← Book details Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 91

Sashe 63

Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wace Ummarsu Babangida kuma?" Ta tambayeta cikin rashin fahimtar wa take nufi.
*MAMAN MARYAM ONLINE BUSSINESS*
*Ina kuke Mata Yan kwalisa , Ina nufin isassun Mata ,Wai shin Kuna da labarin shahararren company nan namu na GHT wato good healthtreatments*
*Wanda yazo muku da fitattu Kuma* *ingantatattun suppliment ,na dukkan matsalolin ku*
*Ina maisan tayi kyau,irin na isassun Mata ya fitar Miki da shef dinki tayi Miki gyara in and out ,nemi royal jelly dinmu na company GHT*
*Wanda aka yishi da xuma ,kundai San amfanin Zuma basai na fada miku ba , hajiya ta kixo ki Yi gyara domin ki kerewa sa,a kije taro ko baki da ko sisi kiji Ana rangada Miki hajiya , saboda yanda Zaki Kara kwarjini ,kina walwali acikin mutane , magungunan ght anti agen ne suna maida tsohuwa* *yarinya ,yarinya Kuma ta koma jaririya*
*Muna da magunguna iri iri*
*NA GYARAN JIKI*
*NA GOGE NANKARWA*
*NA RAGE QIBA*
*NA CIRE TUMBI*
*NA QARIN HIPS*
*NA GIRMAN BREAST*
*NA QARA TSAHON GASHI*
*NA QARIN NI'IMA WANDA ZAI SAUKAR MIKI DA NI'IMA YA QARA MIKI DADI DA ZAQI A GURIN OGA*
*Muna da hadin bita zai zai ,indai kishiyar ki tana Shan magungunan GHT, tohh lallai sunan ki sorry domin kuwa tazarar dake tsakanin ku kamar tazarar sama ne da kasa*
*Muna da Wanda zai matseki ciki da waje Andai na yayin dinki uwargida*,
*Sannan company mu na GHTBai tsaya anan ba*
*Ya kawo muku maganin dukkan matsalolin ku*
*INA MASU HAWAN JINI?*
*INA MASU CIWON ZUCIYA?*
*INA MASU CIWON QODA?*
*INA MASU CIWON HANTA?*
*INA MASU SICKLER?*
*INA MASU HIV?*
*INA MASU CANCER?*
*INA MASU NEMAN HAIHUWA?*
*Tohh Ku matso GHT taxo muku da magungunan matsalolin ku*
*Kuma muna da testimonys da yawa ,na wadanda suka gwada suka da ce*
*Munanan a KANO KUNTAU*
*Kuma muna tura Kaya ko wanne gari cikin aminci da gaskiya , kuma kayan mu muna badashi ne cikin price Mai rahusa ga kyau ga inganci sannan ga Rahusa*
*Kutuntube mu ta wannan number
08129249549*
07011401314*
"Au, Bara'atu zance miki ko zaki fi ganewa.

Juma'a idan tazo mako uku kenan da tarewarsu, kinga gida badai gida ba tamkar naku ba Birni, ai gaskiya Alhaji Audu yayi karamci ya kuma kyauta saboda dangin uban nan nata tasamma ci musu mutunchi sukayi wlh, kinsan basa son uwarta ta fa daman akace.

To yana mutuwa suka tada bala'i wai gidan da yake ciki gadonsu ne su goma ya hana a raba ya ke zaune ciki dan haka se su fitar musu a gida a raba sannan su san kasonsu, kinga dan taqin da akace sun cire musu a matsayin rabon baban nasu?

Ai badan Alhaji Audu ba a garin nan bamu san Ina Inna Hajara da yayanta zasu tsoma ransu ba shine fa ana gaya masa ya aiko aka far....."
"Ya isa haka dan Allah, kije Allah ya kaimu goben se kizo ki rakani" Binta ta dakatar da Jamila daga zubar da takeyi tamkar famfon daya lalace.

Jamilar ta fice bayan ta mata sallama tana dariya kamar wata wawiya tana fita Binta ta mayar da qofa ta rufe, wani kalar tashin hankali ke rufzo mata dukda yanayin garin babu zafi amma ita zufa ce take keto mata ta kafofin gashin jikinta.

Ta ri ga safa da marwa a dakin tana huce ita kadai tama rasa ta ina zata fara tunani, Audu ya ginawa Bara'atu gida yaushe akayi haka bata sani ba kuma akan me?

To kodai sun maida Auransu ne bata sani ba tana can gaho?

Ta jefawa kanta tambayar seta zabura a fili tace
"Kut**uba kenan ma ai kuwa da anyi yaqi duniya ni za'a yaudara a ninke baibai?"
Kukan da Naziru ya sakane ya ankarar da ita hayagagar da takeyi ta daukeshi taci gaba da zaga dakin tana jijjigashi, wato mutanen nan anyi qungurumayen munafukai, ashe da Jamila bata gaya mata ba haka zata gama zamanta ta tafi ba tareda ta samu wannan mugun labarin ba aikuwa zasuga tatura, seta nuna musu ta fisu iya tashanci wato uta zasu hadewa kai?

Tabbas Turai tayi gaskita da tace tana can Bihim zasu rabe komai a barta da zare ido gashi kuwa an fara.

Daren ranar bacci barawo ne ya saceta dakyar aiko tayishi da mafarkin wai Audu ya mutu an kwashe komai an bawa Yayan Bara'atu da Zubaida ita bata samu ba.

Da safe kuwa dakyar ta iya zama jiran Jamila da ace tasan gidanta ma da ba zata iya zaman jira ba gara taje su wuce daga can.

Wadanda suka dawo washegari son zuciya ganin yanayinta yasa suka watse dan a dare dayan ciwon qyashi da Hassadar data dorawa kanta ya zabgeta kai ka dauka kwana tayi tana gudawa.

Jamila bata zoba se bayan La'asar dalili kuwa Hashimu na gida ranar bayan ya gama Tijarata akan Zabonsa data dauka tayiwa Binta Miyar da ko dandanata batayi ba da safe da Sauda ta kai mata kayan Karin Kumallo tace ta dauke tuwon a bawa Yara.

Seda ya fita kafin ta samu ta kammala duk abinda zatayi gudun kar sukai Magriba kafin ta fito.

Tinqis tinqis se gasu a sabon gidansu Bara'atu Jamila nata zuba mata dan banzan Surutu ita ko Ruhinta da gangar jikinta suna ga su isa taga gidan da Audu ya ginawa Bara'atu.

Tun daga qofar gidan yanda aka lailayeta da fulasta tasha fenti yanayin tsari da taswirar ginin kai ba zakace a cikin Bechi yake ba.

Wani abu me daci da maiqo ya taso mata har seda ta dafe qirji tana kallon qofar gidan dake garqame da kwado alamar basa nan.

Jamila ta qarasa tana shafa qofar ta juyo ta kalli Binta da taje tunga tace
"Kinga basa nan, ko ina suka tafi se Allah amma babu komai gobe ma ranace se mu dawo" tana rufe baki sega Qanin Bara'atu ya shawo kwana ta washe baki tace
"To qila ma gasu nan kinga qaninta".

Ya qara gurin ya gaishesu a mutunce Jamila tace
"Ina mutanen gidan mun tarar qofa a rufe?

Ka ganta can ka ganeta ko Matar Alhaji Audu ce tazo muku Allah sanya Alheri".

"Ai kuwa kunyi sabani dan basu koyi Minti Ashirin da fita ba sun tafi Rano" ya bata amsa.

Ta dafe qirji tace
"Rano?

Kai sun luluqa da nisa, to kuma yaushe zasu dawo?"
"Gaskiya ban sani ba" ya bata amsa cikin qaguwa da maganarta ya fara tafiya ta tareshi tana cewa
"Aida ka bude mana to taga gidan tunda kaga ita ba mazauniyar nan bace balle ace ta sake dawowa idan sun dawo, qaraso Hajiya ya bude mana mu Shiga" ta fada tana kallon sashen da Binta ke tsaye sedai wayan bataga kowa a gurin ba.

Ta hau waige waige qanin Bara'atu me suna Isah yace
"Indai wannan Hajiar ce ai ta dade da tafiya tun sanda nace miki basa nan" daga haka shima ya wuce ya barta tsaye tana cizon yatsa.

Bawai da zuciya daya ta sanarwa da Binta wannan maganar ba so tayi ta hada bala'i ta kuma so ace sun tarar da su Bara'atun dan ta tabbatar da Binta bazatayi haquri ba se tayi musu tijara da rashin mutunchi iyakar qarfinta.

Cike take da qyashi da hassadar ya za'ayi ace dukda Bara'atu bata tare da Audu kuma taci gaba da kere masu ta kowanne fanni na rayuwa?

Shekaru Aru Aru suna zaune gidan qasa lokaci daya Audu yazo ya tadawa Bara'atu da Iyayenta ginin Jan bulo ya danqara musu gida kamar na wani sarki Alhalin su suna fama da jar laka?

Shiyasa ta kwazawa Binta maganar tunda ta lura bata sani ba yanzun ko tasan inta koma Birni wacce za'ayi se Allah ita dai fatanta Audun ya kwace gidan kawai tunda dai yana tsoron Binta.

Farar safiya Binta ta kammale kayanta tsaf tasa a nemo mata shatar mota zata tafi gida.

Goggo Fadi ta ringa tambayarta abinda ya faru data tashi tafiya gagaga haka Alhalin sati guda tace zatayi bata da abin fada mata a matsayin dalilin tafiyarta dan haka kawai ta laqawa Danta ciwo tace shine bashida lafiya gara su tafi ta kaishi Asibiti.

A wata mota da Jaki ya fita dadin hawa da saurin tafiya ta kamo hanyar Kano, ita ma din da dakyar aka samo mata ita dan masu motocin daukar kaya tuni kowa ya fita ai kuwa taji jiki kafin taje gida, baya da qafafunta sun fada dan jinjirinta kansa ya gane kurensa a wannan tafiya seda sukayi jinyar gaske ita dashi ga qarin baqin ciki ta tarar Audu baya gari seda taje gidan Turai a kwana na uku bayan taji dama dama sannan ta gaya mata ai sun tafi Legas tareda Ali zasu dakko kayansu.

"Karki tareshi da hayaniya kibishi ta siyasa idan kika gano bakin zaren sannan musan abinyi" Turai ta fada mata bayan data shaida mata zancen gidan da Audu ya ginawa su Bara'atu.

Haka kuwa akayi, tayi matuqar qoqarin boye tashin hankalinta da damuwa akan Al'amarin harya dawo daga tafiya seda ya kwana biyu ya ware gajiya kafin ta tada masa da zancen ai taga gida akace shiya ginawa su Bara'atu.

"Badan Bara'atu na gina musu gida ba nayine saboda Yarana, ya za'ayi ace da raina ban mutu ba a watsarwa da Yayana da uwarsu kayansu a waje bayan ina da halin da zan iya siye garin gaba daya ma ba iyakar gidan da suke ciki ba (kuji fariya).

Shiyasa na yanke shawarar yi musu gini na Alfarma irin wanda babu shi a kaf garin da makwafta" ya bata amsa.

Binta tayi murmushi a qoqarinta na boye tashin hankalinta tace
"Gaskiya hakane amma dai basu kyauta ba suma se kace ba yan uwa ba?
Chapter 63 · 0% Book details