Sashe 153
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read
iya shigowa gidan, Baby har ta gaji da lallashi tayi tagumi tana kallonta, yau kam tasan yayanta xai sha lallashi, d'an murmushi tayi dai dai lkcn da wayarta ya fara ring, Hafsat ta mika mata taga Aliyu ke kiranta, kallon khadijah tayi kafin ta daga ta kai kunne hade da sallama, shiru ya d'an yi kafin yace "Ku fito sai a ajiye ku gida yanxu" Tace "Toh" kamar khadijah taji abinda aka ce ma Baby tana kallonta a tsorace tace "Waye ya kira ki?" Baby ta sauke idonta tace "Mijin ki, mu xa mu wuce yanxu Iman, Allah ya bada xaman lafiya" khadijah ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku, me yasa baxa ku kwana ba don Allah kar ku tafi, ki bani wayar xan masa magana" dariya ta ba baby amma bata yi ba tace "Gobe fa da safe xan xo Iman" cikin kuka sosai Khadijah tace "Don Allah ki rufa min asiri ki kwana" Baby tace "In dai gidan nan ne wllh baxan kwana ba, gwara ki hakura gobe in dawo, idan kuma kika ban haushi in ki xuwa goben ma, ko a kauye an daina haka kina abu kamar wata yarinya..." Dariya kawai Hafsa take don khadijah ta bata dariyan, Baby ta mike ta hade rai tace "Mu je Hafsah, ji wani abu da take fa kamar yar yarinya, ko yara sun daina haka, balle ita wayayya" Da haka baby ta samu fa fita Hafsat na biye da ita, Ban da kuka babu abinda khadijah take tana kallon kofar har suka fita suka rufe, Baby ta ji tausayin ta har ranta, amma tasan idan ba haka ta yi mata ba sai ta iya ma biyosu, A waje ta tadda Aliyu tare da Sudais a tsaye jikin motar sudais din, da alama su suke jira, Baby tayi kasa da kanta tace "Ina yini yayanmu" yace "Lafiya lau" Hafsat ta gaida Sudais sannan ta gaida Aliyu tayi masa fatan alkhairi a aurensa, murmushi kawai yyi bai iya yace mata komai ba, Sudais yace "Alryt, sai da safe Dr" Aliyu ya kallesa a hankali yace "Baxa ka shiga ba?" Ya bude motarsa yana d'an murmushi yace "Gobe xan xo in sha Allah" Aliyu bai iya yace masa komai ba, can ya kalli Baby yace "Ku shiga xai yi dropping din ku gida" Ta d'an buda ido, Aliyu ya matso kusa da ita da damuwa yace "Did she know...." Baby ta girgixa masa kai a hankali, sauke idonsa kasa yyi, Hafsat ta bude back seat ta shiga, Bayan few seconds ya kalli baby yace "Don't keep him waiting, ki shiga motar ku wuce, sai da safe" A hankali baby tace "Yayanmu wllh kunyarsa nake, daxu da safe na gama tsigale shi a waya I never knew makirci matarsa ta hada masa" Aliyu ya bude ido yana kallonta, ta marairaice tana kallonsa, yace "Ki basa hakuri idan kin shiga motar" shiru tayi, ya gyada mata kai yace "Yea, do that" a hankali tace "Toh sai da safe yayanmu" daga haka ta xaga ta shiga front seat ganin Hafsat baya ta shiga Aliyu ya bi ta da kallo, Tana shiga motar ta rufe ta kasa kallon Sudais, bayan ya tada mota ba tare da ya kalleta ba yace "Good evening" sai a sannan ta kallesa dai dai nan shi ma ya kalleta, Murmushi tayi cike da jin kunya tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" a hankali tace "Am soo sorry for what I did daxu da safe don Allah kayi hakuri" kallonta yayi da kyau, sai kuma yyi murmushi yace "Wai dama ke kika kirani?" xaro ido tayi ganin ashe ita kadai ke ta haukanta shi bai ma san wa ya kirasa ba, wani murmushin ya kuma yi yana shafa kansa ya ja motar yace "I bet da muna kusa har duka sai kin kai min" sauke kanta kasa tayi bata ce komai ba. Tun da Aliyu ya shiga gidan gabansa ke faduwa, ya kashe wutan parlorn da kyar ya haura sama, ya fi minti daya tsaye kafin ya bude kofar bedroom din da khadijah ke ciki, tana xaune can karshen gado ta hade kanta da gwiwa tana shesshekar kuka, ya kasa karasawa cikin dakin, a hankali ya kai hannunsa kan switch dake jikin bango ya kashe wutan dakin, da sauri ta dago kanta, ya rufe kofar a hankali, cikin rawar murya tace "Barrister ka kunna plss..."