← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 91

Sashe 24

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi yayiwa Tunde cikakken kwatancen zuwa inda yasan idan Baballiya ya gani ze iya kaisu gida kafin suka dauki hanya suna musu fatan sauka lafiya.

A ranar tare suka fita da Alhaji gurin da yake aiki wato Matatar Mai ta Kaduna.

Audu na zaune a office dinsa tsayin lokaci bayan Alhaji ya fita ya barshi sannan ya dawo ya same shi.

"Na barka kai kadai ko?

Meeting muka yi" Alhaji ya fada yana zama akan kujera, Audu yace "babu komai ina ta kallon Talabijin ma bansan lokacin ya ja haka ba".

"Dalilin da ya saka na taho dakai saboda kaga gurin da nake aiki, ko ban fada maka ba kasan nan din ina ne, matatar Mai ce, itace Ma'aikata mafi girma da daraja da kuma kawo kudin shiga a Arewa baki tana kuma takewa ta Legas data fatakwat baya.

Na so ace kayi karatu me zurfi ko da Diploma ce saboda a nan gurin takardar sakandire sedai a daukeka a matsayin lebura bawai babban Ma'aikaci amma dukda hakan bata baci ba, na dade ina so na bude gidan Mai a Kano, sedai rashin Ido ya saka ni daqile qudurin nawa amma yanzu dana hadu dakai ina ganin lokacin ne yayi ina so ka gwada harkar mai domin ana samun Alkhairi sosai da sosai a ciki"
Audu yaji abin ya masa girma, domin a sanda yake bunburutu yayi bincike cikin sabgar yaso ya shigeta da gaske amma irin maqudan da aka karanto masa wai a talauce ze zuba a matsayin jari bashi dasu baya kuma tsammanin nan da shekaru goma ze mallake su sedai kuma lamarin ubangiji babu yanda baya zuwa se gashi ya samu tayin shiga harkar daga sama duk se ya rasa abinda zecewa Alhajin.

Sunyi maganganu sosai, Alhajin yace masa idan ya koma Kano ya nemi guri da yake ganin zasu fara bude gidan Man ze hadashi da wakilai da zasuje tare da zarar guri yayi za'a fara aikin ba tateda bata lokaci ba domin tuntuni ya samu lasisin yin hakan Allah ne bai nufa ba se yanzu.

Suka yita hira Alhajin yana fada masa yanda harkar take, sirrikan kasuwar da yanda ake tafi da ita dashi kansa abubuwan daya mallaka a ciki da wadanda yake shirin mallakar.

Se yamma lis suka koma gida cike yake da murna yana hasaso yanda zata fashe nan da wani dan lokaci Audu ze zama manajan gidan Mai.

Ya ringa hasaso nan da shekaru kadan shima ze mallaki nasa idan Allah ya yarda.

Seda yayi sati cif kafin ya shiryi tafiya Kano tareda wakilan da Alhaji ya hadashi zasuje duba gurin da za'a assasa gidan Mai, a cikin satin kullum se sun fita da Alhajin haka yayi ta sakashi cike ciken takaddu, ana gobe zasu tafin kusan raba dare sukayi a tsakar gida da Binta suna hira wadda ke cike da Alhinin rabuwa da juna.

Wata irin shaquwa ce ta qullu tsakaninsu, shidai Audu a bangarensa babu wani abu face ya dauki Bintan a matsayin qanwa kuma diyar mutum mai daraja a gurinsa da yake shirin canza rayuwarsa.

Sedai ita ba haka bane a bangarenta, duk yanda taso hana kanta ta kasa tilas ta amince da tana qaunar Audun kuma duk sanda ta tuna haka se taji kamar ta rufe kanta da duka tsabar takaici.

Bata san sanda haka ta faru ba, yaushe zuciyarta ta yanke mata wannan danyan hukunci dukbata sani ba kawai dai ta tsinci kanta dumu dumu a soyayyar Audu Bechi kuna ta gagara boye hakan ta nuna masa sedai sam yaqi nuna mata ya gane abinda ta ke ciki ita kuma ba zata iya karya bille ta zubda girmanta ta fada masa da fatar baki ba domin ta wuce da Ajin haka, zuciyace me aiki gaba gadi ta janyo mata ba tareda tayi shawara da ita ba koda yake bataga laifinta ba, Audun Namiji ne ingarma irin zabinta.

Dukda cewar be yi wayewar Azo a gani bata tabbatar zuwa gaba za'ayi Namijin gaske musamman yanzu da ta fara hango haske a gobensa saboda yanda Dady yake tsamo tsamo cikin Al'amarinsa, a kuna dan zaman da sukayi yanda yake bata labarin Harkokin da yake tabawa ta tabbatar Gobensa zatayi kyau.

A tsarinta kuma tana so ta auri Namijin da zasu ginu tare suyi Arziqi tare ta yanda babu wanda ze bigi qirji yayi mata kankanba akan sa.

Haka ya tattaro ya dawo Kano, beko huta ba suka shiga neman lokashon inda za'a kafa gidan Man.

A cikin kwanaki biyu aka samu, filin a bakin titi yake sukayi dace na Magada ne ana kan gabar yin rabo daman neman me siya sukeyi babu bata lokaci akayi ciniki suka karbi fili a bisa qololuwar darajarsa.

Abinda ya qara bawa Audu mamaki hatta da Filin da sunansa aka yi takarda, be manta ba gidan man kansa Alhaji ya tambayeshi sunan da yake so ayi masa register dashi yace masa meze hana ya saka sunansa Zakariyya Paki amma Alhajin yace masa Aa, shiya bawa zabi daga qarshe BECHI ENERGIES akayiwa gidan man suna sannan ga fili an siya da sunan Audu.

Cikin qasa da watanni biyar aka bude gidan Man wanda ya kasance na farko a Kano mallakin mutum ba kamfani ba, dangi yan uwa da Abokai sunyi masa murna.

Yan Bechi duk sunzo bude gidan Man dukda yana gayawa kowa bana sa bane na ubangidansa ne, ya kuma debi ma'aikata harda Yayan yayyensa silar barowasu Bechi kenan suma.

A taqin lokacin Audu yaje Kaduna babu adadi, soyayya ce ta qullu tsakaninsa da Binta wadda besan sanda shima ya afkawa soyayyar tata ba.

Abinda ze iya cewa kawai Bintan tayi daidai da tsarinsa, kuma ita ta bashi fuska shiyasa beyi shayi ko jin dar na amincewa da buqatarta ba dukda ya kanga kamar abin bame yuwuwa bane amma tabbas yana son Binta kuma in har ya samu dama ze aureta.
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*HALIN KISHI*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 400 (PROMO PRICE BAYAN KAMMALA FREE PAGES ZE KOMA 500) A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*FREE PAGE 11*
Kamar da wasa magana ta qullu tsakaninn Binta da Audu, da kanta ta sanarwa da Mahaifinta wanda yayi matuqar murna da Al'amarin saboda shidai Allah ya saka masa qaunar Audub a ransa tamkar dan cikinsa haka yaje jinsa.

Mahaifiyar ta dai saisa saisa, bata nuna qinta ga Al'amarin ba haka kuma batayi murna ba saboda a ganinta Audun barene.

Haduwar hanya bata isa tasa Alhaji ya daukake shi haka bayan aminta dashi akan dukiyarsa kuma yace zero dauki Yarsa mafi soyuwa ya aura masa ba.

Yan uwanta kuwa kaf da sukaji take suka nuna qin Amincewarsu.

"Allah ya sauwaqe, ke wace kalar wawiyace Binta?

Kodai irin Asirin da yayiwa Dady duk ya rikice a kansa kema yayi miki?

Daman qauyawan nan da surkulle suke wlh ban yarda da wannan Al'amarin ba Asiri yayi muku daga ke har Dadyn kuma dole mu tashi tsaye mu karya" Salima da take takewa Binta baya a fannin tsiwa ta fada aiko Bintan ta maka mata harara tace
"Idan ma Asirin ya mun meye naki a ciki?

Ke zaki aure shi ko kuma ke zaki zauna dashi?

Da kika Auro Inyamuri waya ce miki qala seni da zan auri Bahaushe dan uwana.

Ni bana fada muku dan ku yarda ko karku yarda bane kawai dai a matsayinku na yan uwana ya kamata ku sani Aure da Audu kuma babu fashi in sha Allahu" ta fada tana murguda baki.

Haka aka ringa dauki babu dadi, sun nuna qin Amincewarsu qarara Jalal ne kadai da yake Namiji beqi abun ba dukda be nuna dokinsa a fili ba tamkar dai mahaifiyarsu amma da yake Bintan ta kafe kuma Alhaji yayi na'am haka aka qulla magana.

A bangaren Audu kuwa sanda ya sanarwa da Yakubu da sukaje hutu maganar tashin farko shima ya nuna be yarda ba.

"Haba Audu, daga ka fara samun duniya sakayyar da zaka farayiwa Bara'atu da ita kenan ta qarin aure?

Karka manta sadaukarwar da yarinyar nan tayi maka.

Kwata kwata ma shekarun mu nawa da auran matan namu nawa suke?

A bariki fa sa'anninsu har yanzu suna gaban iyayensu ana musu kallon qananan yara kai ko me yasa ba zaka barta taci arziqin da kuka tara tare cikin kwanciyar hankali ba?" Yakubu ya fada.

Audu ya karkace, shi fa a yanzu Jin Binta yake kamar daga sama aka yo masa wahayinta tsabar so.

Ba wai ya dena son Bara'atu bane Aa, yanda Bintan ta iya magana da tattala Namiji idan yaje Kaduna har ya dawo Kano yayi satittika kafin ya sake komawa cike yake da bege da shauqin kalaman data ciko shi dasu.

Ga tarin wasiqu datake rubuta masa masu dauke da kalamai masu gigita tunani, haka ze ringa dauka kullum yana karantawa idan sun qara ya ringa maimaitawa har se yaje ta sake hadoshi da wasu ya dawo yaci gaba da tisa karatun kalaman soyayya.

Irin wadannan abubuwan yasa ya fara ganin baiken Bara'atu wadda bata san komai ba bata kuma iya komai ba se abinda ya koya mata ko ya nuna mata.

Ya kasa gane banbancinta da Binta wadda ta kereta a shekaru, sannan ta bangaren wayewarsu babu hadi Binta haihuwar cikin Turawa girman Kaduna zagaye take da gogaggun yan Boko yan uwa da qawaye baya ga haka ita din tana cikin mutane da Allah yayi masu dan banzan wayo da iya magana.

Duk dakiyar mutum tana iya canza masa akala a cikin ruwan sanyi yayi abinda take so ba tareda ya ankare ba.
Chapter 24 · 0% Book details