Sashe 74
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 6 min read
daman sakin maganin gaba daya a Hijab din cikin dubara sai kuma tayi saurin dage kafarta kamar xata daura kanta bisa kneel dinta, har lkcn kuma hannunta na dunkule kamar tana rike da drugs din, Yusuf yace "Baxa ki sha ba?" Bude baki tayi ta yi kamar ta watsa su ciki sannan tayi saurin xuba ruwa bakin ta tana yamutse fuska har da kokarin amai, da sauri Sudais yace "Don't try that" ta hade kai da gwiwa suna ta tsaye suna kallonta har ta dago a hankali, Yusuf ya juya ya fita sudais ya bi bayansa, Yusuf yace "Toh sai kayi xaman gadi" daga haka ya bar gidan, Sudais na ta xaune har dare amma shiru, mamaki ya dinga yi anya ba yaudararsa Yusuf yyi ba, a fusace yaje har gida ya samesa don jin me yasa yyi masa haka, Yusuf dake dakinsa kwance yace "Toh ka kai ma wani likitan takardar maganin ka tambayesa na menene, I think that's all I can tell you" Bayan kwana biyu sudais ya sake komawa Yusuf office da rana, da damuwa yace "Dr ko xaka canxa wani method din ne, wllh I don't have rest of mind, am afraid kar Mami ta san abinda nake yi, gashi in few weeks time xan je UK, to ya xan yi da yar mutane?" Yusuf yayi dariya yace "Tunda taimakonta kake son yi ka tafi da ita mana" Yusuf ya watsa masa kallo yace "Ko matata ce ke wannan laulayin ina xa ni da ita balle wannan" Yusuf yace "In baka shawara Barrister?" Sudais yyi shiru yana kallonsa, Yusuf ya mike tsaye yace "Wllh ka kyale mata cikinta tunda ka ga haka, Allah kadai yasan me xata haifa, there is power in the baby, banda haka ban ga dalilin da xai sa ta sha drugs din nan har sau biyu ba amma shiru ake ji, just let her pls and idan son samu ne ka taho da ita clinic ko gobe da safe ayi mata scan cos this is almost a miracle" kasa cewa komai Sudais yyi can ya juya ya fita. Washegari kamar yarda Yusuf yace haka Sudais ya sa khadijah ta shirya suka je asibiti don a mata scan, gaba daya jikinsa yyi mugun sanyi bayan result ya fito, shi kadai da Yusuf ne a office din Yusuf din, ita kuma tana reception, Yusuf yace "You see, da haka xaka sa ayi wasting bayin Allahn da basu san komai ba, 2 souls barrister" Sudais bai iya yace komai ba. A hakan dai Sudais ya ci gaba da ba Khadijah kulawa yanda ya kamata, bai rage ta da komai ba a gidan sa, damuwarsa daya yanda ta ki kwantar da hankali har lkcn ga yawan koke koke, idan ya sa ta gaba ta fadi me ke sa ta kuka sai ta ce masa ita bata da kowa yanxu, hakan nasa jikinsa yyi sanyi, sannan hakan ke kara masa kwarin gwiwan ci gaba da taimaka mata, ganin saura yan kwanaki ya fita kasar ya sa ya shiga tunanin wanda xai bar ta da a gidan, idea ne ya xo masa yasa aka nema masa wata dattijuwar da xa su xauna tare da Khadijah a gidan nasa, hakan aka yi bayan matar da baxata haura shekaru hamsin ba ta amince duk wata xai dinga bata dubu arba'in. A yau Khadijah na daki xaune kasan carpet tana shan kunun da dattijuwar da ta dama mata, dattijuwar matar da a ranan tayi kwana uku a gidan duk tunaninta Khadijah matar Sudais ce, su biyu ne dakin Sudais yayi sallama bakin kofa, ta mike da sauri ta iso kofa ta bude tana cewa "Sannu da xuwa yallabai" Gaisheta yyi ta amsa cike da jin dadin yanda yake girmamata sannan ta fita, Sudais ya karasa cikin dakin yana kallon khadijah, wani mugun haske tayi da kyau sai kyalli take, lips dinta yyi pink colour, dauke kai yyi ya isa gefen gado ya xauna, a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya jiki?" Tace "Da sauki" shiru yyi na wasu yan mintuna kafin yace "Am traveling Amira" ta dago tana kallonsa, ya gyada kai yace "Yeah, gobe xan tafi" sauke idonta kasa tayi, lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Tafiya xaka yi ba bar ni" ya tsura mata ido kafin yyi murmushi yace "Aiki xan tafi yi can, in sha Allah xan dawo when am done" ta kallesa hawayen idonta ya sakko tace "Toh yaushe ne xaka gama" ya wara Manyan idonsa yace "Nima ban sani ba, but da na gama xan dawo ai" kai kawai ta gyada masa amma kana ganinta kasan jikinta yyi sanyi, murmushi ya sake yi yace "Ba ga mama ba xata dinga kula da ke xan bar mata kudi ta dinga siya maki duk abinda kike so, just promise me baxa ki dinga damuwa ba that's all" murya can kasa tace "I promise, amma yaushe xaka dawo?" Dariya ta basa ganin ta yi tambayar daxu yace "Duk sanda kika samu lafiya kika fara cin abinci sosai sannan bakya damuwa xan dawo" xaro ido tayi tana kallonsa, yace "Yes" murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, sae ranan ya fara ganin murmushinta ya dinga kallonta ganin xata dago kanta yyi saurin dauke kai, tana wasa da dogayen yatsun ta tace "Toh naji" yace "Yauwa ko ke fa" wayarsa daya ya Ciro ya mika mata yace "Xan dinga kiran ki in sha Allah" karba tayi a hankali tace "Toh" yace "to tashi ki raka ni" Ba musu ta mike shi ma ya tashi ya nufi kofa sannan ta bi bayansa, a parlor ya tsaya yyi sallama da Dattijuwar ya kuma sanar da ita xai yi tafiya ta dinga masa addu'ar Allah ya tsare yace "Ameen Ngd mama, don Allah ki dinga sa mata ido bata son cin abinci" tace "In sha Allah kar ka samu damuwa" Dubu hamsin ya ba matar ta dinga siya ma khadijah duk abinda ta bukata, ya kuma sanar da ita komai babu gidan Dr Yusuf xai kawo masu, daga haka ya juya yana kallon khadijah dake ta kokarin ganin bata yi kuka ba yace "Toh mu je" har bakin mota ta rakasa kanta a kasa ya kara mata sallama ta kasa daurewa ta fara kuka, duk jikinsa yyi sanyi, a hankali yace "Look Amira ba dadewa xan yi xan dawo ba, ki daina kuka pls" kai ta gyada masa cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya tsare hanya" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da ido. Kamar kar Sudais ya bar kasar Khadijah ta fara samun lafiya sosai dattijuwar me kirki komai take so shi take mata kafin wani lkci duk babu ramar da tayi sai cikinta da ya fara fitowa, kullum a rana sudais xai kirata kusan sau biyar just to check if she is fine, idan bai kirata ba kuwa ta dinga damuwa kenan, a haka har watanni suka shude.