← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 168

Sashe 25

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

kawo maki abinci ba..." Khadijah ta mike ta fita da sauri daga parlorn Hajiya ta bi ta da kallon mamaki don a tunaninta xata shiga kitchen ne, wanke wanken taje ta d'an yi kafin ta fita gate da sauri ta bude flower sai ga wani ledan, tayi murmushi ta dauka ta dawo ciki ta wuce favourite position din da take xama ta bude take away din taga shinkafa ce da miya sai nama kusan yanka biyar ta wara ido cike da jin dadi ta fiddo goron five alive ta ajiye sannan ta fara ci, cikin few minutes ta gama saboda saurin da take ta koshi ba kadan ba don har ta kasa shan drink din gaba daya, ta boye a inda ta saba boyewa sannan taje ta jefar da ledan ta dawo ta ci gaba da wanke wanken tana gyangyadi tsabar koshin da tayi, da kyar ta karasa ta shiga ciki wajen karfe tara tana shiga kuwa isha tayi suna ta kallonta su ji ta ce ina abincinta amma sai ji suka yi tace xata je kwanta daga haka kuma ta tafi tayi kwanciyarta. Haka nan Khadijah ta ci gaba da rayuwa gidan har na kusan wata biyu bbu ranan da ya taba fashin ajiye mata abinci gashi tun haduwar da suka yi a kanti ta bukaci ya dinga ajiye mata abincin basu sake haduwa ba, duk kwana biyu sai ta ajiye masa note din godiya cikin flowers, Bbu abinda ke daure ma Hajiya Maimuna da Hajiya salaha kai irin yanda suka ga Khadijah ke ta kiba tana kyau gashi fa sai ta kai har washegari wani lkcn bata ko bi ta kan abinda suka girka ba, ga uban aikin xa take narka kullum a gidan, ranan dai abun ya ishi Hajiya Maimuna tace "Ni kam yarinyar nan ko dai akwai gun da take xuwa cin abinci ne ba mu sani ba, dubi fa ko bin ta kan abincin gidan nan bata yi ko da an xuba mata sai ta ki ci, gashi lafiya lau sai ma kiba da na ga ta yi kamar" Hajiya Salaha tace "Nima abun na daure min kai kuma kema kinsan bbu inda take xuwa sai gun mai kanti kuma bata dadewa take dawowa gida" Hajiya Maimuna tace "Yanxu dai kawai mu sa ma duk movement dinta ido sosai" Da rana Khadijah na ta xaune parlorn tana jiran su tafi su kwanta taje ta dau abincin ta a flowers, kallon wani Hausa film suke, taga basu da niyyar shiga ciki, ta mike ta dauke few plates dake parlorn duk da tayi wanke wanken safe tace "Mama in je in wanke" Hajiya Salaha tace "Toh sai kin tambaya, ko ba aikin ki bane" fita tayi da sauri don dama abinda take nema kenan, tana ajiye plates din ta fita gate, tuni su Hajiya suka fito suna lekan compound suka ga bbu ita, hakan yasa Hajiya Salaha xata nufi gate Hajiya Maimuna ta rike tace "Jira kamar ga kafafuwanta can a tsaye" ko rufe baki basu yi ba sai gata ta shigo da leda suka yi saurin makalewa da bango, ko lura da su bata yi ba ta wuce inda ta saba xama da sauri, ta bude soyayyen kwai da indomien dake turiri kenan ta ajiye five alive a gefe, sai ga su a kan ta, tsuru tsuru tayi tana kallonsa kamar yanda su ma suka saki baki suna kallon abincin, salati suka saki a tare, Hajiya Maimuna tace "Uban wa ta baki wannan abincin Khadijah" Khadijah da tayi mugun tsorata xata mike ta gudu Hajiya Maimuna ta cafketa tace "Gun ubanwa kika karbo?" Jikinta na rawa tace "Ku yi hakuri" Mari Hajiya Maimuna ta xabga mata tace "Dama shi yasa kika daina bi ta kan girkinmu a gidan nan, karuwanci kika fara ba mu sani ba? To yau sai kin fiddo wanda ke baki abincin nn" cikin kuka tace "Gidansu yana can mama" janta suka yi suka fita ko warce ta yafe dankwalinta a kai ana huci suka ce "Mu je gidan"
Chapter 25 · 0% Book details