Sashe 32
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da suka dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace "Meye wannan din kika dauko?" Da kyar khadijah tace "Firewood, it's too heavy, and it's pricking me all over" a fusace Yakumbo tace "Kin ma uwar ki Amina turanci ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta je ba tunda ba ki da mutunci" korata Yakumbo tayi ta fita ta na share hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki ta daura mata a kai tace "Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji" a hankali khadijah tace "Toh nagode" A haka ta isa gida tayi ta tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta kike ta sauke mata tana cewa "Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki daina ma mutane kamar mara laka a jiki" Khadijah dai bata ce komai ba, bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace "Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan" Yakumbo na huci tace "Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni... Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu" Salamatu tace "Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu...." Katse ta yakumbo tayi tace "Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita" Ladi tace "Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d'an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d'an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh" Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace "Kai amma fa kun kawo shawara, amma...." Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce "Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu" juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace "Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba" dariya Ladi tayi tace "Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita" Yakumbo tayi murmushi tace "Dadina da ku akwai shawara mai ma'ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba...." Ladi tace "Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka" yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace "Dari bibbiyu dai" daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace "Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta...." Ladi tace "Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta... Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba" hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa'a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace "Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako" Bibalo tace "Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya" daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace "Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda" tagumi tayi tace "Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa" Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace "Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa'a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A'a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta" Yakumbo tace "A'a mu je kawai mu gwada sa'ar mu" Bibalo tace "Toh ki sallame ni ni xan wuce" Yakumbo ta hade rai tace "In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki" Bibalo ta bude baki tace "Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki" mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa "Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba" dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace "Ya fi babu ai" daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace "Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?" Yakumbo ta hade rai tace "Idan an dauki yarinya ba" Abu tace "Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?" Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace "Warcen da ta fi minti ashirin tana d'an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba" yakumbo ta marairaice tace "Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari" Abu ta tabe baki tace "Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya" Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa "Toh bamu minti biyar kacal" tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace "Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba" tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace "Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?" Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace "Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai