← Book details Noor Al Hayat Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 168

Sashe 62

Noor Al Hayat Complete Hausa Novel · about 4 min read

tace "Sai ki sha yanxu, an riga an sallame ki, yace yan uwanki na hanya koh?" Ta gyada mata kai tace "Toh Allah ya kawo su lfya" daga haka ta fita, ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata kuna, sai a snn envelope din kudin dake hannunta da ta fadi ya fado mata, bata wani damu ba don tasan me rabo ya dauke shikenan kuma, bayan wani minti ashirin din nurse din ta shigo tana mata wani kallo tace "Wai har ynxu ba su iso ba yan uwan naki?" Tana kallonta a sanyaye ta gyada mata kai kawai, nurse din ta tabe baki ta juya ta fita, taa ta xaune ta rasa me ke mata dadi har lkcn kanta na bisa gwiwanta nurse din ta shigo da likitan daxu, likitan yace "Ke daga wani garin yan uwanki xa su xo ne har yanxu basu iso ba, ko karya kawai kike ma mutane?" Hawaye cike idonta cikin rawar murya tace "Ehh" ya xare glass din idonsa yana xaro idon yace "Karyan kike?" Ta fashe da kuka a hankali tace "Ni bani da yan uwa, ban san kowa ba, ban san ina xan je ba" a mugun fusace yace "You must be joking, Look malama fita ki bar ma mutane asibitin su, get out yanxun nan, maxa dau sauran abincin ki ki fita kar in kira masu gadi su yi waje da ke" jikinta na rawa ta sakko ta dau abincin da yace tana jin kamar jiri xai kada ta hawaye na sakko mata sosai ta nufi kofa, nurse din ta bi ta da kallo, murya can kasa tace "Dr ko xaka kira shi wanda ya kawo ta tun da kasan shi?" ya jefa mata wani kallo yace "Toh me xai yi mata idan na kira sa, sanin wacece ita yayi aka gaya maki? He just helped her tayi collapsing a gefen titi daga anyi hatsari" khadijah ta bude kofa xata fita likitan yace "Tsaya malama" tsayawa tayi ta juyo tana kallonsa a tsorace, ya ciro wayar sa a lab coat din jikinsa yyi danne dannensa kafin ya sa hands free wayar ya fara ring, sae da ya kusa katsewa aka daga, likitan ya ce "Sudais, ga patient din da ka kawo mana taki tafiya fa...." daga daya bangaren aka ce "I don't get you" a d'an fusace likitan yace "I also didn't get what she meant by saying she don't have relatives and she don't knw where she's heading, don Allah ka xo ka fidda min ita a asibiti plss" Wanda ya kira da Sudais cikin expression din mamaki yace "Ji min walakanci fa, toh ni da ka kira ni me xan yi? If I am not mistaken I told you I don't knw her Yusuf, then why calling me? Me yasa kake kirana? Wait wllh sai ka gaya min me yasa ka kirani ma dai, are you not just suppose to tell her to leave kayi discharge dinta???" Likitan ya kalle Khadijah a fusace yace "Ke malama maxa nemi Inda dare yyi maki kada in sa a xo a fitar da ke yanxun nn, get out plss" kai ta gyada masa jikinta na rawa hawaye na sakko mata, Da sauri Sudais din yace "Wait Yusuf, you knw what? kaga dare yyi ynxu ka bari gobe da sassafe kace ta wuce plss since she's lying she don't have relative" likitan yace "Sai dai idan xata sake biyan kudin gado, don da ace haka ake yi a clinic din da ba mu samu ci gaba ba" Shiru Sudais ya d'an yi kafin yace "Toh naji xan biya ka, though I hate lies and liars let her just be safe there kafin ta wuce gobe, just dat 1st thing tomorrow morning send her away, good nyt" daga haka ya watse wayar, ko kallonta likitan bai yi ba yace "Bani hanya" ta bar bakin kofar da sauri yyi ficewarsa kamar xai tashi sama, Nurse din ta karaso kusa da ita tace "Me yasa kika yi karya yan mata, ke ba musulma bace?" Khadijah ta girgixa mata kai hawaye mai xafi na xubo mata, nurse din ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh tafi ki kwanta" daga haka ta fita ta bar ta tsaye, karasawa tayi kan gadon ta kwanta tana share hawayenta, wajajen karfe sha biyu ta tashi xaune jin yunwa na nemanmatat illa ta bude abincin daxu, amai ne ya taho mata bayan ta kai baki ta sauka kan gadon da sauri ta shiga bayi ta dinga amai kamar xata amaye hanjinta, jikinta a mace ta fito ta kwanta bisa gado tana sauke ajiyar xuciya ta kudundune waje daya daga haka bacci ya dauketa sanyi na shiga jikinta.
Chapter 62 · 0% Book details