Sashe 38
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 5 min read
gun da take a tsaye, ya shiga kitchen din ya hada abinda xai hada a cup ya fito har ya wuce ya juyo ya daure fuska yace "Baki iya gaisuwa ba koh?" Ta turo baki tace "Good morning" daga haka ta juya ta wuce gun kyauta a waje, ya kusa second ashirin a tsaye kafin ya juya ya wuce sama. Ruwan wanka kyauta ta hada mata bayan sun koma daki, khadijah tace "Anty mai girki ni fa ban yi brush ba kika bani abinci" kyauta tace "Ni na hanaki brush?" Khadijah ta langwabar da kanta tace "Toh su fauxiyya sunyi lost din min brush dina a gidansu" kyauta tace "Oho dai tafi kinyi wanka ga ruwa can" khadijah na fitowa daga wanka kyauta ta bata Vaseline ta shafa sannan ta fiddo mata da daya daga kayan ta da ta linke bayan ta kwaso mata su jiya, khadijah tace "Anty mai girki kinsan wa ya siyo min new pants din nan" kyauta tace "Oho" khadijah tace "My lovely Umma" kyauta bata sake kula ta ba ta fixgota ta lafta mata uban kwalli a ido ta shafa mata farin powder a fuska sannan tace "Wuce can baya ki xauna kar ki shigo gidan nan sai na kira ki na gaji da surutun ki" khadijah tace "Toh" sannan ta fita, dakalin da ta saba xama ta xauna bayan ta tsinka flowers da yawa ta dinga yin jakar hannu da su kamar yanda aka koya masu a schl da dadewa, kamar ance ta daga kai suka hada ido da Aliyu dake kallonta, ta dauke idonta ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ta daga kai bata sake ganinsa xaune balcony din ba, gajiya da xama tayi ta shiga ciki ta bude kofar kyauta a hankali ta ganta kwance tana bacci, shiga tayi ita ma ta kwanta gefenta nan da nan bacci ya dauketa. Da yamma Mumy na xaune parlor da Anty khadijah da ita ma dawowarta gidan kenan tun daxu da ta fita, khadijah ta fito daga daki bayan ta ajiye kayan kyauta da ta bata, mumy ta kirata ta karasa parlorn ta durkusa tace "Anty gani" mumy tace "Meye da meye bbu a kayan ki?" Khadijah tayi shiru tana naxari, can ta fara lissafo su da fingers dinta tace "I don't have toothbrush and toothpaste, I don't have towel, I only have six pants da ummata ta siya min sauran fauxiyya ta sace min, even ves bani da shi, kuma bani da mai da xan shafa, Anty har da na gashina" murmushi kawai Mumy take, Anty khadijah kuwa ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Aliyu dake dinning yana cin abinci tabe baki kawai yyi, mumy tace "Toh in ga kan naki" khadijah ta xame hular kanta Anty khadijah ta saci kallon dogon gashin, mumy tace "Kai maa sha Allah ran Saturday sai ki bi su Siyama kema a gyara maki koh" da sauri khadijah ta xauna a tsorace tace "Anty ummata ta gyara min ai, it's just of recent ta kai ni saloon" Mumy tace "Anjima driver xai kawo maki duk abinda baki da, kina da takalmi koh?" Ta gyada kai tace "Amma ya kusa tsinkewa su fauxiyya suke sa min" mumy tace "Toh tashi kije xa a siya maki" khadijah tayi murmushi tace "Toh Anty I like you" daga haka ta wuce kitchen gun kyauta da sauri. Mumy na kallon Anty khadijah da har lkcn ranta a bace yake tace "Khadijah am thinking ko in sa yarinyar nan a islamiyya su dinga xuwa tare da su baby da yamma, kowa ya ganta yasan she is from a wealthy home, it's just condition...." Katse ta Anty khadijah tayi tace "Anty fatima ki raba kanki, Anty Fatima ki raba kanki ki kyale mutum yanda kika gansa na sha gaya maki times without number, su wa enda suka kawo ta gun aikin sun fa pi ki sanin akwai islamiyya, me yasa kike son sa ma kanki matsala ne wai, tsinannun masu aikin nan da kiris suke jira su tura wanda ya kyautata masu cikin rana, meye hadin ki da yarinyar idan ba shisshigi ba da neman wajen xama??" Mumy ta kalli Aliyu dake ta kallonsu tace "Abuturrab yanxu don nace ayi enrolling din baiwar Allahn nan a islamiyya laifine don Allah?" Ya mike yace "Noo, ba laifi bane mum, sai ma lada da xa ki samu in sha Allah" daga haka yayi wucewarsa sama, Anty khadijah ta bi sa da wani mugun kallo, mumy tace "Atoh, baka san yanda Allah xai yi da naka ba gobe, baka kuma san ina reward din ka yake ba, yarinyar nan tare da ke take gaya mana ita marainiya ce, to don me baxa a ji tausayinta ba, kika san kudin iyayenta a da, don duk wanda yaga yarinyar nan yasan ba daga karamin gida ta fito ba, just put little baby in her shoes... Kin dai ga sa'anni ne su din daga ganin, to da baby ce ta shiga irin halin nan yaya xa ki ji, Allah ya rufa min asiri don dai kudin islamiyya xan iya biya mata, toh ni ban san meye damuwarki ba khadijah" Tsaki Anty khadijah tayi ta mike ta nufi stairs tana cewa "Muna nan da ke sai kin yi da kin sani Anty, shi kuma Aliyu ya ci gaba da daure ma karya kugu, daga ganin yarinya shegiya ku hakikance ku ce a sa ta a Islamiyya for what reason, shi aka aikota yi gidan nan" Mumy tace "Aniyar ki ta bi ki khadijah, shi yasa kike samun matsala da kowa a rayuwa ni dai baki yo halin mahaifanmu ba Allah ya ji kansu, nima ba halin mu daya ba, tirr"