← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 168

Sashe 116

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa Mumy tayi tana kallon Anty khadijah a mugun tsorace tace "Ciki kuma khadijah? Ciki fa??" Da kyar Anty khadijah ta juyo kai tana kallon Mumy, Aliyu ya juya ya fice daga ward din, mumy ta fashe da kuka tana kallonta tace "Ciki fa Khadijah, innalillahi wa inna ilai hi raji'un, turr da halin ki Khadijah, tsofe tsofe dake khadijah" Mumy ta xauna kan kujera ta dafe kai tana kukan abun kunyan da Anty khadijah ta dauko masu, Aliyu ko minti biyar bai kara a cikin asibitin ba ya bar ma saleem makullin motarsa ya hau motar haya xuwa Kaduna, don gaba daya hankalinsa na sudais, har ya isa gida kuma yana mamakin Anty khadijah, wai ciki... jiki a sanyaye ya wuce sama xuwa bedroom dinsa, har sannan baby na xaune dakin kusa da sudais dake bacci, tana ganinsa ta mike tace "Yayanmu ya jikin Anty khadijahn?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Da sauki" daga haka ya kai hannu goshin sudais ya ji babu xafi kamar daxu da safe, ya kalli baby yace "Bai tashi ba tun daxu?" Ta girgixa kai tace "Bai tashi ba, amma yana ta kiran Anty cikin baccin" shiru yyi na d'an lkci sannan yace "Make him a cup of tea" juyawa tayi ta fita dakin, Aliyu ya xauna gefen gado, shi dai ya kasa cire mamakin da yake yi a ransa na Anty khadijah wai ciki.... Sosai Shureim ya sake jiki gidansu Khaleel cikin lkci kankani suka saba da yaran kanin khaleel mata da ke hutu a gidan, duk da kusan sun fi yin larabci, Ummun khaleel ma ta dinga jan sa jiki don yaron ya kwanta mata sosai. Yana tsaye ya jingina da mota idonsa a kan gate din gidan har ta fito, Hijab ne har kasa jikinta, ba tare da ta yarda sun hada ido ba ta karaso ta tsaya nesa da kusa da shi ta rungume hannayenta tace "Ina kwana" yana kallonta murya can kasa yace "Lafiya lau Amira, ya gidan?" Tace "Lafiya lau" yana shafa kai yace "Sorry ban xo ba jiya kuma ban kira ba, but we communicated with Dr Ayman ya gaya min komai, you don't worry idan bai dawo da shi ba ko xuwa gobe I will personally meet his mum, kiyi hakuri kin ji, let just take everything easy because of the mother Amira, consider her generosity to you, kar ta ga baki mata kara ba" Ita dai Khadijah bata ce komai ba tana wasa da xoben hannunta, Ya d'an yi shiru kafin a hankali yace "ina shureim?" tace "Yana gidansu Dr Ayman" kallonta ya dinga yi yace "Me yake can?" Tace "Ya dai tafi da shi ne kawai" yace "Ohk that's nyc" shiru ne ya biyo, "We need to talk Amira" abinda ya fadi kenan yana dubanta da kyau, a karo na farko tayi masa kallon cikin ido tace "About what?" Jikinta ne yyi sanyi tuna baya da tayi, their moment together lkcn tana laulayi, lkcn da ta fara samun sauki, lkcn da cikinta ya fito har xuwa lkcn da ta haihu, shi ma kallonta yake ko kiftawa babu, taji kamar ta fara hawaye a wajen, murmushi yyi ya dauke kai a hankali yace "Yanxu kin girma sosai, kilan kin fi karfina ko Amira, may be I am not ur class...." Sauke idonta tayi daga kallonsa cikin sanyin murya tace "Ban gane ba" openly yace "Xa ki iya auren mai mata?" Bata kallesa ba bata kuma ce komai ba amma sai da gabanta ya fad, wani murmushin ya kuma yi yace "That says it all, you are not interested" sai a sannan ta daga kai ta kallesa tayi murmushin karfin hali ita ma tace "I know marrying u is not even enough in biyaka abinda ka min a rayuwa barrister, but..." Ya katse ta da sauri yace "But what?" A hankali kuma a sanyaye tace "It looks as if you are afraid of ur wife, ba lallai ta bari ka kara aure ba..." lkci daya mood dinsa ya canxa yace "Says who Amira?" Ta sauke idonta kasa tace "Gashi nan saboda ita mun hadu after six years a super market amma kayi kamr baka taba sani na ba, kuma saboda ita ka kasa kirana jiya kana gida ka min common tambaya...." Ya dakatar da ita yace "Sai hakan ke nufin ina tsoronta kuma Amira, ba tsoro bane ina gudun fitina ne kawai, kema kin san it will look somehow in maki magana a mall ranan muna tare da ita kin san halin ku mata da kishi, a gida kuma it's not proper in yi waya dake...." Khadijah tayi murmushi tace "Upon ur profession? Ta mance wa ta aura ne?" Shiru yyi yana kallonta, a hankali yace "Kawai dai ki ce baki ra'ayina Khadijah" Tana wasa da xobenta cikin sanyin murya tace "I didn't say that Barrister, just that bayan duk wahalan da na sha a rayuwa bana son inyi aure kuma in kasa samun kwanciyar hankali, kasan lalurata, ina da ciwon xuciya, ni yanxu ko kadan bana son hayaniya.... Ban san me yasa ba" tana magana ne hawaye cike idonta, "Ban da haka bani da abinda xan iya biyanka da shi a duniya barrister da ya wuce in amince da auren ka a yanxu, but am afraid..." hawaye na sakko mata ta kai karshe, Lumshe ido yyi na few seconds kafin ya bude ya ga kallonsa take, da sauri ta sunkuyar da kanta yace "Kar ki damu da matata Amira, beside ba gida daya xa ku xauna ba" ita dai bata ce komai ba amma gaba daya hankalinta a lkcn ya tafi kan khaleel..., lkci daya jikinta yyi mugun sanyi, A hankali ta ji yace "Plss Amira..." Ta daga kai a sanyaye tana kallonsa. Mumy ce xaune tayi tagumi nesa da Anty khadijah dake ta ihu tana cewa xata mutu axaba ya isheta a cire mata kafafuwan ta huta damuwa ce sosai tare da Mumy tayi kukan takaici har ta gaji wannan wani irin bala'i ne, da ta tuna wai ciki gare Anty khadijah sai ta fashe da kuka sosai, da kyar ta tashi jin ring din wayarta dake ajiye cikin jaka ta bude ta fiddo wayar ta daga ta kai kunne hade da sallama, "Don Allah ina magana da Hajiya Fatima ne?" Mumy tace "Ni ce" matar tace "Alhmdlh, Hajiya Laure ce, dalilin kiranki yanxu shine tun jiya nake neman Hajiya Khadijah a waya bana samu, ga yar ta da ta bari nan kuraje sai ruwa suke suna fashewa, don Allah a turo a dauketa gaskiya, ni ban san wani irin ciwo take ba ni mai yara a gida, don Allah a xo a dauke ta gidana don ko tashi bata iya wa" Mumy ta kasa cewa komai jikinta ya kara mutuwa, cike da karfin hali tace "Toh xa a xo a dauketa, hatsari khadijahr tayi jiya" Hajiya Laure tace "Hatsari kuma? Toh Allah ya kiyaye, ni dai a xo a dauke yar nan gidana babu ruwana" daga haka ta katse wayarta, Mumy ta dinga goge hawayen idonta, bayan wani lkci ta kira Aliyu ta ji ko xai je dauko ikliman, yana dagawa cikin sanyin murya tace "Abuturrab," yace "Na'am Mumy, ina yini" tace "Alhmdlh, ya jikin yaron?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Muna Asibiti fa Mumy" tace "Asibiti kuma, jikin ya ki ne?" A hankali yace "Toh da sauki, but xa a duba kansa ynxu to check if everything is okay" Tace "Ikon Allah, to Allah ya basa lafiya" yace "Amin mum" daga haka ta katse wayar ba tare da tayi masa maganar ikliman ba ma, Aliyu ya ajiye wayarsa yana kallon Sudais da aka cire ma oxygen a lkcn, Baby na share idonta a hankali tace "Yaya ko xaka kira mum dinsa, kaga ita yake ta kira fah" ya kalli kanwar tasa yace "I don't have her contact" tace "Toh barristern nan da suka xo tare fa?" Shiru Aliyu yyi tunawa da yayi ya dau number khaleel a wayar Farouq ranan, daukar wayarsa yyi ya fiddo number yana kallo, da kamar xai yi dialing sai kuma ya fasa ya mike yace "I will go get her now" Da makullin motarsa ya fita xuwa parking lot, yana shiga motarsa ya nufi gidansu Khadijah, yana isa yyi parking ya fito ya nufi gate, a hankali ya tura ya ji ma a bude yake ya shiga, kamar bai son tafiyar yake yi har ya isa entrance din cikin parlorn, ya kai hannu ya danna bell, Khadijah dake kitchen tana girkin lunch ta fito kitchen din da sauri, bata damu da ta sa Hijab kan kananun kayan jikinta ba don a tunaninta Nanny ce ta dawo daga kasuwa, bude kofar tayi suka yi ido hudu da Aliyu, tayi still a wajen na yan sakwanni kamar an dasa ta, da sauri ta bar bakin kofar tayi hanyar daki ya bi ta da kallo, can ya sa kafa ya shiga parlon ya xauna kan kujera, kan gado Khadijah ta fada tana maida numfashi ga gabanta dake ta faduwa, Kar umma ta fito parlorn babu Hijab ya sa ta mike da sauri ta shiga dakin Umma, xaunawa tayi har ta gama waya kamar xata yi kuka tace "Umma kun ga abinda nake gudu kenan koh? Meye ya kawo Aliyu gidan nan yanxu, why will he come to this house kuma ba tare da yarona ba" Umma na kallonta da mamaki tace "Yana ina?" Fuska daure tace "Yana parlor mana" Umma tayi shiru, sai kuma tace "Toh ai sai ki tsaya ki ji me ya kawo sa koh" Khadijah ta kara hade rai sosai tace "Umma ni idan xan koma UK da yan biyun xan tafi gaba..." Shiru tayi a sanyaye tunawa da tayi ai a can ma ta fara jam da Aliyu, Umma tace "Ki tashi kije ki ji abinda ke tafe da shi, ni kar ki min fitsara" rai ba dadi Khadijah ta mike ta fita, labewa tayi da bango a corridor tana kallonsa, the mouth, the nose, the eyes, worst of all the face... Sosai jikinta yyi mugun sanyi, wayarsa kawai yake dannawa idonsa a kai, kamar ance ya waiga suka hada ido gabanta yayi mugun faduwa, tayi saurin dauke kai, shi ma hakan yayi, ta hade rai bbu yabo babu fallasa tace "Me ka
Chapter 116 · 0% Book details