← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 168

Sashe 33

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma" khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace "Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba" yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya" daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa'a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace "Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?" Yakumbo ta tsuke fuska tace "A kan me?" Abu tace "A'a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace "Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?" Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu'ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace "Toh Allah ka bamu sa'a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba... Yakumbo tace "Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru" daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace "Wa ku ke nema?" Yakumbo ta mike tace "Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana" ya girgixa kai yace "Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo" Bakin yakumbo ya fara rawa tace "Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh" Mai gadin yace "Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn" daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa "Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi" Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya.
Chapter 33 · 0% Book details