← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 91

Sashe 89

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ai ko ke abinda yasa kikaga ina kai matsalarki gurin Malamina saboda nasan ba layinki bane dole tasa kike le
awa kuma ba zakimun yankan baya ba.

Ki kuskura ki kaiwa Halima matsalarki zaki gane baki da wayo wlh ke baki san da yawa neman hanyar ganin bayan mu akeyi bako?

To idanbata kaiki inda za'ayi miki magani ba ta kaiki inda za'a
ara dagula miki lissafi ai.

Maganar Hafsatun ce ko yaya?

Ba jiya kince mun yau yaron zezo ba?

Be zo bane ko yaya?

Amma abin da kamar wuya ace be zo ba dan kiranyen da Malam ya masa idan kinga be zo ba to a kabari yake dan wlh aikin da aka masa irinsa akeyiwa Ri
un masu laifo kiji ance sun gudu daga Magar
ama to Aljanu ake turawa su
auko su, yauwa ya wancan zancen ku
in komai ya tafi daidai ko?

Dan ko
azu seda Malam ya mun tunin kasonsa nace masa ban dawo ba bamu zauna naji yanda ake ciki ba tukunna".

"Uhm kedai Turai Allah ya kaimu jibin ku dawo ma zanta, maganganun da yawa ni na rasa ma abinda zanyi wlh" Bintan ta fa
a kamar abar tausayi, Tirai ta she
e da dariya tace
"Ai Binta lamuranki kamar me bakin uwa, kiga abu rumi rumi an
ullashi se yayi kamar yaci komai ya watse gaskiya ki tashi tsaye magauta sunga gadon barcinki lokacin daya kamata ki huta yazo, Yayanki sun kawo
arfi amma kuma kwanciyar hankali ta
i samuwa?

Allah ya kaimu jibin to mu dawo zuwa gata seki shigo muji yanda ake ciki" daga nan sukayi sallama ta rafka tagumi tana tunani.

Masifar gidan da kullum gaba takeyi ba baya ba ta sakata fara abinda bata da ra'ayi akai kwata kwata wato Bin Malamai, tun Kissar tana ci a sannu ta dena tasiri saboda an kai ga
ar da wata kwarkwasa ko kisisina ta dena tasiri akan Audun, sabgar Kasuwancinsa kawai ya saka a gaba, shekarun baya lokacin da yake ta tiri tiri da
arin ganin BECHI GROUP OF COMPANIES ya tsaya da
afarsa lokacinsu ma wahala yake masa, ga tafiye tafiye ko yana
asar ma se su kwana su wuni basu sakashi a ido ba a wannan lokacin ne kuma tayi Arzi
i domin itace akan komai, Ashana idan babu a gidan gurinta za'a nema cefane se abinda taga dama za'a kawo ta ringa tara ku
i tana siyar Kadarori, Filaye, gidaje ta zuba yan haya da kuma sar
in gwal wanda ba sakawa take ba suna nan narke a drawer wani Design dinma wanda suka
irkireshi sun manta da Kalarsa.

Da su Zakariyya suka gama makaranta kuma dukda daman tun suna ciki take cusa su akan harkokin Audun kullum tana nuna masa ya kamata ace ya sakasu domin sune magadansa tun yanzu ya kamatu su san komai da yanda ake gudanar dashi ba wai se rana tsaka ne zasu kama abin ba, tun baya sakar musu har yazo dakansa ya yarda yana da bu
atar su horu akan sabgar kasuwancin nasa domin Bare ze iya ha'intarsa wata rana kamar yanda yake gani ga Abokanan kasuwancinsa da suka tashi tare da yawa sun dur
ushe kuma idan aka bi kadi daga
arshe yakan kasance wasu daga cikin ma'aikatan gurin ne da suka fitar da sirrunsu ga abokanan Hamayya har hakan ya janyo dur
ushewar gurin amma se tunanin sa be kawo masa cewar ba su ka
aine yayansa ba ko kuma ba su ka
ai ne magadan nasa ba kamar yanda take fa
a, burinta ya cika suka samu gurin zama dukda da farko sun fara ne a
anana ma'aikata tafi tafi suna ha
a tuggu da mana
isa irin wadda suka sha a Nono har suka saka aka tun
uke asalin wa
anda suka da mu
amansu na yanzu suka maye gurbinsu.

Aminu da Alhaji Babannan Al
ali Yakubu ne ya cusa su a gurin da kansa, duk kuma bala'inta haka tayi ta ha
ura wannan tasa ta matsa Yakubu
arami sukayi yanda sukayi har suka ciccibashi ya kai matsayin mataimakin Accountant General wato mataimakin Aminu a birinsu na ganin a sannu sun tun
uke Aminun se Yakubun ya maye gurbinsa ta haka suka shirya wannan
ulla
ullar suka zabtare lissafi wanda daman aikinsu kenan yawan ku
en da suka zabtare ne yasaka har ta tashi aka gane aka kuma
ora laifi kacokan akan Aminu dukda daman ku
in babu su, lissafi ne kan lissafi tsoho da sabo suka harha
a ya bada wannan Adadi amma Asalin abinda suka kwasa Naira Biliyan daya ce kuma tana kwance cikin boyayyen Asusun Crypto wanda Naziru ya bu
e musu, Asusu ne irin wanda ba'a iya tracing koda an tura ku
i ba za'a iya bibiyar su aga inda suka tafi ba can suke tura duk wata Albarkar office da suka samu kafin su zauna su ukun, ita Hajiyar, Zakariyya da Nazirun ayi kasafi kowa a tura masa nasa dan hatta da su
in ba wai ta yarda data bar ku
inta a hannunsu bane, wani sa'ilin ma Ruwan Cash take kar
owa ta zube a
aki abinta tayi ta shafasu tana jin da
To wani sa'ilin kuma idan Al'amura sun cukurku
e mata ta rasa mafita se Turai tace suje gurin Malam, tun akan Mu
amin Yakubun da Audu yaso yayi mata buyagi ya
i yarda Turai tace ta kawo ku
i, har yarjejeniya sukayi akan odan aiki beci ba zata maido mata ku
inta se gashi tana zaune Audun ya kira Yakubun wannan tasa ta fara amanna da sabgar dukda ko bu
atar ta taso ba ita take zuwa ba, Turai take bawa ku
i aje a mata abinda ya dace tunda sabgarta ce, ta da
e dayin amannan da Bin Malamai harda Bokaye zuwa gurinsu takeyi shiyasa har kawo yanzu Ta kanainaye Ali, shekaru an tasamma Hamsin amma se yanda tayi dashi
arin Aure da yake da burin yi tunda jajayen sahu ta hana haka yake ta gurgura rayuwa ga ku
i ya tara mata ita da yayanta suna wada
a Yau tana waccen
asar gobe tana wannan kayan Alatu kuwa kullum cikin siya takeyi dan ita ba irin Binta bace tana cin ku
inta Binta kuwa har yau har gobe abin naira goma sabo idan ka ganta dashi to Yaranta suka siya mata shi ko ma ace Jafar dan shine duk abinda ya gani na kwalliyar jiki a gurin hamsha
an mata ze siyawa Hajiyar abin takaici kuma ba zata saka ba musamman idan taji ku
in kayan, suturu da sauran kayan Ado da ku
i kam ta tarasu babu Adadi har tsokanarta Faisal yake yana cewa
"Hajiya idan kika mutu zamu ja kaya da yawa dan wlh inaga kason abinda zamu samu na gadonki se yafi na Alhaji" duk ranar da yayi mata wannan maganar kuwa Ashar da tsinuwa babu wadda baya sha tace sedai ubansa ya mutu tamkar ita
in zata zauna gadin duniya ne.

Bayan sun gama waya da Turai ta mi
e tayi sallar Ishar da aka idar tuni, tana zaune a gurin takaicin duniya ya isheta, jibgin kayan snacks da Kaji da akayiwa Abba Tee take tunawa ya zatayi dasu harda irin shinkafar Larabawan nan da ake dafawa da naman Rago yayi ligib aka masa yanzu duk sun tashi a banza ta saka ran ze cakewa Hafsatu ku
in da zasu maida wanda aka kashe harda riba se gashi wancan Dan is** yaron ya janyo mata Asara.

Tsaki ta rafka yanda kasan wata ri
iyar tsaka, ita ka
ai taci gaba da bala'i daga zaunen da take tana dannanwa Yakubu Ashar.

Faisal ya shiga kamar an jefoshi, ya kalli Hajiyar ya kalli cikin falon ganin ita ka
aice zaune kuma tana ta faman sababi yasa ya matsa gabanta yana cewa
"Hajjaju, kin
i yarda Jayy ya kaiki Asibitin da yace, lamarin nan naki fa kullum
ara gaba yakeyi gara a tari abin tun beyi nisa ba"
"Dan ubanka Faisal kaima mahaukaciyar kake so kace mun?" Ta fa
a tana mi
ewa tsaye, Faisal yayi wata dariyar sha
iyanci yaja ja da baya dan ya san tana iya kai masa duka yace
"Ni ba haka nake nufi ba, bafa ciwon hauka bane Ciwon damuwa akace kamar yana damunki kuma idan yayi yawa ne yake komawa haukan kinga ba zamu so haka ta kasance ba gara ki daure aje Asibitin nan asan abinda za'ayi dan wlh daga mutum yana zama shi ka
ai yana maganganu kodai wata rana aganshi warwas a
asa ya mutu ko kuma aga ya zura da gudu saitinsa ya kwance.." Be dire maganarsa ba ta fashe da kuka tana cewa
"Sedai kaga hauka ko mutuwa a kanka dan iska kawai, fice mun daga
aki kafin nayi maka baki"
"Allah huci zuciyarki ni ban fa
a dan kiyi kuka ba,
aki kuma sedai kiyi ha
uri amma yau a nan zan kwana bazan shiga can ba akwai tamu da Salim" yana gama fa
a mata ya shige kitchen da lafcecen takalmin Salim daya sace.

Abincin daya gani a gyare ya
ebi iyakar abinda ze isheshi ya sha
o plate ya fito har sannan Hajiya na kuka da fa
e fa
en maganganu marasa da
i akan Yakubu daya fara jangwalota da kuma Faisal
in daya
ora nasa wanda kuma be kyautu ace uwace take danganta Yaranta da irin kalamanba.

Kan kujera ya haye abinsa bayan ya kunna Tv ya
ure volume abinda ya fito da Hafsatu ya hau cin abincinsa ya gama ya gyara zama yana kallo, duk Tijarar da Hajiyar take zuba masa be tanka ba harta gaji dan kanta ta wuce
aki ta barshi anan bacci ya kwasheshi dan ko giyar wake yasha bazeje
akinsu ya tarar da Salim ba tsaf seya masa dukan mutuwar da yace ze masa.

Washe gari da safe zuwan Alhaji Zakatiyya ne ya wankewa Hajiya Binta ba
in cikin data kwana dashi jiyan, dukda sun fara maganar a waya tunjiya amma da yazo yayi mata bayani dalla dalla na yanda komai ya faru se ranta ya sakeyin fari
al.

"Ai ni wani tunani nakeyi, anya wannan shegen yaron ma ze bamu ha
in kai idan ya hau kujerar?
Chapter 89 · 0% Book details