Sashe 68
Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bude motar Sudais yyi ya fita yana kallonta yace "Come down" a hankali ta fito gabanta na faduwa, ya nufi gate din gidan ta bi bayansa kamar me tausayin kasa, da farko Usman mai gadi ya tsaya tambayarsa wanda yake nema amma ganin khadijah ya fito da sauri yana kallonta da mamaki yace "Khadijah?" Ta kirkiri murmushi ta gaishesa, tuni Sudais ya shiga gidan, Khadijah ta bi bayansa Usman yace "Duk kika daga ma kowa hankali ana ta neman ki har station Hajiya ta kai report, to Alhmdllh tunda Allah ya bayyana ki, Alhmdllh" ita dai Khadijah bata ce komai ba ta kalli parking space xuciyarta na bugawa ta ga ba motar Aliyu da na Mumy, Sudais ya danna bell din entrance na gidan a hankali, sau uku yana danna bell din kafin a bude kofar, Anty khadijah ce tsaye bakin kofar kana ganinta kasan bacci take, idanuwanta suka bude sosai ganin khadijah dake gefen Sudais a tsaye tsoro dauke fuskarta, Sudais da yana ganin ta yyi guessing ita ce Anty khadijah ganin kallon da take ma khadijah yace "Assalamu alaikum" hade rai Anty khadijah tayi tace "Wa'alaikumus salam" daga haka ta kalli khadijah tace "Lafiya? Daga ina? Wa ku ke nema?" Sudais yace "Aliyu muke nema" daga haka ya shiga parlorn, Khadijah ta kasa shiga saboda tsoro, Wani kallo Sudais yyi mata yace "Come in" a hankali ta daga kafa ta bi gefen Anty khadijah ta shiga cikin parlorn ita ma, tuni Sudais ya isa kan kujera ya xauna, Anty khadijah dake kallonsa da mamaki tace "Malam nan din fa gidan matan aure ne ka shigo, lafiya? wa kake nema?" Yace "Shi yasa nayi sallama kuma kika amsa min kafin in shigo hajiya" Anty khadijah tace "Me kuma ya hada ku da Aliyu ku ke neman sa?" Sudais yace "Xai fi kyau idan ma bai nan ki yi hakuri ki kira mana shi ya dawo, and mahaifiyarsa hope tana nan?" Anty khadijah tayi mitsi mitsi da ido cike da masifa tace "Nima uwarsa ce ae halak malak, sannan Aliyu bai ma kasar gaba daya idan xaka fadi abinda ke tafe da kai malam ka fada don bacci nake ka taso ni..." Shiru Sudais yyi na d'an lkci kafin ya nuna mata khadijah yace "Kin san wannan yarinyar koh?" Ta kalli khadijah ta kara tsuke fuska tamau tace "Kwarai kuwa, yar aikin da muka dauka kwanaki kenan ta lalata mana xumunci ta shisshige ma d'a na, ta raba ni da shi ina ji ina ganin bana iya cewa komai, wannan shari'ar kuma sai a lahira don duk da barin ta gidan har yau abubuwan da ta cakuda bai gyaru ba, Allah ya isa tsakaninmu da ita" Kuka Khadijah ta fara yi a hankali ta durkusa inda take tsaye, Sudais ya ciro handkerchief dinsa ya share fuskarsa yana kallon khadijah yace "Dena wannan kukan xa kiyi ki bude baki da kanki kiyi mata bayani yanxu" Anty khadijah ta dawo tsakiyar parlorn da sauri tana xaro ido tace "Bayanin me?" Khadijah ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata, kare mata kallo Anty khadijah ta shiga yi, can ta fashe da dariya irin na mugunta lkci daya kuma ta tsayar da dariyar tana ma Sudais wani matsiyacin kallo tace "Xuwa kayi da ita tace mana tana dauke da ciki?" Sudais yace "Alhmdllh fine, unfortunately kin ma san halin d'an naki kenan" Khadijah ta hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Anty khadijah ta fashe da wani shegen dariya kamar bokanniya tayi mai isarta tayi shiru sannan ta nuna masa kofa fuskarta kamar bata taba dariya ba idonta yyi mitsi mitsi tace "Tun muna mu uku a nan bamu fi haka ba ku tashi ku fice mana a gida" a tsawace ta kare maganar, sudais ya tabe baki yace "Tsawar ki ko ihun ki fa baxae razana ni ba malama... Don haka hold it xai maki amfani gaba a wani wajen" Anty khadijah na huci tace "Xan nuna maka a nan ma yana da amfani, har wannan karuwar xata xo ta makala ma d'ana cikin shegen da tayi a wani wajen saboda ita matsiyaciya ce" Sudais yace "Toh abu mai sauki sai mu je asibiti a ga kwanakin cikin nawa, idan yyi dai dai da kwankin da ya koreta ta bar gidan to nasa ne in sha Allah" Anty khadijah tayi shiru jin abinda sudais yace, auuuu wato Aliyun ne ma ya koreta ashe, ita dai ta dawo kauyen da taje bayan kwana biyu da tafiyarta taji wai ba a ga khadijah ba ko sama ko kasa har station an kai report, Ranta yyi mugun baci a lkcn don bata so Khadijah ta tafi haka nan bata walakanta ta ba kmr yanda ta yi alkawari, me yasa xata tafi bata gama cika burin ta a kan ta ba har hawaye sai da tayi sbda bakin cikin kudin mota da kudin magani da tayi asara, suree a lkcn tayi mugun mamakin yanda Aliyu bai wani damu can ba kamar yanda mahaifiyarsa da baby suka damu amma ita bata taba kawo cewar shi ne ma ya koreta ba, Muryar Sudais ya dawo da Anty khadijah "Hajiya kin yi shiru daga nayi xancen asibiti" abinda ya fada kenan yana kallonta, ta yi masa wani shegen kallo tace "Ji gantalalle, to tunanin da nake daban malam, kuma asibitin ya ci kaza kazan sa baxa a je ba, idan ma cikin Aliyu take dauke da, idan ma ba nasa ba... bbu wanda ya isa ya shigo mana da shege cikin xuri'ar mu, I can swear with the Qur'an fasikanci ba halin Aliyu bane idan ma yyi Ita ta koya masa don kullum dakin sa take yini, wa ya sani ma ko har kwana tana yi can, yayata ba mai xama bace don yanxu xancen da nake ma bata kasar, kullum nice ke tare da su, wai hanata shige ma Aliyu da nake har shi ya janyo min bakin jini gun ta, ta janyo d'a na ya daina ganina da gashi a gidan, yanxu tun muna magana irin ta mutane ba mu dawo na mahaukata ba ku tashi ku fice min a gida kar ku ga d other side of me, ku fita nace" a tsawace ta kare maganar, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Toh cikin nasa dake jikinta tayi ya da shi kenan?" a takaice Anty khadijah tace "Ta xubar, don kaf xuri'ar mu ba shege kuma baxa a fara a kan d'a na ba, idan kuma taga xata iya sai ta raini cikin ta haifa ma kanta ajalinta...." Khadijah dai banda kuka babu abinda take, Sudais ya mike yace "Good, I made her brought me here for just 2 reasons, na farko... is to find out how sincere she is, and na karshe... Is just to let you and ur son knw d pains u are about putting the innocent orphan coz ni dai nasan definitely baxa ku taba accepting cikin ba, kun rabata da warce take da ita a duniya, kun goga mata bakin fenti da ba lallai ya gogu ba har karshen rayuwarta, amma Hajiya ina son ku sani, kamar yanda marainiyar nan tayi bankwana da farin ciki to wallahil azeem kuma hakan ne xai same ku a a xuri'ar ku barin shi Aliyun, He will know no peace da hakkin marainiya a kansa, who knows tunda tace likita ne shi signs na pregnancy din ya gani ya koreta, in sha Allahu sai kun yi da kun sanin abinda ku ka aikata ma yarinyar nan" yana kai wa nan ya karasa gabanta ya ciro ID card a gaban rigarsa ya nuna mata yace "Barrister Aliyu Umar, or just sudais.. we might meet some other time in sha Allah.... Or probably not" ya fadi hakan yana gesturing da hannunsa, khadijah da gabanta yayi mugun faduwa ta dago da sauri tana kallonsa wasu hawayen masu xafi na xubo mata, wani dariya Anty khadijah tayi tana tafe hannu tace "Are you threatening us?" Ya girgixa kai yana murmushi yace "Noo, not at all, kilan idan kika gaya masa aika aikan da yyi xai iya biyota, here is my complimentary card..." Ya ajiye card din gefen kujera, dauka tayi ta yayyage ta xubar nan kasa a gabansa tana huci tana kallonsa, yayi murmushi ya kalli khadijah yace "Tashi mu je" khadijah ta mike a hankali ta bi bayan sudais da har ya isa kofa, tana goge hawayen ta har ta iso gun motarsa, shi ya bude mata motar ta shiga ya rufe ya xaga ya shiga maxaunin driver, har suka hau titi bai ce komai ba ta hade kai da gwiwa tana rera kuka ko xata ji saukin tukukin da xuciyarta ke mata, A bakin hanya sudais yyi parking ganin masallaci ya fita don yin sllh da bottle water ya dawo motar, bayan ya sha ruwan ya ci gaba da driving dinsa, ya hade rai yace "Will you stop those tears and start thinking of how to face reality" ba shiri tayi shiru tana shessheka ya ci gaba da tukin sa. Dab da isha suka shigo kano, direct ya nufi hotel bayan yyi parking yace "Gobe da safe xa mu je gidan Step mum dinki" a tsorace take kallonsa, ya bude motar ya fita yace "Ki fito" daga haka ya wuce reception, daki biyu ya amsar masu, ya siya masu abinci a nan reception din sannan suka wuce sama, yana tsaye daga bakin kofar dakin da ya bude mata ta shiga na hotel din yace "Make sure you try and pray, ki daure ki ci abinci kiyi wanka sannan ki kwanta" spare ki ya cire yace "Don't leave the key jikin kofar" daga haka ya juya ya shiga nasa dakin, wanka kawai yyi, yyi sallah abincin ma bai iya ya ci da yawa ba ya kira mami, bayan sun gaisa ta tambayesa ya hanya, yace "Alhmdllh mami gobe xan dawo in sha Allah" tace "Toh maa sha Allah, in ji anyi nasara" yace "In sha Allah mami" tace "Toh Alhmdllh" a hankali yace "Am very tired mami xan kwanta" tace "Toh Allah huta gajiya" yace "Ameen" daga haka ya kwanta nan da nan bacci me nauyi ya daukesa, bai farka ba sai karfe uku, mikewa yyi xaune da sauri ya dau shirt dinsa ya sa