← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 91

Sashe 11

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dada ta yafa gyale ta yafice shi suka yi soro, Goggo Fadi, Maryo da sauran Maqwafta yan tsogumi da suka baza tabarma, sun gama kallon dakin Balaraba suka fito aka kafa gulmar ana jira aga me za'a sakawa Bara'atu ita kuma,
"Koda yake ina dakin ma?" Fadar Goggo Fadi, Maryo ta karkace baki tace
"Dukdai qaryar Birnin ta qare, ayita zuwa ana burga a bikin jama'a ga nashi ya tashi ko dakin da za'a ajiye Amarya babu idan da gaske da kudin ai daga tsaida rana yaci a dora ginin Bulon sumunti ma bana qasa ba" suka tafa da matar Hashimu dake kusa da ita.

Dada kuwa suna zuwa zaure tace
"Ina ka tafi Audu bayan kasan halin da ake ciki babu inda dan uwanka bw zaga a garin nan ba amma ba'a ganka ba Jama'a har ana cewa ka gudu".

Dariya ta kwace masa yace
"Na gudu kuma Dada naje ina kamar wani mara gaskiya?"
"Oho dai duk ba wannan ba, Hasiya tazo ta gaya mun Baban Bara'atu yace bazeyi mata kayan daki ba, da ace mun san da tariyar nan da tuntuni mun fara shiri amma yanzun ma se ayi amfani da abinda Allah ya hore, na bar muku dakina tunda kaga yafi girma ni se na koma na Malam, Babana kuma ya shiga cikinsu Idrisa (Yaran Yaya Baba da suke zama a gidan) kafin muga abinda Allah zeyi, idan an kwana biyu filin can na gefe seka shigo mata dashi ayi bandaki da gurin girki irin na Yayanka kaga shikenan a sannu Allah ze hore duk kuyi muhalli irin wanda kuke buri, wancan gadon naka ma gaskiya Audu ba'a bawa Amarya ba ga Katifa duk Babana yaci qaniyarta idan da sarari ko katifa ce ka siyo da ledar daki a shimfida mata".

"mma Dada da baki fita daga dakinki ba wancan dinma ya isa ta lallaba kafin muga abinda Allah zeyi" Audu ya fada, Dada ta juya tana cewa
"Kaje dai muga ko katifar da Ledar zasu samu" ya tsayar da ita yana cewa
"Shaf na manta da Ledar wlh sedai ko Bilki taje yanzu inda za'a samu, leqa kiga ga kaya nan dai na samu dukda dai nasan basu kai yanda akeyi ba".

Dada ta leqa, baki ta saki ganin kaya tuni kuma yara da matan Unguwa da sukazo shiga gidan suka baibaye motar ana kallo dan ba'a taba ganin irinsu a garin ba.

"Audu, Kano kaje har ka dawo wannan kaya haka?" Dada ta fada cikin mamaki, Audu yayi murmushi yace
"A turo Bilkin ta samo Ledar tunda ita akw fara shimfidawa ko anjima zan miki bayani.

Dada ta koma ciki bakinta a washe yaqi rufuwa ta tura masa Bilki.

Gidanta ta tafi ta dakko ledar data siya take shirin canza ta dakinta bata rigada ta shimfida ba dama ta bari se an gama hidimar Biki nana da nan aka hadawa Amarya daki ga gado na Alfarma kamar wani gidan zoo haka mata keta leqawa masu gyaran daki na korarsu dan sun hanasu yin aikinsu yanda ya kamata tuni kuma labari yakai wa Innar Bara'atu, ta fashe da kuka tana cewa
"Allah na gode maka daka nunawa masu gulma da munafurci qarshensu" tun safen suke qullawa da warewa da yan uwanta akan yanda za'ayi, ta hada dan abinda ya samu, Gadon katako taso tayiwa Bara'atu dan ance Amaryar Yakubu ma shi aka mata amma abinda suka hada baze isa ba kuma wanda za'a tasa ya tafi Kumbotso a yammar shine aiki har sun saddaqar a dauki na qarfen anje shima me siyarwar wai baya nan abin duniya duk ya mata yawa sega wannan labarin farin cikin dukda tasan wata sabuwar gulmar za'a samu ace Miji ne yayi mata ko babu komai sabon salo ne dan babu yarda Miji yaso haka a garin har yayi mata kayan daki.
https://chat.whatsapp.com/Hi7n2ddpUxZ24e1tJyREqZ
*Assalamualaikum, My name is Maryam hassan, I sell Laces range from 35k to 250k beautiful n classic designs, kids clothes , materials, shadda gezner men materials range from 30k to 120k , women veils , 8k,12k,15k,25k,all available muna bada sari muna maraba da masu siyan daya, muna hada na lefe da kayan barka , location Kano, FREE DELIVERY NATION WIDE BI MA'ANA FA DILIBIRI KYAUTA A TSADAR KUDIN MOTAR NAN YAR UWA ME KIKE JIRA?

MAZA KI TUNTUBE MU
just buy what u want n we deliver safely in Sha Allah,,,,,,,, 07088361522*
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*NAGODE*
*FREE PAGE 5*
Kafin dare dakin Amarya Bara'atu ya dauki haske bakin yan gulma yayi muqus qiri qiri Goggo Fadi ta kasa boye baqin ciki da wannan abu ta ringa yada magana wai Dada tadai tsananta binciken inda Audu yake samunkudi haka ya za'ayi ace daga fita ya dawo da irin kayan nan waya sani ma ko wasu ya bige ya dakko?

Ita dai Dada tun tana mamakin lamarinta harta dena, a zamansu idan aka ce mata wata rana Goggo Fadin zata zama yanda take a yanzu qaryatawa zatayi se gashi da ido ta take gani bawai fada mata akayi ba.

Innar Bara'atu ta aiko da kwanuka da tayi tanadi aka jere masu reras tun daga qasa har sama.

Tana can bagaren Balaraba tun safe Dada tace suje can da qawayenta suyi wanka suka karya nan suka hade da qawayen Balaraba ana ta raha har dare kafin suka fara shirin tarar Angwaye.

A bangaren Balaraban tayi wanka tsaf ta shirya cikin daya daga kayan daya dinko mata daga Kano, Balaraba ta bata Humra ta shafa dan ita dai babu shiri aka hankadota, suna zaune Aisha tazo tace au koma can an gama gyara mata daki suka bar Balaraba da nata qawayen can kuwa se santin daki sukeyi qaunar Audu ta sake linkuwa a zuciyarta ko banza ya fitar da ita kunya ya mata abinda tasan ko Baffabta bazeyi mata kamarsa ba.

Se qarfe Goma Aka rako angwaye, Yakubu aka fara rakawa tunda shine babba kuna duk Abokanan nasu daya, bayan barkwanci da abinda aka saba akayi siyan baki sukayi musu yar nasiha da tunasarwa akan aure da qalubalen dake ciki dan gaba daya Abokanan da sukayo rakiya su bakwai mutum daya ne mara aure wasu da yayayensu dan haka sun san yanda lamarin yake nan akayi addu'a suka sallami yammata wadanda zasu tafi gidan Fadima Amaryar da su Balaraban suka kawo garin harta hadu da Yakubu.

Daga nan aka raka Audu, basu jima ba nan ma akayi addu'a kowa ya watse suka raka Abokanan qofar gida kamin suka koma ciki, Yakubu ya shige bangarensu bayan ya
yiwa Audu sallama ya sakace qofa, Audu ya tsaya kawai yana tunani, duk yanda yaci burin ranar auransa gashi bata zo masa a yanda yake mafarki ba.

Lissafi yake yanzu Yakubu Asirinsu a rufe suna da komai a bangarensu babu wanda ze san me suke ciki amma shifa?

Rufin asirin ma bandakin da yake kusa da ace har yanzu da tsohon suke Amfani da tareren yayi yawa.

Haka ya shiga daki jiki babu karsashi sosai ya saka a ransa bazeyi komai ba har se randa ya samu yanda yake so dangane da muhalli.

Bara'atu ko harta fara gyangyadi akan sabuwar Katifa daman jiya ba wani baccin kirki sukayi ba kuma sun tashi da wurwuri motsinsa ya farkar da ita ta shiga jan mayafi tana boye fuska.

Ya bude musu Kazar da suka shigo da ita dakyar ta iya ci saboda Yunwar da takeji taci kadan tasha ruwa tace ta qoshi.

Qofa yaji ana kwankwasawa, seda ya tambayi waye yaji muryar Inna Hasiya, ya bude ta miqo masa wani qaton Flask din ruwan zafi wanda ya siyawa Dada a Kano guda biyu saboda lokacin sanyi dukkansu cike da ruwa tana cewa
"Da akwai na sirki nan cikin bambu", ta sake miqo masa wani kantamemen baho irin na wankan Jego tana cewa "Allah ya tashe mu lafiya".

Kamar wani munafuki haka ya tattara bahon da fulasan gefe ya ajiye ya kalli Bara'atu data takure a gefen gado kamar jinjirar kyanwa yace
"Kiyi shiri ki kwanta dare yayi"
Da "toh" ta amsa masa ta miqe amma duk ta diririce ta rasa abinyi fahimtar kamar kunya takeji yasa ya fita ya tsaya daga qofar dakin, yana fita ta bude jakar da aka sako mata yan kayanta.

Doguwar rigar yadi me laushi ta ciro da qaramin Hijabi.

A gurguje ta shirya, ta ninke wanda ta cire kafin ta haye gado ta duqunqune kamar me bacci daidai nan Audu ya shiga dakin.

Shirin baccin shima yayi, ya hau kan gadon yanajin wani banbara kwai wai yau shine gado daya da mace.

Dukda yanda yayiwa kansa Alqawarin baze tabata ba har se sunyi kebantaccen guri kamar nasu Yakubu amma ya kasa, cikin tattali da tsantsar So ya mayar da ita tasa, a cikin daren ya taimaka mata ta gyara jikinta kamar yar baby haka ta shige bahon ta gasa jikinta tsaf kamar yanda yayarta ta gaya mata kafin tayi wankan Ibadah dukda kunyar idon Audu haka ta shirya shi kuma ya juye ruwan bokiti ya fita dashi ya dawo ya goge gurin tas kafin ya sirka wani ruwan ya dauko fitila ya wuce bayi.

Seda yayi wanka shima ya shirya kafin ya kwanta gefen Bara'atu da tuni bacci ya kwasheta, wani irin farin ciki da annushuwa yake ji, daman haka auran yake?

Kai dole ashe Abokanan sa su ringa cewa Aure da dadi.

Ya tuna Yakubu ma yana can yana kashe Arna qilan yanzu shi kadai kamar sabon kamu ya fashe da dariya a haka bacci ya dauke shi shima cike da nishadin samu Bara'atun tasa a yanda beyi tsammani ba.

Kiran sallar farko ya farka dan ya rigada ya zame musu jiki tun suna qanana da an kira sallah Malam ze tayar dasu suyi nafila kafin lokacin Asuba su fita masallaci shiyasa jikinsu ya saba duk gajiya duk bacci basa tsallake wannan lokacin se sun farka.
Chapter 11 · 0% Book details