Sashe 61
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anya kai ko da zuciya a qirjinka Audu?
Me yasa baka tunani da kwakwalwarka ka sakarwa zuciyarka Linzami?
To wlh ka farka tun kafin lokaci ya qure maka, wannan rayuwar da ka dauka ta rashin tunani babu inda zata kai ka illah Nadama da dana sani mara amfani.
Ita kuma matarka ka gaya mata tabi a sannu, ina tausayawa rayuwar da zatayi a gaba haqqi dabaibaye da ita.
Se yanzu na fahimci yanda kuka taru kaka kassara rayuwar Bara'atu kuka laqa mata mata mugun qazafi to wlh haqqinta kadai ya isheku a duniya idan har baku nemi yafiyarta ba ina kuma fatan yanda Ubangiji ya wankeni itama ya wanketa ya bayyana gaskiyar duk wani mugun qulli da kukayi akanta" tana gama fadar haka ta gyara kwanciya ta jera yaranta a gabanta bayan ta bashi baya ta rufe ido zuciyarta na tafarfasa tsanar Audu me tsanani tana hudata.
Badan kar tayiwa Allah butulci ba da tace inama ya jinkirta bata wannan gwalalon kyauta a wani gidan inda yafi na Audu Alkhairi?
Amma dukda haka ta godewa Allah ta sake gode masa bisa ni'imar da yayi mata.
Tamkar wanda lakarsa ta tsiyaye haka ya ringa jefa qafafu harya fice daga Asibitin, ya manta da Musbahu sukaje hakanan beyi tunanin mota ba ya ringa taka qafafunsa bude ido kawai yayi ya ganshi a qofar gidansa tundaga Asibitin Murtala, tafiya yayi wadda rabon da yayi irinta a qafa dai ze iya cewa tun Zamanin yana Audu qolo.
Binta na zaune a tsakar gida da jama'arta da suka zo yi mata Sallama makwafta da kuma Turai da Mardiyya Wata sabuwar qawa da tayi babu dadewa.
Yanda Audun ya shigo ya saka duk matan binsa da kallo kamar ma be lura dasu ba haka ya tsallaka ta tsakaninsu ya wuce sama, Turai ta kalli Binta kafin tayi mata alama da ta bishi ta miqe tana murmushin yaqe ta sallami maqwaftan ya rage Turai da Mardiyya kafin ta haye sama gurin Audu.
Yana zaune akan kujera yayi irin zaman nan na balance ya bude qafafu da hannayensa kana kallonsa kasan da akwai abinda yake damunsa.
Cikin salo da kissa ta bude firji ta dakko ruwan sanyi ta matsa gabansa ta tsiyaya masa tana cewa
"Lafiya dai ka shigo kamar baka cikin hayyacinka?"
Seda ya kwalwale ruwan ya miqa mata kofin kafin ya yunqura ya gyara zamansa yana kallonta dakyau yace
"Zubaida ta haihu"
"An ganta kenan, a ina?
To mema ya shafemu da ita ko haihuwar ta?
Halan gurin farkan nata ta je ta haihu acan ko?" Ta yi maganar tana yatsina fuska.
Miqewa yayi ya nufi daki yana tafiya a hankali yace
"Ta haifi tagwaye duka maza, kamanninsu daya dani"
"Me kake nufi?" Ta miqe a zabure qirjinta na dukan dubu dubu kunnenta na mata amsa kuwwar Tagwaye Maza da ya fada, se ya waiwaya ya kalleta yace
"Karmu fara wannan maganar ma.
Kin cuceni kin rabani da matata, waima meye dalilinki na sheganta mun Yaya Binta?
Me yasa kikayi haka?"
"Ni na sheganta maka yaya?
A yaushe akayi haka?
Tsakaninka da Allah ni da kai mun taba magana nace maka cikin Zubaida shegene?
Hasashena nayi na fada kai kuma tunda kasan da walakin goro a miya ka tabbatar haka ne to kuma se kazo kace na cuce ka dana maka me?
Da kake wannan babatun ma me kake nufi ka karbi cikin kenan ko Yaya?"
"Ciki daman nawane" ya bata amsa yana shigewa ciki dan in ya tsaya din be san me zece mata ba.
Gaskiya ta fada magana tayi me harshen damo shi kuma ya hau ya zauna daram wato ta tabbata ya zama wawa kamar yanda Yakubu ya fada Bintan ta karanci rashin tunani irin nasa shiyasa tayi amfani da wannan ta cusa masa tunani a kwakwalwarsa harta kaishi ga yanke danyan hukunci yanzu gashi tun ba'aje ko ina ba ya dawo yana dana sani mara amfani dan yasan ya rasa Zubaida ba zata sake yarda ta komo gidansa a matsayin matar aurensa ba.
Daren ranar Binta ta wuce Saudiyya cikin tashin hankali bayan sun rakaya dasu Turai sunje Asibiti sun ganewa idanunsu Tagwayen da akace Zubaidan ta haifa.
Kuka wiwi ta ringayi kamar wadda kanta ya kwance wai ya za'ayi tazo a bayanta ta haifi tagwaye kuma Maza kenan yanzu ta fita kasafi cikin dukiyar Audu kenan.
A Saudiyyan haka tayi Ibadar rabin Addu'arta ta Allah ya sa tayita haifar Yan biyu Maza ne bayiwa kanta wata kwakwkwarar Addu'a ba balle Yayan da take roqon a bata haka aka sauke Hajji ta dawo kamar yanda Audun yayi tunani daga ita se Kayan data tafi dasu yar tsarabar data yiwo bata kai kota kashi goma cikin uban kudin data tafi dasu ba.
Bayan dawowarta ta tarar da an kwashe kayan Zubaida wannan ya dan rangwanta mata damuqar data saka kanta a ciki.
Daman daga Asibiti Zubaidan gidansu ta wuce kamar yanda Mahaifinta ya buqata Yakubu yayi iyakar roqon da ze iya amma Malam Hassan yace yayi haquri kawai.
Ran Yakubun ya sake baci matuqa ya dauka Audun zeyi Nadama ya kuma nemi su sasanta ta koma dakinta amma seyaga akasin haka.
Ya dai siyawa Jarirai kayan na Alfarma haka itama Maijegon ya hada da ita da Manya manyan Ragunan suna dana Qauri ranar kwana biyar da Yan Bechi suka zo wanda suma Yakubu ne yaje ya sanar dasu suka kai kayan Barkar.
Da aka kwana biyu har ya koma Ikko ya sake dawowa wata daya bayan haihuwar kenan ya sake tarar Audu da zancen ya suke ciki sun daidaita zata dawo idan ta yada wanka ko kuwa kai tsaye babu boye boye yace masa
"A gaskiya ni bazan iya zuwa nayi bikon wata mace ba, zan bata lokaci harta huce daga fushin da takeyi, idan ta nuna buqatar cigaba da zama a gidana se mu daidaita".
Yakubu ya rasa abin fada ya ringa kallon Audu kawai yana jin kamar ya rufeshi da duka.
Ya dade yana ganin marasa hankalin mutane amma Audu leader ne, cikin tsantsar takaici yace
"Abinda ya hanaka ka maido da Bara'atu kenan tunda bata furta da bakinta tana so ta dawo ba ko?"
"Ka gane ashe, ai Allah ya kallo duk wani abu daya kamata ace nayi da ze nunawa Bara'atu ta dawo dakinta nayi.
Kana kallo dawainiyar gidansu kaf har abinda be zama dole na ba yi musu nakeyi, duk wata se nayi mata aiken kudi da kayan abinci kuma idan naje Bechi ina zuwa naga Yaran to me kuma ya rage da zanyi ya nuna mata Biko nakeyi?
Sena zubarda girmana na roqeta ta dawo bayan Alfarma zanyi mata naci gaba da zama da ita bayan laifin data aikata mun?
Itama Zubaidan ai koda ina da laifi nata yafi yawa a ciki, me yasa bata tsaya tayi mun bayani yanda zan fahimce ta ba amaimakon haka seta ringayin abubuwan da zasu qara tabbatar mun da zargina akanta ni kuma shine ya tunzurani na yanke hukunci.
Kuma ai ita har haquri na bata da naje Asibiti tace babu ita babu ni kuma ta hanani taba Yayana shine kake so naje gidansu nace ta dawo salon ta samu damar rainani ko to ni bazan iya wannan aikin zubarda mutunchin ba" Audun ya fada cikin dagawa.
Mamaki, takaici hade da baqin ciki sukayiwa Yakubu rubdugu lokaci daya amma ya rasa kalmar da zeyi amfani da ita gurin zagin Audun dan haka ya kada kai kawai ya wuce ya barshi yana jinsa yana masa magana akan ya tsaya mana ina zashi be ko waiwaya ba.
Duniya dai akace tafi bagaruwa iya jima, tabbas yana jiyewa dan uwansa randa muguwar Ta'adarsa zata bibiyi rayuwarsa.
https://chat.whatsapp.com/I8xKHGurk7EBf5ZqQdxHKG
*MATAR MUTUM*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU MAHEER*
*FIKRA WRITERS ASSOCIATION*
*LITTAFIN KUDI NE*
*PAY 500 A ASUSUN*
*7061838488*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*MARYAM FAROUK*
*0709290797*
*ACCESS BANK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*IDAN KATINE A DAUKI HOTONSA A TURA ZUWA LAMBAR SAMA VTU KUMA A TURA A 08142548705*
*Kuyi following dina a Arewabooks @Maryamfarouk01 inda zaku karanta wannan littafin tareda sauran littattafaina*
*NAGODE*
*PAGE 24*
Rayuwa ta miqa, kwanan Binta Talatin da bakwai da dawowa daga Aikin Hajji ta haihu ta sake samun Da Namiji da yaci suna Naziru, yafi babu wai Agwai da baqin Da yanayin da ta nuna kenan domin ta gama sakankancewa da Addu'ar data ringa zagaye Ka'aba tanayi akan Allah ya bata yan Biyu Maza ta karbu to dayan ma babu laifi tunda yanzu sunyi kai daya su ukun gaba daya kowacce tana da Yaya Maza Biyu kenan, amma ba ta sare ba za kuma taci gaba da addu'a Allah badi war haka tayi yan uku ma ba biyu ba kuma duka Mazaje dan babu yanda za'ayi wata mace ya fita kaso a cikin Dukiyar da ubantane silar samunta.
Ko kaza bata zo mata barka ba daga Bechi balle suna haka sukayi bidirinsu da ita da yan uwanta se qawaye da makwafta shi kansa Audun tun bayan abubuwan da suka faru zamansu ya canza salo dan gaba daya ya daura mata laifin itace silar Rabashi da Zubaida ita kuma ta nuna sam ba haka bane ba.
Da fari bayan dawowarta ta biyeshi zaman ya zama babu dadi sedai bayan da suka tattauna da Turai da kuma sabuwar mashawarciyar da suka samu wato Basira se abubuwa suka canza daga bangarenta.
Basirar ta qara tunasar da ita cewar muddin fa tana son biyan buqata seta kwantar da kai.
Tilas ta maida kanta banza a gurin Audun, tunda har ta fahimci shi mutum ne me matuqar son girma da son a nuna ya isa to tayi amfani da wannan damar gurin kaishi matsayin da Allah be kaishi ba.
Ta ringa nuna masa nan duniya babu yashi, duk kuma abinda ze fada karta kuskura ta musa masa ta barshi akan komai yayi daidai ne baya kuskure.
"Hajiya sufa Maza kamar qananan yara suke wlh, fahimtarsu kawai zakiyi me suke so menene basa so shikenan ku zauna lafiya.
Kuma a yanzu abinda ya kamata ki mayar da kai gurin yi shine ta yanda zaki kafa kanki da Yayanki a gurinsa yanda zakiyiwa duk wata mace da zata shigo rayuwarku Zarra" Basirar ta fada taba durqusar da kai irin na shahararrun munafukai.