← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 168

Sashe 71

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read

ta kara saukewa jin aman ya d'an lafa mata, ta kallesa da kyar tace "Xan kuskure baki" table water dinsa da ya shigo da ya mika mata ta tashi ta wuce bathroom da sauri, bata fito bayin ba sai da ta amayar da gaba daya gyadar da ta ci, ta fito da kyar ta xube nan tsakiyar dakin tana satan kallon sa tana mayar da numfashi, wani kallo ya dinga mata Daga inda yake xaune, bata sake kallonsa ba ta lumshe ido, lkci daya kuma bacci ya dauketa, gashin kanta taji ana gyara mata ta bude ido da sauri ta gansa durkushe gefenta yace "Ki rufe gashin ki ki hau saman gado" ba musu ta mike xaune ta hade uban gashinta waje daya ta tufke, xata mike tsaye jiri ya kwasheta ta koma da sauri ta xauna yace "Be careful" gyada masa kai tayi ta kuma tashi ta koma kan gadon ta kwanta, ac dake dakin ya rage yace "In kashe maki wutan?" Ta girgixa masa kai, yace "Sai da safe" daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin. Kafin asuba Sudais ya shigo ya fi sau biyar duba ta don da ya bude kofa xata farka, gaba daya ya kasa bacci tunanin yanda xai yi da khadijah ya damesa gashi mami Bata san ya dawo ba ma, shigowarsa na karshe ne ya rufe ta da blanket don xaxxabi ne sosai jikinta, da asuba da ya shigo tashinta tayi sllh amai tayi ba kadan ba kafin ta dauro alwala ta fito, ruwan wanka ya hada mata bayan ta idar da sllhn, da kyar ta yi wankan ta fito, ta kasa shiryawa ta kwanta nn kan gado ya lullubeta da bargo, bayan kusan minti sha biyar ya dawo gefenta yace "Daure ki tashi ki shirya mu tafi clinic" bata ce komai ba don har fuskarta ta rufe, ya cire bargon suka hada ido, sauke idonsa yyi yace "Tashi ki shirya" daga haka ya fita dakin, har ya dawo bata tashi ba, yace "Ke fa nake jira" cikin sanyin murya tace "Ni baxan iya ba" yace "Toh ni xan sa maki kayan?" Bata ce masa komai ba, yace "Look bana son in dawo in gan ki cikin bargon nn it's better ki daure ki tashi kiyi abinda xa kiyi" juyawa yyi ya fita, cike da karfin hali ta mike xaune hawaye cike idonta, kamar ynda yace mata haka ta dinga daurewa har ta sa kayan a nan inda take kan gadon, tana gama sa wa ta koma ta kwanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin, tsayawa yyi kusa da gadon yace "Toh tashi mu je" rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta mike xaune a hankali tana sauke numfashi, Wayarsa ce ta fara ring, ya daga yana kallon screen din kafin ya xauna da sauri ya daga ya kai kunne tare da sallama yace "Good morning Mami" murmushi yyi yana shafa gashin kansa a hankali yace "Ku yi hakuri Mami ban kira ba, amma in sha Allah yau xan taho, am done with what am doing" bayan wani lkci yyi mata sallama ya mayar da wayar aljihu, yana kallon khadijah yace "Tashi mu je" daga haka ya nufi kofa, a hankali ta sakko da kafafuwanta kasa tayi karfin halin mikewa, har suka isa compound din gidan bai juyo ba, sai da ya isa gun motarsa ya juyo yana kallonta, can ya bude motar ya shiga, ta karasa ta bude front seat ta xauna ta lumshe ido don ji take kamar wani aiki me wahala tayi, wani babban private asibiti suka tafi, bayan yyi parking ya juyo yana kallonta da kyau yace "Har mu bar clinic din nn bana son jin bakin ki, am nt asking for ur opinion or anything, I am doing wat I think is right, am I clear?" A hankali ta gyada masa kai, yace "Good" da yake da safe ne ba su wani dde ba suka samu ganin likita bayan ya biya kudin kati, ta xauna daya daga kujeran dake kallon likitan, ya xauna shi ma yana facing dinta, hannu ya ba likitan suka gaisa, likitan na kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "How you madam, though u look sick" khadijah tayi murmushin karfin hali, likitan yace "Allah ya sauwake, ya raba lafiya," kallon Sudais dake shafa beard dinsa yyi yace "Drugs xan rubuta maku yanxu da xata dinga sha, there is nothing more I think.... She will get better gradually" Sudais ya ce "Ba abinda ya kawo mu ba kenan Dr, though I knw it might look wrong, but... she got pregnant by mistake, it's just some weeks old, so plss I want u to get rid of it...." Tunda ya fara maganan likitan ke kallonsa da expression din mamaki, Sudais yyi kasa da murya yace "Yes plss" likitan yace "Sorry we don't do that hear sir, xaku iya tafiya wani asibitin" kallon Sudais khadijah take kamar idanuwanta xa su fito, Sudais yyi kasa da murya sosai ya marairaice yace "Yeah, I knw it's very wrong Dr... But she is my.... Wife, the last pregnancy wasn't funny, and.. She's breastfeeding an eight month old baby now" kamar ana forcing dinsa yyi magana, likitan sai kallon khadijah yake, Sudais ya ciro handkerchief ya share goshinsa don har xufa ya keto masa yace "Plss Dr, ka taimaka for d sake of d eight month child" Likitan ya girgixa kai yace "I think xai fi a daina breastfeeding babyn, she shud take care of d one she's carrying now, sai kaga Allah ya taimaka komai ya xo da sauki" Sudais yace "Nooo Dr, don Allah ka cire mata I will pay what ever amount u request for plss" likitan ya mike ya nufi show glass dake office din ya dauko wani allura da syringe, ya dawo yace "I will give her this injection sauran drugs din kuma xan rubuta maka kaje pharmacy ku siya" Sudais ya sauke ajiyar xuciya yace "Thanks very much Dr, nagode sosai" Lkci daya khadijah t fashe da kuka ta mike tace "Nooo, ni bana son a cire min don Allah ku yi hakuri" bude baki Sudais yyi yana kallonta da mamaki, ta hade hannuwanta tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, I don't want to abort d pregnancy, Allah will be angry with me plss" Likitan ya ajiye alluran ya rungume hannuwansa yana kallonta yace "Ba mijin ki bane kenan?" Hawaye na ci gaba da sakko mata ta gyada masa kai alamar eh, Sudais dake mata wani irin kallo ya mike yace "Sae ki san inda dare yyi maki kuma daga nan" daga haka ya fice daga office din kamar xae tashi sama, a hankali take kuka tana kallon likitan dake kallonta yana girgixa kai, can ta nufi kofa cikin sanyin jiki ta fita, babu motarsa a parking space, ta fita gate tana share hawayen da ya ki tsaya mata.
Chapter 71 · 0% Book details