← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 168

Sashe 129

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 7 min read

ni dai she was very free with me da muka hadu a cafteria jiya" Jawahir ta jinginar da kanta jikin kujera cike da damuwa bata ce komai ba, tausayinta Deejah ta dinga ji, Maryam dai na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, mikewa Jawahir tayi ta dau jakarta ta wuce sama, Xaunawa Maryam tayi, Deejah na kallonta tace "Maryam ko dai budurwar Ayman ce Khadijah kar ki boye min?" Maryam ta bude ido tace "A'a gaskiya ban sani ba, ni ban ma taba ganinsu tare ba ko a schl" Tare Aliyu ya sakko da Hajiya Mariya dake rike da Shureim, shi kuma yana rike da ledan na lotion da turaren yara da small mum din tasa ta ba Shureim, Maryam na kallonsu tace "Ya Aliyu dama ba kwana xai yi ba" Aliyu ya kalleta yace "Aa" Hajiya Mariya ta xauna kan kujera tana kallon Shureim dake gabanta tace "Ka gaida mumy ka ji boy?" Ya wara idanuwansa irin na Aliyu yace "Mumy ai tana can Nigeria, Anty xan gaida maki" Murmushi Hajiya Mariya tayi tana shafa kansa tace "Toh ka gayar min da Anty son" Aliyu ta kalla tace "Toh yaushe Antyn xata xo ta gaisheni" Aliyu yyi yar dariya yace "Ai Antyn nan sai a hankali ba xuwa xata yi ba" a hankali Hajiya Mariya tace "Kar ka damu, Allah xai dai dai ta ku ko don albarkacin yaron nan" murmushi kawai Aliyu yyi bai ce komai ba ya kama hannun Shureim xa su fita yace "Toh bari in mayar da shi mum, it's getting late" Shureim ya daga ma Hajiya Mariya da ta bi sa da kallo ganin sak mahaifinsa yana daga mata hannu, mikewa Maryam tayi ta bi bayansu, sai da suka fita waje ta kamo hannun Shureim ta durkusa tana gyara masa hular sweater dinsa tace "Darling ni baxa kace min bye bye ba" Dariya yayi yana kallonta ya daga mata hannu yace "Byee" mikewa tayi tana murmushi ta daga masa hannun ita ma sannan ta ce ma Aliyu sai ya dawo ta juya ta koma ciki, Aliyu ya sa Shureim mota sannan ya xaga ya Shiga ya tada motar ya nufi gida da shi, sai da suka kusa isa gidan ya juya yana kallonsa yace "Wani school kake xuwa Boy?" Shureim ya fada masa sunan makarantar, yace "Did you like the schl?" Gyada masa kai Shureim yayi, Aliyu yyi parking dai dai gidan yana kallonsa a hankali yace "Anty ce ta kai ka schl din?" Shureim yace "A'a uncle dina ne ya kai ni" Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba, can ya dauko wayarsa ya shiga kiran Khadijah, Tana xaune parlor tana karatu kiran ya shigo wayarta, tana ganin number ta gane ta daga ta kai kunne, Aliyu yace "ki d'an fito ki dau Shureim" Katse wayar tayi ta mike ta shiga daki ta sa hijab ta fito, kamar mai tausayin kasa take tafiya har ta isa inda motar Aliyu yake, fitowa yyi daga motar ya xagaya ya bude side din Shureim ya sauko da shi, Khadijah ta karaso ta kama hannun yaronta ba tare da ta kalli Aliyu ba tace "Sai da safe" Riko Hijab dinta yayi yana kallonta, ta juya suna hada ido gabanta ya fadi tayi saurin sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "Sai da safe kuma? baki amshi sakon sa ba" Bata ce komai ba ya saketa ya bude bayan motar ya dauko babban leda ya dau ledan da Hajiya Mariya ta ba Shureim ya sa a ciki da ledan da yayi masa shopping duk ya hada su waje daya ya mika mata, karba tayi yace "Xa ki iya" Bata ce komai ba ta kama hannun Shureim ta fara tafiya, ya bi su da kallo, Shureim ya juya yana daga masa hannu, murmushi yayi ya daga masa hannun shi ma a sanyaye har suka wuce ciki. Manyan sweaters da head warmer ke cikin ledar da Aliyu ya bata na Shureim sai kaya kala hudu, ta bude daya ledan taga chocolates, biscuits sweets da dai abubuwan ci na yara, ta bude ledan da Hajiya Mariya ta basa taga lotions masu tsada da turare, tabe baki tayi ta mike ta wuce ciki da kayan, sai da ta ajiye kayan inda ya kamata a daki sannan ta fito da ledan chocolates din parlor, turus ta tsaya ganin khaleel xaune parlorn, ta dinga bin parlorn da kallo ganin bata ga Shureim ba, Mikewa khaleel yayi yana kallonta, sake ledan hannunta tayi ta juya da sauri xata koma ciki yace "Khadijah" tsayawa tayi amma ta ki juyowa, kawai ganinsa tayi gabanta yana kallonta, tayi saurin juyo masa baya, a hankali yace "Gaya min me na maki?" Ta turo baki tace "Toh ni na ce ka min wani abu ne?" D'an murmushi yayi yace "Saboda Aliyu kika canxa min Khadijah?" Shiru tayi ta rasa ma abinda xata ce masa, lkci daya jikinta yayi sanyi, jin shi ma bai ce komai ba ta juyo a hankali tana kallonsa, hawaye ya cika idonta tace "Me yasa xan canxa maka saboda Aliyu?" A sanyaye yace "Nima ban sani ba Khadijah" hawaye idonta ya xubo tace "Ko dai kai ne ka canxa min saboda budurwar ka" tana fadin haka ta fashe da kuka, kallonta ya dinga yi shi ma jikinsa yayi sanyi, da wani expression fuskarsa yace "Why? Why will I change because of Jawahir?" tana hararensa cikin kuka tace "Toh nima me yasa xan canxa saboda Aliyu?" Ya lumshe ido ya bude a hankali yana kallonta, rasa abin fadi yayi, har ransa yake jin kukanta, ya bude hannayensa cikin sanyin murya yace "Can... I console you?" Make kafada tayi ta juya masa baya, ya lumshe idanuwansa a hankali ya rungumota, cikin sanyayyan muryar sa yace "You know I love you Khadijah, and... I want you to be the mother of my kids, i want to marry you Khadijah, but you met me with Jawahir, I was with her before you, kin ga baxan mata walakanci ba saboda ke, jawahir na da saukin kai sosai, she don't have problem, and I don't want to betray her... Beside ita daban a rai na haka ke ma, Give me a chance to show you how much I love you plss Khadijah" kasa cewa komai Khadijah tayi, duk gaba daya jikinta yayi sanyi, jin tayi shiru ya juyo da ita a hankali yana kallonta, Bata yarda sun hada ido ba ta sulale nan kasa ta xauna, dukawa yayi gabanta yana kallonta murya can kasa yace "Say something plss Khadijah... Nace Ina son auren ki baki ce komai ba" Ta hade kai da gwiwa jin hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace "But Barrister Sudais...." Sai kuma ta fashe da kuka, ya dago kanta gabansa na faduwa, da kyar ya iya cewa "what about him Khadijah?" Tace "He proposed before you..." Shiru yayi yana kallonta ko kiftawa babu, a sanyaye tace "He said he want to marry me, and you know I can't tell him no Doctor, aure ma bai isa na biyasa abinda ya min a rayuwa ba, he deserves more than that from me, though nasan 6 years back I will confess I was in love with him, but yanxu I only respect him as someone that brought light to my life after my Lord, sai gashi ya dawo yace yana son aure na, baxan iya cewa bana son Sudais ba, baxan iya cewa baxan auresa ba, but I am afraid of his wife" shi dai khaleel bai ce komai ba, kana ganinsa kasan jikinsa yayi sanyi sosai, mikewa yayi a hankali bayan few seconds yace "Ohk then, Khadijah, Allah yasa hakan yafi alkhairi, wishing you all the best" daga haka ya juya xai fita ta tashi da sauri hawaye na sakko mata tace "But I know I love you so much Dr, bayan Sudais you are the next in my life, da ba don kai ba da ban san abinda xai sameni ba few months back, you made me lively once more in life, may be...." sai da ya isa bakin kofa ya juyo yana kallonta ya katse ta yace "Forget I did that to you Khadijah" daga haka ya fita, ta bi sa da ido xuciyarta na bugawa.
Chapter 129 · 0% Book details