kuma yanxu xa mu xuba" Mumy tace "Toh sai ki debar maku har da farfesun" Kyauta tace "Toh mun gode Hajiya" Mumy tace "Toh ya tana kokarin aiki kuwa ita?" Mumy ta fada tana nuna khadijah, kyauta tace "Ehh ba laifi Hajiya" Mumy ta juya tace "Toh shkkn" A dinning kyauta ta dibar ma Aliyu nasa abincin a plate ta xuba masa farfesun kaji sanin bai cin sauran, sama ta tafi kai masa khadijah ta biye da ita, ta kwankwasa masa kofa ba a dau lkci ba ya bude yana buttoning din shirt din jikinsa, kyauta tace "Ga abinci yallabai" kallo daya yyi masu ya karbi tray da kyauta ke mika masa yace "Nagode" khadijah tace "Nan ne dakin ka" bai ce komai ba ya rufe kofarsa, kyauta ta ja khadijah suka sauka ta shiga daki da ita ta hade hannayenta biyu tace "Ke wai dan gidanku ina ruwan ki da likitan gidan nan, kin taba sanin sa ne idan ba shisshigi ba?" A hankali tace "Kiyi hakuri" kyauta ta ja bakinta da karfi hade da dungurinta tace "Sai na cire maki wannan mayun idon naki wllh idan kika sake yi ma kowa magana a gidan nan" khadijah ta gyada mata kai hawaye cike idonta, kyauta ta fita ta bar jin alamar su baby sun shigo gidan daga makaranta. Ko kafin kyauta ta sallamesu ta dawo ciki har khadijah tayi bacci, tashin ta ta shiga yi ta ci abinci cikin magagin bacci take cewa Umma na koshi, kyauta ta debo ruwa ta yarfa mata a fuska, da sauri ta farka gaba daya kyauta ta ajiye mata abincin a gabanta ta shiga bayi don yin alwala, ko da ta fito Khadijah bata ci abincin ba ta koma bacci, hakan yasa tace "Ke kika sani" dagata tayi ta kwantar ta xauna cin abincin ita kafin tayi sallahn. Washegari kyauta na idar da sallah ta fita daura breakfast, ta gama fere dankalin turawa Anty khadijah ta shigo kitchen din, kalle kalle ta shiga yi kafin tace "ina wannan yarinyar take?" Kyauta tace "Ina kwana Anty?" Anty khadijah tace "Lafiya, ina yarinyar nace?" Kyauta tace "Na aiketa daki shiru shiru" fita Anty khadijah tayi ta bude kofar dakin kyauta tana yatsine fuska, kwance ta tadda khadijah shame shame kan gado, karasawa tayi ta maka mata duka har sau biyu a baya, khadijah ta farka a rikice, Anty khadijah ta fixgota tace "Ko yan gidan gaba daya ma sun tashi bare ke shegiya, a hakan xa ki iya aiki a gidan nan, a kirga har dubu goma a bai ma iyayenki jiya ki yi ma mutane shame shame kina bacci kan gado har yanxu?" Khadijah ta sauka kan gadon hawaye cike idonta tace "Anty kiyi hakuri" fixota Anty khadijah tayi ta turata waje da karfi tace "Fita kije ki kama ma kyauta aiki, ko ita din baiwar ki ce, ina ce yanda ake biyanta haka ake biyan ki kema" khadijah ta wuce kitchen da sauri tana hawaye, Anty khadijah ta biyota har kitchen din tace "Maxa hada wanke wanke ki fita ki yi" da sauri ta dinga fita da plates waje hawaye na sakko mata, ita dai kyauta bata ce komai ba har Anty khadijah ta fita kitchen din, khadijah ta dau cups uku xata fita da su, kyauta tayi tsaki tace "Mata ta ki xaman aure duk ta xo ta addabe mutane a gida tirrr, ke kuma ai kinga result din bacci kamar matatcciya" khadijah dai bata ce komai ba ta fita, Kyauta ce tayi wanke wanken bayan ta sallami yan makaranta khadijah na mata dauraya, karfe tara da rabi mumy ta sakko xata fita aiki, bayan sun gaisa da kyauta dake hada mata breakfast a dinning mumy tace "Ina khadijah" Kyauta tace "Tana can tana shara Hajiya" Mumy tace "Ohk" kyauta ta koma kitchen bayan ta gama hada ma mumy shayi sanin gimbiya na can sama tana ta bacci yanxu haka, Kallon khadijah tayi da tasa dankali da kwai da shayi a gabanta ta ki ci, Kyauta tace "Au baxa ki ci ba?" Khadijah ta kalleta tace "Ina ci" sai kuma ta fara kuka, Kyauta tace "Samun waje, wato duk da lafiyayyen abincin nan dake gaban ki har kuka kika samu daman yi koh? Kila ma a gidan da kika baro baki samun irin haka" khadijah ta mike tana kuka ta daga rigarta tana nuna ma kyauta bayan ta tace "Anty mai girki har yanxu fa xafi wajen da ta dokeni yake min" kyauta ta buda baki ganin shatin hannun Anty khadijah a bayanta, can tace "Tabdi, toh Allah ya isan ki, kuma in sha Allahu a baxawara xata Karachi rayuwarta, ni kam ko yanxu na bar gidan nan nasan xan samu mijin aure, ita kuwa wllh sai dai taga ana yi, kuma ina jin ita ma ta bar 'ya yanta a wani gidan to haka xa ayi ta cin ubansu ana gallaza masu in sha Allahu" Kyauta ta sauke rigar tace "Maganinki kenan kema dai, gobe ba sai kin jira an tashe ki ba" daga haka kyauta ta ci gaba da aikinta, da sauri kyauta ta fita jin mumy xata wuce gun aiki, ta gama sauraren abinda mumy ke ce mata ta risina tace "In sha Allah Hajiya, Allah ya tsare hanya" tsaye jikin kofa Mumy ta hango khadijah tace "How are you" a hankali khadijah tace "Good morning maa" mumy ta kalli kyauta tace "Anya baki cika ma yarinyar nan aiki kuwa kyauta?" Da sauri kyauta tace "Wallahi ko daya Hajiya, ki tambayeta bana cika ta da aiki" Mumy tace "Ohk" sannan ta mayar da dubanta kan khadijah tace "Am off to work, hope kin yi breakfast?" Ta gyada kai tace "Nayi Anty" Mumy tace "Good" daga haka ta nufi kofa, kyauta ta rakata tana mata Allah ya kiyaye, Mumy na fita da motar ta kyauta ta koma kitchen ta kwashi sauran kayan wanke wanke ta tafi wankewa a waje, khadijah na ta tsaye bakin kofar kitchen din Aliyu ya shigo gidan, tun da ta kallesa bata sake kallonsa ba har ya wuce sama, bayan kusan minti ashirin sai ga shi ya sakko, har lkcn khadijah na
Chapter 37 · 0% Book details