← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 168

Sashe 128

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude mata motar Aliyu yayi yana kallonta, ta ki kallonsa tana dai tsaye kamar me contemplating ta shiga ko kar ya shiga, a hankali ta karasa gun motar daga karshe ta shiga ya rufe, sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar. Sai da suka hau saman titi yace "Wani anguwar kike?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Tun da Maryam ta gaya maka gidanmu daya da Dr Ayman nasan ai baxata rasa gaya maka address da house number ba" Murmushi kawai Aliyu yyi yana ci gaba da driving dinsa bai ce komai ba, sai da suka iso street din ya kalleta yace "I only know the street...." ta fada masa number din gidan, yana isa dai dai gidan yayi parking yana dubanta yace "Wani schl din Shureim ke xuwa Iman?" Sai a sannan ta kallesa tace "I don't think I have to tell you" Yana shafa kansa yace "It isn't an offense ai Iman" ta bude motar ta fita tace "Thanks for the ride" murmushi kawai yayi ta wuce ciki ya bi ta da kallo, tabe baki Khadijah tayi ganin babu motar khaleel a garage ta fiddo makullinta cikin jaka ta bude kofar ta shiga ciki, wanka tayi sannan tayi sllh ta canxa kaya ta fito parlor, xaunawa tayi tana tunanin abinda xata girka, can ya mike ta wuce kitchen din, shinkafa da miya tayi deciding tayi sanin Shureim na son sa sosai, tana parboiling shinkafa taji shigowar motar khaleel gidan, da gudu ta fita parlor ta isa gun kofa ta sa makulli sanann ta koma kitchen ta ci gaba da abinda take, bell taji an danna, ta hade rai ta tura kofar kitchen din, ba a sake dannawa ba sai ringing din wayarta dake parlor ta ji, ta bude kofar ta fita ta dau wayar tana kallon screen din, ganin khaleel ke kiranta da har xata ajiye sai kuma ta daga ta kai kunne ta ki cewa komai, yace "Bacci kike ne?" Tace "What about that?" Yace "Ohk, naga takalman ki kin bari a waje, and ki fito ku gaisa da jawahir" Wani kallo tayi kamar yana gabanta tace "For what?" A hankali yace "Am waiting Khadijah...." daga haka ya katse wayar, mamaki ne ya cikata, a kan wani dalili xa ta gaisa da jawahir, tsaki tayi xata ajiye wayar text ya shigo nasa, ya budewa tayi tana kallon content din, "Plsss" abinda ya turo mata kenan, ta turo baki sai kuma ta harari kofar, a hankali ta isa gun kofar ta bude, tsaye ta gansa shi da jawahir din, suna hada ido jawahir tace "Sannu Khadijah ya gida?" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Lafiya lau, fatan kin xo lafiya" Jawahir tace "Alhmdllh, ya hakuri?" A hankali Khadijah tace "Alhmdllh nagode" kallonta kawai khaleel yake, Jawahir tace "Dama Dr yace in taho in maki gaisuwa ne" Khadijah tace "Ayya nagode, baxa ki shigo ba" khaleel na kallon jawahir yace "Shiga sai kiyi sllh" jawahir tace "Toh bari in yi" daga haka ta shiga parlorn Khadijah, ba tare da Khadijah ta kallesa ba ta rufe kofarta fuska daure, murmushi kawai khaleel yyi yana kallon kofar. Jawahir na kan darduma xaune parlorn Khadijah ta kawo mata abinci a plate, jawahir tace "Ayya na ci abinci Khadijah, am not hungry" Khadija tace "Haba ki ci ko kadan ne" Jawahir tace "Da gaske bana jin yunwa ki bar sa kawai" juyawa kawai Khadijah tayi rike da abincin ta koma kitchen, tana fitowa jawahir ta mike tace "Toh nagode bari in je" Khadijah tace "Welcm" daga haka ta fita, tana ji ta bude apartment din khaleel ta shiga, tabe baki Khadijah tayi, ta ja tsaki ta wuce daki, mayafinta ta dauko ganin Shureim ya kusa tashi a schl, tana fita apartment dinta ta sa makulli ta nufi waje, cab ta samu ya kai ta har makarantar, Rungume ta Shureim yayi bayan ya fito daga cikin makarantar yana kallonta yace "Anty me yasa uncle bai xo ba" Khadijah ta hade rai tace "Don't ask me that again" daga haka ta kama hannunsa suka shiga cab din, suna isa gida ta biya mai cab din ta wuce ciki tana rike da hannunsa, sai kallon kofar khaleel take ta tabe baki ta bude kofarta ta shiga parlor da Shureim, makulli ta sa ma kofar, ta Shiga bedroom da shi ta cire masa uniform, tayi masa wanka ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi sanan ta sa yayi sllh, suka fito, a plate daya ta xuba masu abincin, tana ci a hankali tana kallonsa, muryarsa taji yace "Anty yaushe Sudais xai dawo? Umma tace min after one month, kuma ai one month yayi ai koh?" Khadijah ta sauke idonta daga kallonsa tana ci gaba da cin abincinta tace "Nima ban sani ba, sai dai anjima idan Umma ta kira ka tambayeta" ya langwabar da kai yace "Ohk" kallon wayarta dake ring tayi taga sabon number ke kiranta, ta dauka ya kai kunne, muryar Aliyu taji yace "Iman" a hankali tace "Na'am" yace "Fito ki amshi sakon Shureim din" kallon Shureim tayi tace "Ohk" daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon Shureim tace "Mu je ka rakani Shureim" ya tashi ta dauko plate ta rufe abincin, ta dau tissue ta goge masa bakinsa sannan ta dauko masa takalmansa ya sa suka fita, ba dai dai kofar gidan yayi parking ba, Khadijah na rike da hannun Shureim ta tsallaka xuwa side din da yake, daga cikin motar Aliyu ke kallonsu ko kiftawa babu har suka iso dai dai inda yayi parking, a hankali ya bude motarsa, Shureim na ganinsa ya nufe sa da gudu cike da murnar ganinsa Aliyu ya daga sa ya rungume sa ya lumshe ido, cike jin dadi shureim yace "Uncle ka kai ni wajen mama plss" Aliyu ya dago kansa yana kallonsa yayi pecking goshinsa yace "Mama tana Nigeria ai, idan kun yi hutu sai in kai ka" Shureim yace "Uncle plss ka tafi da ni" Aliyu ya kalli Khadijah dake wasa da ring din hannunta, a hankali yace "Thanks for coming out Khadijah" Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, jin bata ce komai ba ya bude bayan motar ya fiddo babban leda, Shureim yace "Uncle Anty ta bani irin wannan chocolate da kake bani da Sudais..." Aliyu ya wara ido yace "Da gaske?" Yace "Yes uncle" ya kalli Khadijah ya langwabar da kai yace "Toh Anty ki bari muje in siyo masa irin chocolates din, sai mu dawo yanxu" Khadijah bata ce komai ba, Aliyu yayi kasa da murya yace "Ko xa ki raka mu?" Girgixa kai tayi tace "No way" daga haka ta tsallaka ta wuce ciki abun ta, Aliyu ya bi ta da kallo kafin yayi murmushi ya xaga ya bude front seat ya xaunar da Shureim, ya dawo ya shiga driver seat ya tada motar ya bar street din. Khadijah na dai dai apartment dinta khaleel ya bude motar ya fito rike da makulin motarsa, ganinta yace "Let me go pick Shureim, na sha'afa wllh" a takaice tace "You don't worry na dauko sa, Ni ban sha'afa ba" daga haka ta Shiga ta rufe kofarta, ya fi minti daya a tsaye kafin ya koma nasa apartment din. Shopping mall din da Aliyu ya kai Shureim kusa da gidan kanwar Abbansa yake, don haka yana gama masa shopping ya shiga gidan tare da Shureim, Tasowa Maryam dake xaune parlor da Deejah tayi ganinsa ta tafi da sauri dau yaron ta rungumesa tace "Waow yau ga Shureim a gidanmu, Yaya Aliyu a ina ka samo mana shi? Jiya kuwa muka hadu da mum dinsa a cafteria a schl" Maryam ta kalli Deejah dake parlorn tana kallon Shureim da expression na Waow a fuskarta tace "Kin tuna warce muka gani a cafteria jiya?" Deejah ta xaro ido tace "Wai Khadijahr nan da nace maki suna kama da Safeenah??" Maryam tace "Yauwa ita" da mamaki Deejah tace "Kar ki ce min ita ta haifi yaron nan?" Maryam tayi dariya tace "Yaronta ne mana, yan biyu ne ma, daya ya rasu" lkci daya jikin Deejah yayi sanyi ta mike tace "Allah sarki" Aliyu dai bai tanka su ba ya wuce sama bayan ya amshi Shureim hannun Maryam don kai ma Antyn sa shi, Deejah ta bi su da kallo murya can kasa tace "but naga yaron na kama da cousin din naki ai, I mean sosai fa" Murmushi kawai Maryam tayi sai dai bata ce komai ba, bude kofa aka yi sai ga jawahir ta shigo, wurgar da takalman kafar tayi, ta jefar da jakar hannunta kan kujera ta xauna, Deejah dake ta kallonta tace "Ke kuma meye haka? me ya faru?" A fusace ta fara magana tace "Wllh Anty deejah na gaji da Ayman, abinda yake min ya fara isata, am just tired" Maryam ta xauna kusa da ita tace "Toh fah, me kuma ya hada ku?" Mikewa Jawahir tayi rai bace tace "Don rainin hankali sai yayi ta wani hada ni da yarinya da ban san meye tsakaninsu ba, I really want to know wacece yarinyar nan, sanann ta wani dinga daga min hanci tana amsa min da kyar kamar dole.... Da yaje Nigeria gaba daya lkcn sa ita yayi dedicating ma, ashe ma gidansu daya a nan ban sani ba sai daxu da ya fita yake gaya min, Ni kuma abinda yasa ma na sake ma yarinyar fuska tun farkon da muka hadu a Nigeria naga tana min yanayi da Safeenah ne, ban da haka tayi kadan in ganta da saurayina in raga mata, sannan ni a tunani na matar aure ce don ina ganin yaran nan nasan nata ne but now I am totally confuse...." Deejah ta kamo hannunta a hankali tace "Kilan it's not what u are thinking lil sis, may be they are just frnds and neighbors, Kar ki bari shaidan ya ci galaba a kan ki, na kuma san ki da hakuri sosai jawahir so meye nasa wannan a ran ki?" Kamar xata yi kuka tace "Anty da kyar fa take amsa min magana idan na mata, kamar ma haushi na take ji shi kuma sai yayi ta sa ni in mata magana, to idan ba budurwarsa bace ita me yasa xata dinga haka" Deejah ta sauke ajiyar xuciya tace "But
Chapter 128 · 0% Book details