Sashe 64
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma naji ma kamar nace fin qarfi kawai suka gwada musu amma tun Baban nasu yana da rai ya fitar da kowa ya bashi kason kudinsa?"
"Oho musu wannan su ta shafa tunda na rigada nayi abinda nayi, gidan ma kuma zan siyeshi na mayarwa dasu Bara'atun se naga ta tsiyarsu ko?" Ya bata amsa, ta zabura se kuma tayi saurin daidaita zama tace
"Aiko dai, ka barwa su Bara'atu ko ka barwa su Babangida?"
"Ita dasu ai duk dayane kuma duk abinda zanyi mata Alfarmarsu take ci ko iya ruqonsu da takeyi ai tayi qoqari Alhalin ubansu nada rai kuma ina da yanda zanyi"
"Uhm hakane, ni da zakayi haquri ma ka yafe abinda ya wuce daka maido su munci gaba da zamanmu kawai hankali kwance.
Duk se naji rashin dadi saboda mutane zasuyi ta kallona a matsayin wadda tayi silar raba Yaya da Mahaifinsu" Bintan ta zartar da hukuncin da take ganin shi kadai ne ze datse alaqar Audu da Bara'atu, tunda dai yace saboda yara yake mata komai to gara a kwaso mata yaran suzo suyi ta dabdala a tsakar gida da dai uwarsu tacigaba da morar Audun.
Wani kallo ya watsa mata me ma'anoni da yawa fuskarsa ta nuna mamaki qarara yace
"Dagaske kike ko wasa?
Kina nufin kin yafe mata abinda tayi miki su dawo muci gaba da zama tare?"
Seta rausayar da kai ita ala dole gata Allah tace
"Abinda ya faru ai ya rigada ya faru na dauki qaddara tunda Allah ya qadarta Yaron bame doguwar rayuwa ko bata silarta ba ze mutu, kuma yara ai basu suka mun laifi ba itan ma kuma na yafe mata Albarkacinsu"
"Amma naji dadin wannan magana matuqa in sha Allahu nan bada dadewa ba kuma zan shirya dawowarsu, harkin wankemun baqin cikin abinda ya faru kuma kin qara daraja a zuciyata saboda ba kowa za'ayiwa babban laifi irin wannan ba ya yafe harya cigaba da zama da mutum" Audu ya fada cikin madaukakin farincikin da shi kansa besan dalilinsa ba.
Ta maka masa harara a fakaice kafin tace
"A kullum burina kenan na faranta maka rai, inda na san wannan ze saka naga farin cikinka haka da tuntuni an aiwatar dashi amma yanzun ma lokaci be qure ba".
Daga haka suka tashi daga maganar da kowannensu da kalar manufarsa akan abinda yake fadi.
Binta tana maganane akan Babangida da Babannan, su take nufin Audu ya dakko su dawo gidan saboda kar Bara'atu taci gaba da cin arziqinsa ta dalilinsu yayinda shi kuma tasa kwakwalwar ta fassara masa Maganar ta a matsayin ya maido da Bara'atu taci gaba da zama da Yayanta a gidan wannan ne ya sanyashi farin cikin da beyi tsammani ba.
Allah ya sani bazeyi qarya ba ba kuma ze iya boye tarin qaunar da yakeyiwa Bara'atun ba saboda ita ya fara so har kawo yau kuma be dena sonta ba Halayen dara tsiro dasu daga baya ne sukayi tasiro gurin ruguza zamansu wanda yake fatan a yanzu ta hankalta ta gane kuskurenta.
Abu na biyu daya qara masa jin dadi shine ya san maida Auransa da Bara'atu ze gyara alaqarsu da Yan uwansa data gurgunce musamman Yakubu da Bilki, wannan farin cikin kadai ya hanashi bacci ranar, washe gari kuwa yayiwa Bechi tsinke sedai ya tarar da su Bara'atun har sannan basu komo ba.
Izza da girkan kan dai yana nan, ya saka a ransa Mace tayi kadan daya je bikonta, Hayatu Abokinsa ya barwa sallahu akan idan Sun Dawo yaje ya tuntubeta yaji ra'ayinta akan komawa gidansa.
"Kai yanzu Audu kana nufin kafi qarfin ka tare ta baki da baki kuyi maganar nan?" Hayatun ya tambayeshi cikin mamaki.
"Ga Amsar nan ka bawa kanka ai, ko yanzun saboda Yayana zan mayar da ita bawai dan ta cancanci na maida itan ba" ya bashi amsar da har ransa yasan qarya ya fada.
"Ai shi kenan, girman kai dai rawanin tsiya, kuma shi ya halakar da mafiya yawan Magabata" Hayatu ya bashi amsa.
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 25*
Wasa ya wasa, qaramar Magana ta zama gaske, kamar yanda Audu ya barwa Hayatu sallahu ya isar da saqo dan Bara'atu na dawowa gida ya doma sallama kofar gidansu, ta fita suka gaisa, batayi mamakin ganinsa ba saboda Abokanan Audunna Bechi sukan leqa sa'i da lokaci suga Yaranta.
Sukance Audu ya musu rana dan haka bazasu yada yaranshi da suke kusa dasu ba dan idan ka ture halin Audu na Rashin son gaskiya da shegen girman kai yana da kirki, kuma abun hannunsa be rufe masa ido ba daidai gwargwado yana kyautatawa Yan uwa da Abokanansa.
Bayan sun gaisa da Hayatun ta tambayeshi jikin matarsa datayi samu da jijjiga lokacin haihu da yake abun a gida ya faru se daga baya aka kaita asibiti abin se yaso ya taba mata kwakwalwa dakyar dai da taimakon Allah aka samu kanta dukda har yanzun dai bata koma yanda take a canbaya ba.
Seda suka gama gaishe gaishe kafin ya amayar mata da ainihin abinda ya kawoshi, tayi shiru tana sauraronsa harya gama kafin tace
"Shi Audun da kansa ya gaya maka ko kuma aike yayi maka?"
"Dakansa yazo lokacin baku gari shineya barmun sallahu akan nazo na tayashi biko da banbaki kafin ya dawo".
"Ya yardada gaskiyar ban kashe masa Da ba kenan yanzu?" Ta tambayeshi cikinkar yayyar murya, tausayinta ya kama Hayatun, Bara'atu mace ce me nutsuwa da matuqar haquri, sun taya Abokinsu baqin cikin rasata kuma a cikinsu da akwai wadanda sukayi niyyar neman Auranta se dai sanin waye Audu da tabbacin da suke dashi na cewar be dena sonta ba yasa suka gaza aiwatarda nufinsu saboda Tijarar Audu abar gudu ce tun zamanin yarintama balle a yanzu da karansa ua kai tsaiko.
"Bamuyi wannan maganar dashi ba, amma na tabbata a zuwansa baya raba nasaba da warwarewar komai, ta yiwu ya samu gamsuwar cewar baki aikata abinda aka zargeki dashi ba shiyasa ya dawo ku daidaita.
Nidai abinda zan iya ce miki kiyi haquri ki mayar da komai ba komai ba ki koma dakinki kodan saboda rayuwar Yaranki.
Kowa ya sani Audu be kyauta ba kuma shikeda laifi cikin duk al'amuran da suka faru amma kin sanshi, qi fadinsa baze barshi ya nuna gazawarsa ba sedai na tabbata ko be furta da baki ba zakiga Nadamarsa a aikace dan haka karkiyi wasa sa damar da ubangiji ya baki, kiyi tunani ki yankewa kanki hukunci".
Ta koma gida tana ta juya maganganun Hayatu, Inna Hajara bata ce mata komai ba dukda chanjin yanayin da ta ganta ciki se tayi tunanin kodai Hayatun yazo mata da Maganar Aure ne saboda irin zaryar da yakeyi tuntuni tasa tayi tunanin hakan.
Har aka kwana biyu da zuwan Hayatu Bara'atu bata sake ba, walwalarta ragu ainun, wani irin cakudadden yanayi take ji na farin ciki, damuwa da kuma zullumi.
Farin cikinta Bikonta da Audu yayi domin ba zatayi qarya ba Allah ya sani tana qunar Audu ba kuma ta tsammanin zata iya zama da wani Namiji a duniya ta soshi bayan Audun wannan dalili yana daga abinda yasa zamanta a gida babu marshinshini be wani dameta can ainun ba,
Damuwarta kuma tunanin idan ta yarda ta koma wace kalar rayuwa zatayi a gidansa Alhalin Binta tana nan?
Zullumin da take ciki kuma shine na tunanin shin Audu ya gane cewar Binta sharri tayi mata ne da har ya nemi ta koma ko yaya?
Zata so ta san amsar tambayar nan domin itace zata qara mata qwarin guiwar Amincewa buqatarsa ko akasin haka.
Zata so su hadu dashi suyi maganar nan kafin ta kaiga yanke hukunci,
"Nikam lafiyarki Bara'atu?
Yaro na tsaye kanki yana magana tun dazu kamar me bacci kin masa shiru alhalin idanuwanki a bude suke?" Inna Hajara data leqo daki dalilin maganar Babannan da take jiyowa yana ta maimaita abu daya, Gidan kitso Bara'atun tace yaje ya tambayo mata tunda ya shiga dakin yake fada mata matar tace taje yanzu bataji ba balle ta bashi amsa tayi zurfi cikin tunani har seda Inna Hajar tayi magana da qarfi kafin ta ankare.
"Banji shi bane Inna, me kake cewa kai kuma?" Ta fada tana gyara zamanta.
Inna Hajara ta shiga cikin dakin da kyau tace
"Ai daman ba zakiji shi ba, kai yi tafiyarka wasa, ki fadamun me yake damunki tun randa Hayatu yazo gidan nan na ke lura dake yanayinki ya canza".
Barin maganar a ranta baze magance mata komai ba kuma a wannan gabar tabbas tana buqatar Abokin shawara wannan abun yasa ta fuskanci Inna Hajarar ta shiga fada mata yanda sukayi da Hayatun ranar da yazo.
Baki ta saki galala tana kallon Inna Hajara wadda ta taqarqare ta rangada guda kafin ta daga hannu sama tana cewa
"Allah na gode maka daka sa zanga wannan ranar da raina ban mutu ba, Allah na gode maka daka karbamun Addu'ata.
Dama bangaya miki ba?
Ba a banza Audu ya jibanci lamuranmu fiye da da ba, tun baroqarki gidansa ban taba yin salla na tashi ba tareda na roqi ubangiji daya bankada sirrin duk wani Azzalimi daya qulla miki wannan mugun shairin ba gashi kuma Allah maji roqon bawansa ya amsa roqon mu.
To meye abin damuwar daya kika kasa walwala?
Wannan ba abin kiyi rawa kiyi shewa ki godewa Allah ne amma shine kika tsangwami kanki kwana kusan uku bana tsammatar kinyi dariya?
Ko kuwa bayan Batun komen akwai wata maganar ne?".
"Babu wani abu bayan wannan amma ni abinda ya dameni Inna banida tabbacin cewar Audu ya zabi ya maidani saboda gane gaskiyar abinda ya faru a baya ni nafi kyautata zaton zeyi hakan ne saboda Yayansa.