Sashe 89
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 5 min read
a parlorn, gidan ya hadu, sai dai fa bai kai na sudais ba, Har TV akwai a parlorn bayan kujeru da center table da dinning table da chairs a area din da aka tanadar don ajiye su, kasa xama khadijah tayi a parlorn, Sudais dake tsaye shi ma ya nuna mata kujera ta xauna, sai a sannan ta xauna cikin sanyin jiki, ya dau little sudais dake ta daga masa hannu wai ya daukesa, Sudais na kallon Nanny murya can kasa yace "Madam ina son ki min alfarma daya na xaunawa tare da su even if it's just for few years to come for the sake of this twins, I will pay all the money in sha Allah" Nanny da jikinta yyi sanyi tace "Ba damuwa yallabai, Allah ya saka da alkhairi" Nan take sudais ya bata check na shekarun da ya fada, sannan ya nufi Khadijah yana kallonta ya ajiye mata envelope din hannunsa a kafarta a hankali yace "Gashi Amira this is for my boys, da sunansu na siya gidan nan don haka na su ne, mallakin su ne" kasa cewa komai tayi tana kallonsa, ya durkusa gabanta a raunane yace "I have always wanted the very best for you Amira, like... sending you out to UK kiyi karatu ki xama likita, a ko da yaushe hakan yana rai na amma saboda kananun yaran ki.... I decided sai sun kai ko da shekaru biyu ne sai ki tafi tare da su.... Am sad I couldn't fulfill that but you can ur self, promise me ko bayan babu ni, xa kiyi karatu ki xama babban likita, I mean ki min alkawarin xa ki cika min wannan burin nawa a kan ki" jin bata ce komai sai kallonsa take a tsorace ya kamo hannunta yana kallon kwayar idonta, he understand she's shock, ya lumshe ido ya mika mata check na kudi, da farko kasa magana yyi can yyi gathering courage with a breaking voice yace "Am going Amira, this is a check of 20 million, I think that all I've got for now, kiyi kokarin ganin with this little am giving you kin inganta rayuwar ki da na boys din ki, sannan ki ci gaba da rike mutuncin ki na 'ya mace duk inda xa ki samu kan ki, I wish na yi kokarin nema maki Umman ki kafin in tafi, I wish na kwato maki hakkin ki a gun dangin mahaifin ki, amma duk hakan bai yiwu ba Amira, ki kyale su xa su mayar maki a lahira idan Allah ya yarda, as for the twins.." Kasa ci gaba yyi, yyi shiru na wani lkci bai son ta ga hawayen idonsa, can yyi karfin halin cewa "I knw i will always love them tamkar yaran da na haifa a cikina, kar ki bari su yi rashi na Amira, ki dinga masu abinda nake masu, I mean ki so su kamar yanda nake son su, you are all they've got now, ke kadai gare su, idan kuma kika samu abokin rayuwar da kika ga ya kwanta maki kiyi aure amma ki fara sanar da shi ke wacece, a duk xaman mu Amira idan na taba saba maki da sani na ko akasin haka ki gafarce ni" kansa a kasa yace "I think that's all, akwai foodstuffs da na siyo daxu a kitchen, goodbye Amira, it's great knowing you in my life, wishing u better future ahead...." Ganin xai tashi Khadijah ta sakko kasa ta rikesa ta fashe da matsanancin kuka cikin rawar murya tace "Na shiga uku, don Allah kar ka tafi ka bar ni ni kadai, you are all I have with my kids, ka ce min fa baxa ka taba barina ba, don girman Allah kar ka min haka Aliyu, idan ka tafi ya xan yi..." Kasa kallonta yyi, ta daura kanta a kafarsa tana kuka sosai cikin raunin murya tace "Kasan ni marainiya ce, I don't have anybody, ya xan yi da yaran idan ka tafi ka bar ni da su Aliyu, don Allah kar ka tafi ko don su, ban san inda xan ga ummata ba kar ka tafi ka bar ni ni kadai a duniyar nan" Hakan da khadijah ta fada yasa Nanny ta fara kuka tausayin khadijah da yan biyun ya cika ta, Sudais yyi iya kokarin ganin hawayen idonsa bai sakko ba amma hakan bai yiwu ba, ya dago ta da kyar shi ma hawaye na xubo masa yace "Life goes on with or without me Amira xaku yi rayuwarku da yaran, you just have to manage the little I gave you cos I knw living in Abuja is expensive, surely watarana xa ki hadu da ummanki har ma da dangin mahaifiyar ki, I have to go now saboda Mamina, baxan iya tsallake maganar ta ba kiyi hakuri, ke dai kiyi min alfarmar kula da yan biyun ki, kuma ki daina jin haushinsu ki ja su a jiki, su kenan gare ki a yanxu, kar ki shafa masu laifin mahaifin su" daga haka ya mike ya isa gun twins din ya duka yana kallonsu a sanyaye, dariya suka fara masa suna daga hannu ya daukesu, ya manna masu kiss gaba daya ya lumshe ido murya can kasa yace "Long life to you both in sha Allah my boys, Allah ya albarkace rayuwarku ku xamto *hasken rayuwar* mahaifiyar ku" tashi yyi ya nufi kofa trying hard to control his self, Khadijah na kuka sosai cikin sanyin murya tace "Thanks very much Aliyu, Allah ya biya ka abinda kayi mana, and I will always pray for you in my life, kai din ka xame min _hasken rayuwa_ a lkcn da rayuwata tayi min duhu, daga ranan da na fara ganin ka ka yaye min bakin cikin dake tare da ni, you will always be the *light of my life* Aliyu" Sudais bai iya ya juyo ba har ya isa kofa, yaran na ganin xai fita suka fara kuka, bai yarda ya juyo ba har ya bude kofar ya fita yana goge hawayen idonsa, yana fita kuma ya bude wayarsa ya cire sim din da Khadijah ta san sa da shi ya jefar nan cikin flowers din gidan ya fita ya hau motarsa, and that was how Barrister Aliyu left Khadijah and her twins.