Sashe 30
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 3 min read
kunnenta tace "Don uwarki kika sake taba min 'ya sai na cire maki hakori wallahi, muguwa kawai mai halin banxa" daga haka Umma ta hankadata, walida ta fasa wani ihu kamar xata tsaga gida tana kiran uwarta. Mikewa Hasana tayi baki bude tace "Amina??? Ita walidar kika mara??" Umma ta juya tana facing dinta tace "An mareta, ki taho ki rama mata, d'a ya fi d'a ne, ai wllh duk shegiyar da tace 'ya ta baxa ta xauna lafiya ba gidan nan sai dai ita ta rasa xaman lafiya, me marainiyar ta maku? Ko ba a cin arxiki dama a duniya, kishin naku ya tsaya iya kai na mana, toh wllh duk ku ja ma 'ya yan ku kunne, duk wanda ya sake ko da yi ma khadijah kallon banxa ne, sai nayi masa abinda bai yi xato ba" tana kai wa nan ta tafi daki da Khadijah ta tura ta ciki tace "Maxa ki canxa kaya" daga nan kuma ta dawo kitchen ta ci gaba da abinda take rai bace, daga Hasana har Shafah haka suka bude baki suna kallonta bbu wanda ya iya cewa komai cikinsu. Da daddare Abban Fadila ya dinga kwalo ma Umma dake xaune kan darduma kira, ta mike ta fita don bata ma ji shigowarsa ba amma tuni har ya shiga parlon sa, bin bayansa tayi ta shiga parlon tana masa sannu da xuwa, bai amsa ba ta xauna ba tare da ta yarda ta kalli kishiyoyinta dake xaune parlorn ga Walida a durkushe a kasa, Abban Fadila yace "Amina, so nake xuwa gobe ki mayar da yarinyar nan dangin ubanta da kika daukota, I agree zan yi sponsoring dinta ko tana can din, idan ya so duk bayan watanni uku ko hudu sai ki je ki dinga dubata, I think that will better, I didn't buy d idea of her staying here anymore...." Tun da ya fara Umma ke kallonsa a sanyaye, Hasana da Shafah da aka wani hakikance kan kujera kamar wasu Hajiyoyi xa a iya ganin murnar dake shimfide fuskarsu, trying hard to control her tears Umma tace "Saboda me kace haka Alhaji? Kada ka mance yarinyar nan marainiya ce ba ta da kowa, tun tana yar shekara biyu mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta kuma bai mata gatan nuna mata dangin mahaifiyarta ta ba, da na sansu da can xan kai masu ita baxan kawo ta ba gidan ka Alhaji" Abban fadila yace "Kiyi hakuri iyakar taimakon da xan ma yarinyar kenan, ko nawa ne kudin karatunta xan biya idan ya kama ma da feeding expenses duk xan ba da, kawai dai gidana ne baxata xauna ba, kuma baki min kara ba da har xaki daga hannu ki mari diyata a ido don abun su can ya hada su, so tafiyarta xai fi, I think that's all... Gobe ki hada kayanta ki maida ta inda kika dauko ta" Umma da hawaye ke xuba idonta a hankali tace "Ina jin da ka sauwake min kawai in tafi da ita xai fi don ni baxan mayar da ita dangin mahaifinta ba" yana gyada kai yace "Kema xa ki iya sauwake ma kanki ai Amina ba sai na sauwake maki ba" mikewa Umma tayi ta fita ta koma bangarenta, ta shiga daki tayi kukanta mai isarta, duk tausayin khadijah ya cika xuciyarta, to yanxu ina xata kai marainiyar nan, ita ba ta da kowa mahaifiyarta ta rasu da sai ta kai ta gun ta tasan xata rike mata ita, bata da wani abun hannu don duk cutar ta yayyin mahaifin khadijah suka yi a rabon gado bayan ya rasu, domin kuwa kafin a ankare sun boye abubuwa da dama cikin dukiyarsa, banda haka da ko boarding sai ta kai khadijah, har gari ya waye Umma bata ritsa ba tana ta tunanin inda xata kai khadijah domin ta ma kanta alkawari first thing da safe xata fitar da ita da gidan, yayarta warce suke uba daya dake Kaduna ta fado mata ta yi shiru tana naxari.