Sashe 108
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 2 min read
amshi shegu gidan nan ba, kaf xuri'ar mu ba a taba haka ba baxa a fara a kan d'an yayata ba" tana wucewa sama mumy na share hawayenta ta kama hannun yan biyun ta wuce sama xuwa dakinta da su. Wata nurse ce ta shigo dakin ba ma sudais allura ta ga babu kowa dakin sai kofar bayi da ake ta bubbugawa ta isa da sauri ta bude kofar da mamaki ganin key aka sa ta waje, khadijah ta fito tana bin dakin da kallo ganin ba kowa ta riko nurse din a rikice tace "Na shiga uku nurse ina yarana? Where are they plss" nurse na kallonta da confusion tace "Yanxun nan na shigo madam" da gudu khadijah ta fita xuwa ward din da aka kwantar da ita, ta ga Umma ce xaune sai Nanny da khaleel dake tsaye ya jingina da bango idonsa a kan wayar hannunsa, ta fashe da matsanancin kuka ta xube wajen tace "Wayyo Umma na shiga uku ya tafi min da yarana" khaleel ya iso gabanta da sauri da mamaki yace "Ya tafi da su ina? Kina kallonsa ya tafi da su" ficewa yyi ward din da sauri, Umma da ta gigice tace "Wa ye ya tafi da su Khadijah, waye shi" Khadijah ta riko Umma tana kuka sosai tace "Umma Aliyu, ya tafi da yaran, ya wuce min da yarana" a sanyaye Umma ke kallonta, Nanny ta bi bayan khaleel da sauri tana cewa "Me ya kawo sa asibitin, mun shiga uku" umma ta dago Khadbijah ta rungumeta, cikin rawar murya take cewa "Umma kar ku bari ya raba ni da su, baxan iya rabuwa da su ba, don Allah a taimake ni a karbo min yarana ni na yafe masa duniya da lahira ya bar min yaran, wllh na yafe masa har cikin xuciyata amma yayi hakuri ya ba ni yarana" tana kai wa nan ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kiran Umma, hawaye ya shiga sakko ma umma ta rasa abinda xata ce ma 'yar tata.