Sashe 64
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read
da ka bar shi irin na wa ends basu da mafadi, am very serious kada ka shigo min gida anjima baka asks gashin nan ba, ka jira idan ka koma UK din sai ka kara barin gashin, wnn iskancin kam ba a gidana ba" kansa a kasa yace "Toh Mami" daga haka ya mike ya wuce bedroom dinsa, press ya bude ya fiddo wani makulli ya sa aljihu sannan ya fito yayi masu sallama ya fita, bacci ya tadda khadijah ke yi, dauke idonsa kanta yyi ya tada motar ya bar layin, tafiyar wani minti sha biyar din yyi ya isa wani anguwar daban yyi parking a gaban wani gida, ana ganin gidan ansan sabon gini ne, ya fita ya bude gate din gidan da makulli sannan ya dawo ya ja motar ciki yyi parking ya fita ya koma ya rufe gate din, tuni khadijah ta bude ido tana bin gidan da kallo, dawowa yyi yace "Come down" ba musu ta fito, tafiya ya fara yi xuwa entrance din main house din ganin haka ta bi bayansa sai dai gabanta faduwa yake kawai, ya sa makulli ya bude kofar shiga parlorn ya shiga, kasa shiga tayi tana lekan parlorn, ya juyo yana kallonta, hawaye ne cike idonta, wani kallo yyi mata ya shiga parlorn ya bar wajen, a hankali ta taka ta bi bayansa, tuni ya wuce bedroom ita kuma ta xauna nan kan kujera a parlorn, bayan wani lkci ya fito yace "Ki shiga ciki kiyi wanka, xan fita in dawo yanxu" daga haka ya fita ya rufe kofar, tashi tayi da kyar ta shiga dakin da ya fito, towel ta gani kan gado sai sabulu ta karasa ta dauke su ta bude kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga taga har ya hada mata ruwa me dumi, wanke bakin ta ta fara yi da mouth wash, bayan kusan minti ashirin ta fito daga bayin da kayan da ta cire a bucket ta wanke, sai taji ta samu karfi jikinta, hijab kadai ne da bata wanke ba ta daura kan towel din jikinta sannan ta fito parlor, wani kofar dake parlor ta shiga taga kitchen ne, ta dauko sweeper da mop ganin gidan is very dusty, tun daga dakin da tayi wanka ta fara gyaran ta fito har parlor duk da sanyin da take ji sosai, tana goge goge a durkushe ya shigo parlorn ya ajiye ledojin hannusa ba tare da ya kalleta ba yace "I didn't tell you to do anything madam, ga kaya nan ki shiga ciki ki canxa ki fito yanxu" ta mike tsaye tace "Toh nagode" bai tanka ta ba ta dau ledan ta shiga dakin, dogayen riguna ne na kanti da undies sai Hijab biyu da perfumes, cikin lkci kankani ta gama shiryawa ta fito parlorn, xaune yake ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yayi nisa tunanin da yake, why is he involving him self in such case ya fa san daga irin gidan da ya fito ya san waye iyayensa, jin ta fito tun da ya kalleta sau da ya bai sake kallonta ba har ta iso nesa da shi ta durkusa tace "Na sa kayan" ledan abinci ya nuna mata yace "Breakfast" ta mike ta isa gun ledan ta bude, a hankali ta ja baya tana rike numfashinta sbda aroma din abinci, Fried Irish ne da soyayyen kwai da plantain sai ketchup, yace "You can go to the kitchen and make a cup of tea for ur self" kai kawai ta gyada masa, ta mike ta shiga kitchen din tana fatan ta iya shan shayin, ta gama hadowa ta fito, ganin kallonta yake bayan ta ajiye shayin ta dau Irish daya a hankali ta kai ba ki, ji tayi cikinta ya fara hautsinewa tun kafin ta fara taunawa, ta dau shayin ta kai baki da sauri don ta kora, tana sha tayi saurin ajiye cup din da sauri ta shige dakin da tayi wanka tun kafin ta karasa cikin bathroom din aman ya xubo mata, tun da ta fara amai sai yau tayi Wanda ya galabaitar da ita don bbu komai cikina, ta kasa motsi wajen duk jikinta ya mutu, ganin shadow dinsa ta juyo hawaye kwance fuskarta, tausayi karara ta gani a kwayar idonsa, yyi saurin dauke kai murya can kasa yace "Sorry" daga haka ya shiga bayin ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya xuba ruwa wajen, kasa tashi tayi ta jingina da bango, ganin jira yake ta tashi, ta runtse ido tayi karfin halin tashi bata xarce ko ina ba sai kan gado ta fada kai tana mayar da numfashi, ya karaso yace "Toh me xa ki ci yanxu" kai kawai ta iya girgixa masa, yyi jim yana kallonta kafin ya juya ya fita a koma parlor, xaunawa yyi yana tunanin how many hours will take them to kaduna.