Sashe 63
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa tashi sallan asuba Khadijah tayi washegari ta dalilin xaxxabin da ya rufe ta, jin an bude kofar ward din ta bude idanuwanta a hnkli taga gari ya waye sosai, likitan da mutumin jiya da ya kira da Sudais suka shigo ward din a tare, tun daga bakin kofa sudais dake sanye da milk jallabiya ke mata wani kallo har karaso gadon yace "jiya da na baki waya wa nace ki kira?" Khadijah ta mike xaune da kyar ganin ynda ya hade rai ta marairaice tace "Relatives dina" ya kara hade giran sama da ta kasa yace "Then why didn't you call dem?" cikin rawar murya tace "I don't have anybody to call, ni marainiya ce, my father is late so also is my mum, My step mum....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, cikin tsawa yace "Karya kike yi, shut ur mouth plss" likitan dai rungume hannu kawai yyi yana kallona yana murmushi, ta hade kai da gado tana kuka cikin rawar murya tace "ku yarda dani don Allah, wallahi ni bana karya, laifi nayi ma step mum dita tace min in bar mata gidanta, I love my step mum and she loves me same, but tace in tafi sbda laifin da nayi, she raised me up as a mother even after my late dad passed away 5 years back, don Allah kada ku ce in tafi ban san kowa ba a garin nan ban taba xuwa ba, ku taimakeni ku kaini gidan marayu in dinga kula da yaran wajen don Allah" tsawa likitan yyi mata da ya firgitata ta dago da sauri, yace "You are mad, wa xa ki raina ma wayo, ni ko wannan da ke kusa dake?" Ya fadi hakan yana nuna sudais, Shiru tayi tana kallonsa, kafa mata ido shi ma yyi, can ya karaso kusa da ita yana kallon kwayar idonta da kyau, ya kai hannunsa ya bude eye lids dinta, can ya kalli fingers dinta sai kuma ya kalli Sudais dake tsaye, daga kafada yyi ya nufi kofa yace "I have better patients to attend to Sudais..." daga haka yyi ficewar sa daga cikin ward din, a sanyaye khadijah ta kalli Sudais dake mata wani kallo yana rungume da hannunsa, harara ya watsa mata bayan mun hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, muryarsa ya daki ear drum dinta, "Wani laifin kika yi ma mum din taki, kuma daga wani gari kike? Kina min karya xan gane kuma daga nan station xan kai ki" Shiru tayi tana kallonsa hawaye na ci gaba da sakko mata, cikin sanyin murya tace "Daga kano na xo" yace "Wato kin saba tafiya garruruwa kenan ko" ta girgixa kai da sauri tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "Wallahi A'a" yace "Toh wani laifin kika yi mata?" Share hawayen idonta ta shiga yi a hankali ta hadiye wani abu da ya tsaya mata, can ta sakar masa kuka tace "Kilan baxa ka min taimakon da nace ka min ba idan ka ji dalilin bari na gida" strictly yace "Malama ki bude baki ki gaya min, stop wasting my time xan je aiki" jinginar da kai tayi da gadon ward din tace, "Duk abinda xan fada maka ka yarda dani sbda Allah, ni bana karya, I knw d consequence of it.... Domin ka min taimakon da nace ka kai ni orphanage yasa xan fada maka ni wacece" Bai tanka ta ba hakan yasa a hankali tace "I lost my mum at a very tender age, and my beloved last year" ta kallesa taga he is listening but not looking toward her direction, ta lumshe ido, a haka ta fara basa labarinta tun daga farko har xuwa yanxu da yake gabanta, bbu abinda ta boye ma Sudais, Kallonsa tayi a karo na farko tun da ta fara gaya masa ita wacece, hawaye masu xafi suka shiga xubo mata, Sudais ya dinga kallonta da wani expression da ta kasa fassarawa a fuskarsa, tana girgixa kai a raunane tace "I told you all but the blank truth about me, believe me plss" kasa ce min komai yyi sai bayan kusan minti biyu yana nuna ni da yatsa da wani irin mamaki yace "You mean... You are pregnant?" Ta gyada masa kai a hankali tace "That's what the Dr told me and my step mum" Jinginar da kansa yyi jikin bango yana kallon saman ward din ko kiftawa bbu, bai kuma ce min komai ba har na kusan minti uku, Khadijah dai sai kallonsa take don bata san tunanin da yake a xuciyarsa ba domin kuwa duk wanda ya gan sa yasan yyi nisa tunanin da yake, bude kofar aka yi duk suka kalli kofa, Dr Yusuf ya shigo yana kallonsa da kyau yace "Ya? Ka gama sauraren karyar ta Malam?" Sudais bai ce komai ba ya shiga shafa uban gashin dake kansa, likitan yyi murmushi yace "Very good then, naga kamar har karyar tayi tasiri a xuciyar ka" Likitan ya karasa kusa da khadijah yana kallonta da kyau yace "Are you married?" Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, wani murmushin ya sake yi ya kalli Sudais, Sudais ya lumshe manyan idonsa ya bude su a hankali yace "Yea xaka cire mata cikin soon as possible....." Wani kallo Dr Yusuf ke yi masa, Sudais ya dafa kafadarsa yace "Yeah... She told me about d pregnancy, an illegal one at it's early stage, i think you just have to flush it Yusuuf, I will pay what ever amount it will take" tunda ya fara magana khadijah ke kallonsa baki bude, can ta fashe da kuka tace "Noo plss, it's illegal but it doesn't deserve that, Allah xai yi fushi da ni, baxan iya ba..." wani mugun kallo Sudais ke mata ya karaso kusa da ita cikin tsawa yace "You are very very stupid, shegen xaki haifa?" Ta kuma rushewa da kuka tace "Eh, saboda Allah ne ya bani, kuma it's not my fault it came this way, beside soul din ba shi da laifi da har xan xubar da shi..." Yusuf ya rungume hannu yana kallonta, Sudais ma wani kallo yake mata lkci daya yana mamakin furucinta cos she look young to think that way, ya matsa dab da ita yace "Then ya xama dole ki koma gidansu Aliyu kika kirasa ko wa???" Khadijah tayi shiru tana kallonsa hawaye na xubo mata, ido ya kafeta da shi yana jiran jin abinda xata ce, ta sauke idonta a hankali tace "Toh me xan ce masu?" Strictly yace "Abinda likita ya gaya ma ke da Ummar ki" tana share hawayenta tace "Toh amma ni yanxu bani da kudin mota" yace "Xan baki" juyawa likitan yyi ya fita, shi ma ya nufi kofa kafin ya fita ya juyo ya kalleta yace "Ki sameni reception yanxu" daga haka ya fita, ta sakko a hankali ta dafe gado jin jiri, da kyar ta karasa reception din sbda jirin dake debanta tana isa ta xauna kan kujera ganin baya gun, office din Dr Yusuf sudais ya shiga, Dr Yusuf yace "What are you trying to do Sudais?" Sudais ya shafa kansa a hankali ya xauna kan table dinsa yace "I don't really knw Yusuf, kawai nayi analyzing naga babu karya a labarinta, I tried hard to figure out...." Yusuf ya katse sa da sauri yace "Da alama lauyancin ka bai fada maka gaskiya ba yau, look at you... sau nawa muke ganin cases irin wannan, tayi ciki ta gudu ta bar gida ta xo nan ta shirga maka karya a matsayin ka na barrister har karyar yyi sinking kan ka? Don't let me call u a disgrace to ur profession..." Sudais ya girgixa kai yace "Babu karya a xancen da ta min, and profession dina yasa nayi figuring din hakan, she told me nothing but the truth" Dr Yusuf yace "Toh naji gaskiya ta fada maka, what do you intend doing now?" Shiru Sudais yyi yana kallonsa, can ya dauke kai cikin damuwa yace "I don't knw frnd, I have never being confuse like this all my life, Yusuf just look at her, she is too young, baxa ta wuce sa'ar Rabi'ah ba, had I known wllh da ban tsaya a motata ba jiya" Dr Yusuf yace "Toh ko gidanku xaka kai ta" sauka Sudais yyi da sauri daga kan table din yana xaro manyan idanuwansa yace "Gun wa Yusuf?" Yusuf yyi dariya yace "Mami wai da" Sudais yace "Mami ta kashe ni kenan, cewa ma xata yi ni nayi ma yarinyar cikin, kai ma kasan ko hauka na fara baxan fara kai ta hanyar gidanmu ba, what for?" Yusuf dai sai dariya yake sanin wacece mahaifiyar sudais, Sudais ya tabe baki yace "Wani lkcn ma d'an Adam na xaman xamansa yake dauko ma kansa matsala da kansa a rayuwa if nt meye haka na sa kai na ciki??" Yusuf yace "Kawai ka ka ita orphanage din da tace xai fi" Sudais yace "In dai kai ta can gidan su dan iskan da yyi mata cikin" Yusuf yace "Wa yaga bata lkci" Sudais ya nufi kofa yace "Muyi waya frnd" Mikewa Yusuf yyi ya bi sa suka fita. Ba tare da Sudais ya kalli khadijah dake ta xaune duk ta gaji a reception ba yace "Mu je" mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, gun motarsa dake parking space ya nufa, ya bude ya shiga, ganin bata shiga ba Yusuf yace "sai ki shiga" a hankali ta kai hannu ta bude motar ta shiga, Sudais na kallon Yusuf yace "I will give you a call" Yusuf yace "Alright then" daga haka ya ja motar muka bar asibitin, bbu wanda yace komai cikinsu, yyi driving din kusan minti sha biyar suka iso wani anguwar masu kudi, nesa da gidansu Sudais yayi parking, ba tare da ya kalleta ba yace "I will be right back" daga haka ya fita ya fara tafiya, tafiyarsa kadai ma abun kallo ne, ya wuce gidaje kusan hudu kafin ya xo na su, Mahaifiyarsa Mami ce xaune parlor da wata bakuwa da tayi, ya karasa ya gaishesu da ladabi, bakuwar ta amsa da fara'a tace "Wannan uban gashin da aka bari fa Barrister, sai kace a turai" Ya kirkiri murmushi yace "Sunna ce...." Katsesa Maminsa tayi fuska daure tace "A hakan