Sashe 18
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read
nan" juyawa khadijah tayi ta bar wajen, Hajiya Maimuna tace "Idan ba ma tsoron Allah ba har Alhaji xai yarda ya rike er Muhammad, uwar me ya tsinana sa yana raye" Khadijah dake ta turo baki ta dau omon da ta gani da sosan wanke, tsaye tayi ta rasa ta inda xata fara wanke wanken, can dai ta dauko babban bahon da ta gani ta tari ruwa ya kusa cika sannan ta xaxxage d'an omon, muryar wata mata da shigowarta gidan kenan taji tana cewa "Ke ya haka, da uban ruwan nan xaki kada kumfa?" Khadijah ta kalleta kamar xata yi kuka tace "Toh ban sani ba" matar ta karaso baki sake, nan ta rage ruwan ta kara mata omon sannan tace "Haka ya isa" parlor matar ta shiga wajen su Hajiya tana cewa "Ku kuma ina kuka samo wancan Ajebon" Karfe kusan hudu da rabi Hajiya Salaha ta fito bayan tafiyar bakuwarta, sakin baki tayi tana kallon Khadijah dake durkushe bakin pampo har lkcn, kwanuka ta ko ina, duk ta hade gumi ta jike kayanta jagab, kai kana ganinta kasan bata taba ba ne, Hajiya ta kwalo ma kishiyarta kira ta fito da sauri, ita ma ta xaro ido tace "Me xan gani ni Maimuna, wanke wanken awa biyu?' Khadijah dake kallonsu kamar xata yi kuka tace " plates din sun bushe, ya ki ya fita" Hajiya Maimuna ta rike ha6a tace "Ehh lallai muna da aiki, yanxu tsalelliyar budurwa kamar ki baki iya wanke wanke ba shekara sha uku sa'ar Murjata" Hajiya Salaha da ita ma ta bude baki ta kalli kishiyarta tace "kina da aiki dai, don ba ni aka kawo ma ita ba, mutum yaji da nasa 'ya yan mana, shima Alhaji wllh, da ba sai ya bar ta gun kishiyar marigayiyar uwarta ba" Juyawa Hajiya Maimuna tayi tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka ta shiga ciki, Hajiya salaha ta mata tsawa tace "Tashi mana kan kwanuka yar banxa kawai, ke ga yar masu kudi ko, to xa ki ci kwakwa a gidan nan don bbu shegen da xai dau iskancin ki, kawai kin bi kin ma mutane asarar omo, maxa kuma ki dau tsintsiya ki tattare gaba daya gidan nan idan shima kuma baki iya ba sai in ga" khadijah da ta bata fuska xata yi kuka ta karasa ta dau tsintsiyar da take nuna mata ta fara sharan, takaici ya rufe Hajiya ganin gwara ma ta shekara a tsugunne bakin pampon da wannan sharan da take na yan iska, juyawa tayi ta bar gun daga karshe tana cewa "Xaki san inda kika xo yarinya" da daddare Khadijah na rakube jikin kujera gaba daya hankalinta da soul dinta na kan kallon cartoon da kananun yaran kawu Jibril suka sa a TV, an kirata ya fi sau uku amma inaa, hauri Sajida er Kawu ta biyu ta kai mata tace "Yau naga mayyar kallo ana magana bata ma san ana yi ba" a firgice ta mike sai dai har lkcn idonta na kan TV, Hajiya Maimuna dake lekosu daga kitchen don ita ke kiran khadijar ta xo ta karbi abinci, ta karaso a fusace ta kai mata dundu, firgita ta juyo Hajiya Maimuna ta murda kunnenta tace "Gafara shegen kallon nan xai maki ne hala, ka ji min yar kaza kaza" sunkuyar da kai khadijah tayi kamar xata yi kuka, Hajiya Maimuna ta turata kitchen tace "Ga tuwon ki can a kitchen ki dauka, gayyar tsiya kawai" tafiya kitchen din tayi tana yi tana waiwayo TVn ta dauko tuwon a wata yar roba an ya6a masa miyar kuka koriya shar, sai kallon miyar take kamar idanuwanta xa su fito, ta dawo parlon ta xauna cikin yara dake cin abinci su ma ta ci gaba da kallonta Hajiya Salaha ta shigo parlon tace "Wato kinsan idan mutum ba ayi masa tarbiya ba sai na kallo, kinga saura kadan ta xubar da tuwon tana kallo" da sauri khadijah ta kalli tuwonta taga ba daidai ta ajiye sa ba, Hajiya salaha ta fixgota a fusace ta juyar da ita tana kallon kofar kitchen tace "Duk kika sake juyowa sai na kashe ki" Khadijah dai bata ce komai ba ta kai hannu a hankali cikin tuwon ta mintsili kadan ta kai baki, yamutsa fuska tayi tana hadiyewa da kyar sai kuma ta kalli Er Kawu ta uku mai suna Rabi tace "Anty akwai indomie?" Yarinyar ta fashe da dariya sannan ta gaya ma Uwarta Hajiya Salaha, Hajiyar tace "Ehh akwai wanda ubanta ya kawo mana daga kabari" Khadijah dai bata ce komai ba, haka tayi ta kallon tuwon ta kasa ci, daga karshe haka ta mike ta kai kitchen ganin kowa na kai kwanonsa can, Hajiya Maimuna ta kwalo ma kishiyarta kira ta nuna mata tuwon da ta bari tace "kin dai ga koh? To wllh har in fita girki sai dai yunwa ya kashe yarinyar nan"