← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 91

Sashe 71

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki Zubaida, aiko kin tunamun gobe idan Allah ya kaimu zanje na dubo su Hassan dukda dai nayi musu aike cikin satin nan amma gara naje na ganosu da kaina" Audu ya fada dan maganarta ta qarshe yasan da Zubaidan takeyi aiko abinda ya fada ya doketa har seda ta kware da Zobon da take sha ta ringa tuttula tari yana mata sannu dakyar ya lafa mata ido yayi jajir ta ringa maida nufashi zuciya na tafarfasa.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
"Sannu bari na shiga ciki nayi wanka kafin ki gama" ya fada mata bayan da tarin ya lafa mata ya shige daki tabi bayansa da harara tamkar idanunta zasu zazzago.

Tashi tayi ta hau tattare kwanuka ta sauka dasu zuciyarta fal da tunani, Wannan shi ake kira goma da Ashirin abu na nema ya hade mata biyu bata gama da wannan yar qauyen ba ya maido mata da zancen Zubaida ashe har aike yake musu yana kuma zuwa ya gansu?

Koda yake itace sakarya data manta da ita gaba daya matsalar Bara'atu tasha mata kai ta manta da batun tsinannun Tagwayen can data haifa to yanzu ita ina zata kama?

Bara'atun zata bari ta koma kan Zubaida?

Ko kuwa bari zatayi seta fatattaki Bara'atu sannan ta dira kan Zubaidar?

Tana hada abubuwan da zatayi amfani dasu a dakinsa take wannan lissafin a ranta, ta gama ta dauki ledar data zuba kayan, Nazirun na saman har yayi bacci Zakariyya kuma dasu Babangida zasu fita ya bisu yanzu da bata gama yanke yanda zatayi da Bara'atun ba tana bar mata yaron ya kwana da yan uwansa ranakun girkinta dan haka ta rufe qofarta ta koma Saman Audun tana ayyana matsalar Bara'atu zata fara kaudawa, zata bar Zubaidan tukunna dan tata me sauqi ce take ganin.

"Wai ni watannin Yan biyun nawa nawane yanzu?" Ta daure ta tambayi Audun bayan sun kwanta, ya danyi lissafi akansa kafin ya kalleta yace
"Kamar Goma kenan ko?

Ki lissafa tafiyarki Hajji yanzu watan sama kwanansa goma Azumi saura kwana Ashirin ko sha tara kinga a wata na Tara suke sun shiga na goma"
"Haka ne" ta fada daga nan ta maida kai ta kwanta tana ayyana dole ma ya karbosu sannan ya nemo me masa hidima dasu yawwa.

Haka dai tayi baccin daren babu nutsuwar zuciya, tunanin yanda zata qulla can ta rushe can kawai takeyi, tana jinsa yana jan minshari hawaye ya silalo mata, kamar ta zabga masa mari taji, duk akansa take wannan fadi tashin.

BARA'ATU
Washe gari da Audu ya fito ze tafi Kamfani ya shiga yi mata sallama bayan sun sake gaisawa bayan wadda sukayi da Asuba, cikin risilama ta maido masa da maganar jiyan saboda tace tana da magana idan ya dawo yace ta fada sannan babu damuwa.

"Se naga kamar dakunanmu sirrinmu ne sannan gyaran daki akwai wanda zakaga yafi so yayi da kansa yafi ganin komai yayi masa daidai kamar dai ni, shiyasa zakaga ko dakinka duk sanda nake ciki se na sake gyarawa koda ace Maman Zakariyya tayi gyaran dan bana jin komai ya mun idan ba da kaina nayi ba" Bara'atun ta fada masa da yanayin da take ganin ze fahimta.

Ya ringa jjjiga kai irin ya fahimce ta din nan sannan yace ze yiwa Bintan magana.

Seda da dare bayan ya dawo ya ya gama cin abinci ya sanarwa da Binta yanda sukayi da Bara'atun, daman tasha kwanan baqin ciki da yinin takaici dan zancen Zubaida da yayanta ya maqale mata a zuciya yaqi wucewa duk haka ta wuni babu walwala qyashi da hassada ya cikata ta ringa hasaso abinda Audun yake kai musu waya sani ko itama gidan ya gina musu irin nasu Bara'atu tunda itama a gidan Laka suke ga Damuna kar yace ze rufto akan Yayansa.

Seda ta gama sauraron Audun tsaf kafin ta narke fuska ta samu mafaka abin kuma yazo a daidai yanda take so dan haka tace
"Ka ga magana ta ta fito ko?

Jiya mena fada maka?

Ai nace maganar batayi mata ba tayi shiru me yasa tuna gurin ba zata fadi nata ra'ayin ba se dai ta jaka gefe ta gaya maka, yanzu ai se aga kamar cutarta nakeyi shiyasa ba zata yi magana a gabana ba.

Ni ina so muyi zaman lafiya da ita amma kaga abinda ta bullo dashi a taqaice dai tana nufin ni qazama ce banida tsaftar da zan iya yi mata gyaran daki ashe duk wanda nake maka ma in tazo seta sakeyi shikenan tunda haka ta zaba se mu zuba mu gani nida ita aga wanda ze sare in har tashin hankali take neman kai ka sani na iyashi wlh banda ma Allahya doramun qaunarta da son muyi zaman lafiya da ita meye ze hadani da wata Bara'atu ka bata labarin yanda muka gwabza da Gogaggiyar Karuwa ma balle ita karan kada miya" nan ta fara qoqarin tayar masa da Jidalinta.

Audu kuwa yaji dadin zaman lafiya baze so abinda ze tarwatsa masa kan gidan daya fara haduwa ba kuma se yaga zancen Binta gaskiya ne Bara'atu bata so ayi zaman lafiya shiyasa zata bullo da wannan maganar inda taso ayi yanda Bintan tace in yaso duk abinda yayi mata badaidai ba ta gyara daga baya baki alaikum.

"Yanzu dai kiyi haquri, zanyi mata magana babu wani tashin hankali ko rigima daze bullo a gidan nan zaku cigaba da zamanku lafiya yanda kuka fara" Audun ya tausheta, se ta fara magana kafinta kai qarshe ta saki kuka tana cewa
"Ni idan zan fada maka wani abu daya shafeta ai a gabanta nakeyi bana munafunci me yasa ita se a gefe zakuyi magana ta da ita?

Allah kadai yasan me take gaya maka akai na shiyasa naga kwanakin nan duk ka canza mun kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba waccen me kama da Zabiyar ta gidan Yakubu ce ta zugota zuwan da kukayi to nidai tunda naga alamun hade mun kai zakuyi tunda ita yar garinku ce ni kuma bare gara nasan nayi tunda sauran mutunchina kafin ka kunyatani ace qaramar Yarinya ta koreni daga gidan Miji"
"Wace irin magana kikeyi haka Binta?

Daga zancen shara seki fara sako wani soki burutsu meye wannnan? bana son irin haka kin sani ko?

Bari na kirata to tazo ayi maganar a gabanki zan yanke hukunci kuma dole kowa yabi abinda nace" Audun ya fada yana miqewa se ta tareshi da cewa
"Hukuncin me zaka yanke?

Bayanta zaka bi ko?"
"Se ki jira kiji tukunna" ya bata amsa fuuuu ya wuce kiran Bara'atu.

Da gudu Binta ta shige bandaki ta wanko fuska tana qyalqyala dariya, ta gama tsanewa ta murza hoda da Gazal kafin ta ware dankwalinta ta gyara daurin tayi fes abinta kamar ba ita ta gama kuka yanzun ba.

Bara'atu na zaune da yara Abdullahi ne yace su kwaso Littattafansu a duba saboda an kusa komawa makaranta saura sati daya.

Ba sanin abinda sukeyi tayi ba dan haka tana zaune kan Kujera kawai tana kallonsu tana kuma kwabar wanda taga ze bata littafinsa da zane musamman Zakariyya da ya fiya qiriniya se qoqarin batawa Yayyen littafi yakeyi da fensir Audu ya fada dakin sallama ciki ciki yana muzurai.

"Ina son magana dake" ya fada ya juya, tabi bayansa da kallo kafin ta miqe a sanyaya tana tunanin to meya faru kuma?

Hijabi ta dora kan Baqar doguwar rigar jikinta ta bi bayansa, shi kadai ta tarar a falon se Naziru dake ta rarrafe a qasa ta daukeshi ganin ya nufi qofar da bata rufe dakyau ba ta zauna kan kujera tana masa wasa yana dariya, satar kallon Audun tayi taga ya tamke fuska yana muzurai zatayi magana kenan Binta ta fito daga daki tana masa magana ganinta yasa ta katse tace
"Au kece?

Yau kinzo hira da kanki kenan ba tare da an kiraki ba"
"Uhm" kawai Bara'atu tace kafin ta gaisheta ta amsa tana zaunawa tana sake cewa Audu
"Kaga abin mamaki yau Bara'atu tazo hira damu"
"Ni na kirata" ya fada fuska a daure qasan ransa yana mamakin yanda tayi kamar bata san yaje kiran Bara'atun ba,
"Koda naji, nidai nasan badai Bara'atun dana sani ba" ta sake fada.
Chapter 71 · 0% Book details