Sashe 112
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har suka isa gidansu Aliyu babu wanda yace komai cikinsu, khadijah tayi nisa tunanin da take bata ma san sun iso ba, Sudais ya fito daga motar ya xaga side dinta ya bude mata ganin bata fito ba, sai a sannan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, tayi saurin sauke kanta ta fito daga motar ya rufe, kallon motar khaleel sudais yyi, dai dai sannan shi ma ya fito daga motarsa, Sudais ya karasa gun sa yace "I pray we meet him at home" Khaleel ya daga kafada yace "Allah ya sa" Sudais ya kalli Khadijah dake tsaye jikin motarsa sai kallon gidan take a sanyaye, gate din gidan ya nufa khaleel ya bi bayansa, bai tsaya sauraran mai gadi Usman dake tambayar sa daga ina ba ya kutsa kai ya shiga gate din ya juya yana kallonsa yace "Six years isn't that far, bai ci ka mance ni da wuri haka ba malam" khaleel ma ya shiga gidan yana kallon mai gadin murmushi dauke fuskarsa ganin yanda yyi kasake yana bin Sudais da kallo, A sanyaye Khadijah ta gaida Usman da ya xaro ido yana kallonta da mamaki yace "wannan kamar Khadijah??" Murmushi ta kirkira ta shiga cikin gidan ta bi bayan su sudais da suka nufi entrance din shiga gidan, haka kawai gabanta ya dinga faduwa tayi slowing pace dinta, Sudais ya danna bell ya ja gefe ya tsaya, bayan wani lkci aka bude kofar, Baby ce tsaye bakin kofar ta dinga kallonsa na wasu seconds kafin ta gaishesa, yana kallonta ya amsa da murmushi yace "Can we come in?" Barin bakin kofar tayi ta rasa abinda xata ce masa, ya kula she is lost don haka ya shiga parlon khaleel ya bi bayansa, tuni khadijah ta labe jikin bango jin baby ce ta bude kofar, hawaye suka shiga sakko mata ta kasa shiga parlorn, Anty khadijah dake xaune parlorn ta dinga kallon Sudais kamar me son tuno inda ta san sa, sarai ya dau fuskarta ya gane ta, a hankali yace "Hello?" Ta mike tana yamutsa fuska tace "Daga ina? Wa ku ma kuke nema?" Yana kallonta yace "Bak'i ne.... Amma nayi mamakin da baki gane ni ba Hajiya" Ta hade rai tace "Do I have any business with you da xan gane ka, malam nan gidan masu aure ne, ka fadi wa ka ke nema, ba haka nan ake shiga gidan mutane ba, from all indications ma batar hanya ku ka yi " Ya taka har gabanta ya tsaya yana mata kallon cikin ido ya fiddo ID card dinsa yace "Barrister Aliyu.... May be this will make you remember me fast" mikewa tayi da sauri tana masa wani kallo, sai kuma ta shiga kalle kalle don ta tabbatar babu kowa parlorn, ta hadiye abu da kyar tace "Wa kake nema malam, me ka sake dawowa yi gidan nan?" Jin bai ce mata komai ba sai murmushin da yake ta juya da sauri ta kalli khaleel da ya nemi kujera ya xauna yyi relaxing a kai, Murya suka ji a stairs duk suka juya, Mumy ta sakko tana kallonsu da mamaki tace "Sannun ku da xuwa" Sudais ya amsa ta karaso parlorn tace "Are you looking for Someone?" Sudais yace "Sure" juyawa yyi ya kalli bakin kofa ya ga khadijah bata shigo ba, ya juya ya koma bakin kofar, yana fita yace "Come in khadijah" Khadijah ta girgixa masa kai cikin rawar murya tace "Baxan iya ba, kuma kila ba nan ya kawo su ba" sudais yace "Trust me, kawai ki biyo ni" daga haka ya shiga parlorn ta bi sa a d'an tsorace don jin muryar Anty khadijah ya kara daga mata hankali, baby ce ta fara xaro ido ganinta lkci daya ta nufe ta da gudu tace "Imann" kasa amsa mata Khadijah tayi, Baby ta rungumeta, hakan yasa khadijah ta fashe da kuka kamar yanda baby ma ta fara kuka, tuni Anty khadijah ta rikice bakin ta na rawa tace "Me ya kawo yarinyar nan gidan nan, me ta xo yi...." Ba tare da Sudais ya kalleta ba yace "Ta xo amsan yaranta" Anty khadijah ta yo waje da ido tace "Tayi aure cikin gidan nan ne da ta xo amsan yara??" Khadijah da ke hawaye a sanyaye ta daga kai ta kalli inda mumy take ta ga kallonta take ko fiftawa babu, sunkuyar da kai tayi kamar me counting steps dinta ta isa gaban mumy hawaye na sakko mata, Mumy da idanuwanta suka kawo ruwa ta rungumeta murya can kasa tace "Khadijah.." duk wannan abun Aliyu na sama tsaye yana kallonsu, cikin rawar murya Khadijah tace "Mumy ki ce ya bani yarana na yafe masa wllh.... Intervene plss mumy" Mumy ta kasa cewa komai sai kuka, Anty khadijah sai wuri wuri ta ke da ido a parlorn ta kasa cewa komai, A hankali Aliyu ya dinga sakkowa stairs din har ya iso parlorn, Khadijah ta dinga kallonsa tana jin tsanar sa, Sudais ya taka har gabansa yana kallonsa da kyau yace "Aliyu?" Aliyu yace "Sure, any problem?" Sudais ya gyada kai yace "Fito mata da boys dinta" Aliyu ya rungume hannunsa yana kallonsa with interest yace "Bodyguards din nata har biyu ne kenan" Khaleel yyi calm smile pretending Aliyu doesn't even exist in the parlorn balle har ya ji abinda yace, shi dai yana xauna kan kujera har sannan, Sudais da idanuwansa suka sauya launi yace "You are stupid... I mean very stupid" Murmushi Aliyu yyi yace "Ku dai da ku ke biyota ne xa a kira da haka, look... ba ku da right din da xa ku dinga interfering a case dina da ita, it's almost a family issue so stay out of it....." Khadijah bata san lkcn da ta isa gabansa ba idanuwanta suka kankance don bala'i tace "Wannan da kake gani ya fi Ka right, when I say right ina nufin right, wllh ya fi ka 100% right over those children, he is almost their father, and will always remain their father, na tsane ka Aliyu, na tsane ka.... I hate you" Tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai, Mumy ta rasa abinda xata ce ban da kuka bbu abinda take, Aliyu yace "Dama ban ce kar ki tsane ni ba Khadijah, you have all right to do so, but Iman am sorry baxan ba ki yaran nan ba, you've past through a lot, ki bar ni da su yanxu let me also play my role, ki tafi ki je ki ci gaba da rayuwar ki da bodyguards din ki, thank God you said he is almost their father not their father, ni kuma I am their biological father..." Tapping dinsa Sudais yyi xuciyarsa na tafarfasa, strictly yace "Malam kasan wanene ni kuwa? Did you knw why I am taking it gently with you, baka sani ba sure.. Then knw this, it's because of ur mother, na ga alamar she deserves some respect, don haka cikin salama ka fito da yaranta yanxu ka bata idan ba haka ba...." Aliyu ya tabe baki yana d'an murmushi yace "You do ur worst....Barrister" Bude baki Sudais yyi yana kallonsa, Khadijah ta durkushe wajen ta kara rushewa da kukan takaici, mikewa khaleel yyi yana ma Aliyu wani kallo yace "Amma kai jahili ne na ga alama, islamically baka da right over yaran nan, kai har yaran da ka samu ta hanyar zina kake alfahari da kake bragging baxa ka bada ba?? Is this how senseless you are" Yar dariya Aliyu yyi yace "U watch ur tongue gidanmu ka xo ka same ni, so you have no place to tell me nonsense, baxan bada yara ba nace" Sudais ya sake tapping dinsa yace "Good, ka saurare sammaci gobe, nasan dai baxa kayi denying kayi raping din yar mutane a court ba koh, sannan kuma don rashin kunya ka dawo kana claiming yaran da baka san da su ba, baka san da yanda aka yi Allah ya raba ta da su ba... You are wicked Aliyu" Aliyu yace "Ka kai ni gaba da kotu.... If there is any" Daga haka ya juya ya haura sama ya bar su wajen, Juyawa Sudais yyi yana wani murmushi yace "Alryt xa mu hadu a can din" daga haka ya nufi kofa yana kallon khaleel yace "Can we?" Mumy ta dakatar da shi da sauri, ya juyo yana kallonta, karasowa gabansa tayi tana goge hawayen idonta tace "I am really short of words, sai dai baxa ayi haka ba my son don Allah ku yi hakuri, xancen baxai kai kotu ba in sha Allah, sure islamically ba shi da right a kan yaran, ina mai tabbatar maku xai bata yaranta in sha Allah, and plss idan baxan bata maku lokaci ba ku bani just few out of ur time ina son mu yi magana da ku" Sudais bai ce komai ba, sai dai shi kansa yasan tun shigowarsa parlorn ya ga darajar matar shi yasa ma bai ma Aliyu haukan da yayi niyya ba, kuma albarkacin irin rikon da tayi ma khadijah truly she deserve some respect, sauke kansa yyi kawai ya koma ya xauna yace "To ina ji Ma" Mumy ta xauna ita ma tana ci gaba da share idonta ta bi parlon da kallo taga babu Anty khadijah, Baby ce kadai jingine da bango tana hawaye, a sanyaye Mumy ta fara cewa "Amma ya ku ke da Iman?" Khaleel ya kalli Sudais da ya kallo sa shi ma, ya ci gaba da operating wayarsa, Sudais ya d'an shafa beard dinsa yace "Yan uwanta ne mu" Mumy ta gyada kai, ta fara magana cikin sanyi tace "It's not as if ina supporting Aliyu don d'a na ne, plss dont quote me wrong, amma ina son ku sani it's a mistake he made kuma ba da gangan haka ya faru ba, tsautsayi ne ya gifta tsakaninsu, ni na haifesa na kuma san halinsa, ita kanta Iman xata shaide sa.... It's not ordinary hakan ya faru da shi" Sudais yace "But kinsan bayan ya sa ta tafi da aka gano tana da ciki na maido ta nan gidan?" Kallonsa mumy take da d'an mamaki, can tace "Gidan nan?" Yace "Sure?" Jikinta yyi mugun sanyi tace "Wa ku ka samu gidan?" Sudais yace "Matar da muka fara samu a parlor