Sashe 36
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bangaren Bara'atu kuwa duniyar ta mata zafi, har ta dangana da cikin dakinta bayan jefa qafa take kawai badan tasan ina take zuwa ba.
Ta zauna dabas a qasa, Balaraba da labari ya iske ta dan bata je zamanba itama ta zama kamar wata mutum mutumi saboda mamaki.
Suna haka Hadiza qanwarta ta shiga dakin ta shiga sauke kayan Bara'atun tana zubawa a Jakunkuna cikin tsananin fushi.
"Wlh se sunga sakayyar mugun abunsu a kansu, shi kuma in sha Allahu har ya mutu yana nadamar wulaqantaki butulu wanda be san Halacci ba" haka Hadizan ta ringa fada tana zuba kaya ta hade mata komai tas dan daman kayan nata ba yawa ne dasu yanzu ba ta kwashe da yawan suturunta ta kyautar kamar yanda ta saba duk sallah kuma zeyi mata dinkuna masu yawan gaske to Bana da abin yazo a zamanin binta kala uku ya mata se lokacin Bikin Saleh nan ma ya mata uku.
Hadiza ta gama hada kayan Bara'atu ta fara hade na yaran se a lokacin Balaraba ta iya bude baki tace
"Karki hada kayansu ki barsu a gidan ubansu babu inda zataje masa da Da"
"Bazan iya barin Yayana ba ba zata riqe su ba" Bara'atun ta fada tana fashewa da kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta.
A mugun fusace Balaraba yace
"Ai ko kashe su zatayi se kin barsu, wlh ba zakiyi masa wahalar yaya ba yanda ya auro ki ke kadai ki tafi su zauna a gidan ubansu kuma dole ta wahalta musu, abinda tayi miki kuma Allah na gani seya saka miki ko ba dade ko bajima se taga sharrinta a kanta da ita da yan uwan nata gaba daya".
Haka aka kwana ana maida magana, washe gari Qarfe shida motar yan Bechi ta daga, Bara'atu kuma mota daban Yakubu ya nemo ta dauketa da kayanta tare dashi da Balaraba suka tafi banda yaran dan kamar yanda Balaraba tace ta barsu shima Yakubun da Asuba daya shiga yace a kira masa Bara'atun haka ya gaya mata ta zube masa Yayansa.
Watsa watsa sukayi da Audu akan al'amarin, babu yanda beyi dashi akan ya janye furucinsa ba amma ya rantse akan baze maidata ba wannan tasa Yakubun barin gidan a cikin daren be kwana ba da Asuba kuma ya fita ya nemo mota aka balle kayan Gadon Bara'atun tas yasa aka lode su sannan ya samo qarama suka tafi a ciki zuciyarsa cike da baqin ciki da takaicin abinda Qanin nasa yayi.
Ya kuma yi rantsuwar cewar babu shi babu duk wata sabga data shafi gidan Audu.
Abin seya zamarwa Bara'atu duka biyu domin kafin su isa wanda suka fara tafiya suna kai labari kamar wutar daji ya yadu cewar hassada tasa ta kashe jariri saboda yayanta kadai take so su gaji Audu.
Mutane da abin mamaki wasu tamkar a gabansu akayi se kace wani hawan sallah haka aka cika qofar gidansu ana jiran aga ta inda zata bullo tunda ance ya saketa ta hado kayanta tana hanya, aiko da suka isa seda Yakubu ya hada da dura Ashar abinda ba halinsa ba kafin matan da sukayi dandazo suka watse da sabuwar gulmar cewa magana ta tabbata gata nan harda kayanta gaba daya da alama auran ya qare saki uku yayi mata.
Seda tayi matuqar dagaske kafin ta iya shanye wannan jarabawa.
Yanda mata suke musu zuruftu suna yada musu magana ita da mahaifiyarta har ciwo ya kwantar da Innar tata.
Babanta kuwa nasa bala'in yafi na kowa dan da farko ma cewa yayi ba zata zauna masa a gida ba.
Duk kuwa sa Yakubu ya sameshi qafa da qafa ya gaya masa komai daya faru amma mutumin nan ya hau kan qarya ya zauna ya dora mata laifi har yana cewa uwarta ce ta sakata.
Watanta biyu a gida Audu ya tattaro yaran ya aiko mata dasu, tana zaune se gani tayi ana shiga da kayansu da buhunhunan abinci ta tambayesu su dawa sukace Direban Babansu ne ya kawo su a cikin kayansu taga kudi, kudade masu yawan gaske se farar takarda da gajeran rubutu a jiki.
"Kiyi amfani dasu gurin kulawa da yarana duk wata zan ringa aiko musu da abun buqata Aminu ze kai su makaranta a nan" abinda takaddar ta qunsa kenan.
Hawaye suka wanke mata fuska, wato dagaske Audu ya cireta daga rayuwarsa kenan baze bata damar wanke kanta ba tana roqon Allah daya bayyana gaskiyar abinda ya faru badan tana so ta koma gidan Audu ba aa sedan ya cire zargin kisan kai daya dora mata a ransa.
******************************
A gidan Audu kuwa duniya sabuwa Binta ta bude ta kori Bara'atu ciwon idonta yanzu bata da wata damuwa ta samu gida ta samu Miji yanda ya kamata musamman wannan abin daya faru yasaka yake qara riritata yana lallabata da sunan tausayinta yakeji akan abinda ya faru.
Da farko da taga an bar yaran bata damu ba dan ta qulle a ranta ta samu bayi sedai yanda taga Audun ya ninka kulawar da yake musu sanda uwarsu tana nan yasa hankalinta ya tashi dan haka tasan yanda tayi Abdullahi ya tafi makarantar kwana wanda daman an gama masa shirin hakan tafiyar Bara'atu tasa Audu yace an fasa nan ta san yanda tayi ya tafi daman tare suke kwana dasu Babangida shine dawainiyarsu idan Mairo tazo ta karba babu abinda Bintan take musu se Audu na gida dan haka Abdullahi bayan tafiyar Abdullahi makaranta ya zaman yaran su kadai suke kwana a daki, sun saba ana tashinsu suyi fitsari ko basu ruwa da sauran abubuwa yanzun basu da meyi musu cikin dare haka Babannan ze tashi yayi ta koke koke sedai Audun ya sakko yaji dasu tana kwance se ta fake da cewar nauyin bacci ne da ita bama ta jiyo su, randa aka samu akasi suka mata fitsari a kwance ranar wuni zatayi yana gana musu Azaba idan ya fita in ya dawo kuma ta ringa cewa ita ta kasa gane kan yaran nan, qana na dasu amma se nunkufurci tamkar uwarsu haka suke mata duk yanda take jansu sunqi sake mata.
Ya gasgata hakan saboda ko a gabansa ta jasu basa zuwa dalili kuwa Izayar da take musu idan baya nan kuma tace in suka fada seta yanka su, daya gaji da dawainiya dasu da dare baya samun bacci ya yanke shawarar a nemo me aiki da zata ringa kwana nan kuma tace bata yarda ba qarshe dai ya yanke shawarar mayarwa da uwarsu su tunda yasan itama ba a sonta ta barsu ba Yakubu ne ya tilasta mata wanda tunda ya koma a Lagos ko sau daya basuyi magana ba, fushi yake na gaske dashi shi kuma bega abinda yayi me girman da har Yakubu da sauran yan uwansa zasuyi fushi dashi haka ba.
Basu dubi abinda ita Bara'atun ta aikata ba, idan daya bar Binta niyya tayi ta daga maganar zuwa Kotu sakin da yayiwa Bara'atu ne ya rage kaifin rigimar amma kowa be duba hakan ba laifinsa ake gani hatta da Alhaji Zakariyya Baban Bintan seda yayi masa fada sosai akan abinda yayi dukda ya fahimci da alama Alhajin be san musabbabin sakin ba.
Kwanci tashi har aka shekara da rabuwar Audu da Bara'atu a sannan kuma Binta ta sake haihuwa aka maida mata da sunan Babanta Zakariyya, rayuwa taci gaba da gungurawa, budi da Arziqi suna qara zuwarwa Audu a shekarar kuma yaje aikin Hajji tareda Yaya Baba babban Yayansu da Goggo Fadi, da Yakubu yaso suyi tafiyar amma yace ba zashi ba dan har sannan be sauka daga fushin da yayi da Audun ba, wannan dalili ya saka Audun bawa Yaya Baba kujerar ita kuma Goggo Fadi Yakubu ne yace ya biya mata, a cewarsa iyayensu Malam da Dada duk basuyi tsahon ran da zasuci arziqinsa ba dan haka yayi mata yasan zasuyi Alfahari dashi a inda yake ai kuwa taji dadi yayanta sunji dadi suka ringa masa Addu'a kamar me wannan abun da yayi ya saka Yan uwan zage jin zafinsa akan rabuwa da Bara'atu, dukda tafiyar ba'a son ran Binta akayita ba amma ba yanda ta iya tunda tana da danyan Jego a sannan haka sukaje suka dawo Audu ya koma Alhaji Audu.
Bayan dawowar Audu daga aikin Hajji ya tattara kudade daya dade yana tarawa tun bayan daya fara harkar mai.
Kaduna ya nufa dasu ya samu Alhaji Zakariyya.
Sanda Alhajin ya gama sauraron jawabinsa tsaf yana kallonsa yana murmushi.
Shikam haka nan Allah ya dora masa qaunar Audun, tamkar sun hada jini ta wani gurin.
"Da gidan Mai, da jarin dana baka duk kyautace Abdullahi shiyasa hatta da filin da sunanka aka siyeshi haka nan na baka zabin sunan da za'a sakawa Kamfaninka.
Ina fatan ya zame maka hanyar riqe kanka da Ahalinka gaba daya kuma Al'umar annabi su amfana da dukiyarka" Alhajin ya fada yana kallonsa.
Haka Audu ya dawo Kano cike da mamakin karamci irin na Alhaji Zakariyya, wannan ya saka ya qara daura aniyar kulawa da Binta domin yana ganin babu wani abu da zeyiwa Alajin ya biyashi tamkar kyautata mata.
Yanayin Budi da sana'arsa ta sakashi haduwa da sababbin Abokanai matasa masu tashen kudi kamarsa a lokacin, kamar kuma yanda rayuwa take a kowanne fanni mutum yakan hadu da Abokanai na kwarai dana banza, ya rage a karankanka kayiwa kanka Alqalanci kabi wanda Tarbiyya da dabi'arku tazo daidai to hakan ce ta faru da Audu yayi sababbin Abokanai da suka kasance Yan cikin kwaryar Birni wayayyu kuma yan Boko sun fantsama cikin harkar Man fetur domin sannan itace harka data bullo da akeyin kudi da ita a dare daya.
Alhaji Bashir da Alhaji Ali sune mutum biyu da suka fi shaquwa da Audu saboda koda tafiya ta kamasu zuwa inda suke dakko Mai tare sukeyi sannan suna wasu sabgogin Kamar fitar Kayayyaki irinsu Cocoa da Qaro zuwa qasashen dake da buqatarsu.
Wannan shawarar Audu ce dan tun yana zaman bakin rimi yakan tsince hirar ana zuwa daga waje ana siyan wadannan Abubuwa.