Sashe 52
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 3 min read
tace "Abuturrab amma tare da Iklima xa ku je" Ya hade rai yace "A'a ni ban ce xan je da ita ba mumy" mumy tace "Toh sai a fasa tafiyar ai" daga haka ta juya ta shiga dakin Anty Khadijah ta ga iklima xaune can karshen gado tayi tagumi tana rera kuka, Mumy tace "Sai ki shirya ku tafi gaba daya" mumy na fadin haka ta juya ta wuce, ko kunya babu iklima ta tashi ta fiddo sabon kayan ta da takalmi mai tsini da jaka, ta sha uban make up ta sa spec, ta feshe jikinta da turarurrukan uwarta sannan ta sakale mayafinta a kafada ta fito, dakin su baby ta shiga su ma har sun gama shiryawa baby na ganinta ta kwashe da dariya har da faduwa kan gado ta dinga kyakyatawa, Khadijah tayi murmushi ta dauke kanta, Baby ta kuma dagowa ta kalli Iklima ta kwashe da dariya, Iklima ta maka mata harara tace "Ai dama ke mahaukaciya ce" Baby ta mike xaune tace "You are not even ashamed of ur self, yanxu wa yace xai je da ke, har da wani sa dogon hill da spec, ji wani make up kamar na yan kasuwar tasha" Juyawa iklima tayi ta shiga dakin mumy, can sai ga ta ta fito tana huci tace "Mumy na kiranki" Baby tayi tsaki tace "Ae a haka xa ki kare da reporting din mutane" Dakin mumy ta wuce tana hararanta, har mumy ta gama ma baby fada bata ce komai ba, tana fita ta kira Khadijah suka sauka downstairs su jira ya Aliyu tana kumbure kumbure. Babu yanda Aliyu ya iya haka ya tafi har da iklima, baby ce gaban motar, iklima da Khadijah kuma a baya, babu abinda ya fi ba Aliyu takaici irin shegen make up din da tayi a fuska. Smart kids ice cream spot ya nufa da su, bayan ya siya masu ice cream da pizza da fries ya mayar da su gida duk da ba haka ya so ba amma saboda iklima ya fasa duk abinda yyi niyya. Ranan lahadi da daddare Anty khadijah ta dawo gidan, Mumy da Aliyu dake xaune parlor suka bi ta da kallo ganin yanda ta yi wujiga wujiga, bata yarda ta tsaya parlor ba sannu da gida kawai tayi ma yar uwar tata ta wuce sama da sauri, Aliyu ta kalli Mumy yace "Daga ina take mum?" Mumy tace "Allah kadai ya sani" Anty khadijah na shiga daki ta bude press dinta ta tura jakarta sannan ta rufe ta tube kaya ta shige bandaki, sai da tayi wanka ta sauya kaya sannan ta fito tana kwala ma siyama kira ta xo ta xuba mata abinci, xaunawa tayi parlor, Mumy dake ta kallonta tace "Lafiya na gan ki haka" da sauri ta kalli mumy tace "A ya kika gan ni?" Mumy tace "Atoh, kinga wani duhu da kika yi kamar warce taje kauye" Anty khadijah tace "Kauye kuma, Zaria fa nace maki xan je, kuma gashi har naje na dawo" Mumy tace "Toh Allah rufa asiri" Sai a sannan Aliyu ya gaisheta, fuska a murtuke ta amsa can ciki, ya mike yyi wucewarsa sama, tana kallon mumy tace "Ina d'a na saleem?" Mumy tace "Ya je Abuja jiya da kika tafi, ina jin daga can ma xai wuce Germany, toh wai ke da kika ce kwana biyu xa ki yi Khadijah ya aka yi kika dawo yau, jiya da safe fa kika tafi?" Anty khadijah ta hade rai tace "Kai Anty fati, to kwana biyun bai yiwuwu ba" daga haka ta mike ta wuce kitchen don xuba abinci ganin siyama bata sakko ba.