Sashe 4
Matar Mutum Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Audu najin wannan batu yana komawa gida ya sanarwa da Dada a wannan karon itama bata ce Aa ba tasan kuma shima mahaifinsu baze hana ba inda zaa iya samun matsala be wuci yanzu da suka tasa ba suna taya sauran yan uwansu aikin Gona amma tasan hakan baze zama wani abu ba.
Haka kuwa akayi ta damu Malam Tijjani da batun yayi na'am har yace ze samu Malam Tsalha malamin tsangayar tasu yaji kanun maganar, bayan duk shirye shiryen da suka kamata Audu da Yakubu suka bi tawagar Yaran Gari zuwa birni Almajiranci, dukda Malam Tijjani yaso iya Audu ya tafi Yakubu ya tsaya amma Audu ya kafe kaida fata se sun tafi tare saboda shirinsu na karatun Boko wanda Yakubu ya fishi buri akan abu shi neman kudi kawai yake so yaje yayi a Birni ba wani Karatun Allo kona boko ba.
Seda suka shafe wata uku a tsangayar Gwani Musa suna kuma karantar birnin na Kano, basu san inda zasu nemi Shamsu ba balle ya kaisu makarantarsu, Audu a shige shigensa yayi Abokanai anan cikin Magashi suka shaqu da wani Yaro Sa'an sa Hayatu yaron gidan da Audu yake yiwa aikace aikace ne.
Hayatu da sauran yan uwansa suna makarantar boko dan haka Audu ya nuna masa shida dan uwansa Yakubu suna sha'awar karatu kuma abinda ya fito dasu daga qauye kenan.
Hayatu ya sanarwa da Mahaifinsa wanda a lokacin suna cikin mutanen da suka karbi Boko sosai yaji dadi kwarai da wannan abu dan haka ba tareda bata lokaci ba yaje da kansa ya samu Gwani Musa ya sanar masa da buqatar su Audu tayin karatun Boko.
Da yake Malami ne me fahimta kuma shi kansa cikin yayansa akwai wadanda suke Bokon saboda yanda Sarakuna da masu kudi da suke samun damar fita Waje suke fada musu Alfanun Bokon be hanasu Audu ba, ya kafa musu sharadi dai na dole zasu cigaba da daukar Karatu, da safe suje bokonsu su dawo Yamma da dare su zauna a makaranta suyi karatun Qur'ani haka kuwa akayi su Audu suka fara zuwa makaranta shekara daya da haka yace shi ya gaji saboda Shamsu ce masa yayi idan anyi karatu za'a samu aiki a samu kudi shi kuwa kullum karatu ake dora musu bema ji ranar da za'a gama ba dan shekaru ake lissafowa Yakubu ne yayi ta tausarsa akan yayi haquri da sannu zasu kai matakin da suke buri.
Haka suka ci gaba, Yakubu na matuqar maida hankali ga Karatu yayinda Audu turanci kawai ya saka zuciyarsa ze koya saboda idan ta tabbata sun gama makaranta za'a kaisu turai kar yaje ya rasa bakin magana.
A hankali ya faratiwa Makarar asha ruwan tsuntsaye, Sadi, da aka kawosu Almajiranta tare amma shi dan Bagwai ne shiya fara nuna masa hanyar Kasuwa.
Da safe idan sun tafi Boko shida Yakubu ze zame ya tafi bakin Asibiti anan zeyi duk wani aiki daya samu, dako ne, aike, duk wani abu da zeyi a biyashi haka ya ringayi kan jiki kan qarfi dake ya saka abin a ransa kuma yana da zuciyar yi se gashi baya jin wahalar kowanne irin aiki indai ze kawo masa kudi.
Da Yakubu ya gane baya zama a makaranta yace ze gayawa Malam seya dakata da zuwa Kasuwa, cikin yan kudaden daya samu ya auno Aya da gyada ya kaiwa Matar Malam da suke kira Nene dayake suna shiri yace tayi masa gyada me gishiri da Aya me siga ya daura abarsa a Boko ya siyar a Allo ya siyar se gashi an gane shi a unguwa Audu me gyada da Aya kuma sosai yake ciniki abinsa.
Seda suka shekara biyu kafin sukaje gida, a lokacin sun fara zama samari dan Yakubu nada shekaru sha biyar Audu nada Sha uku.
Cikin yan kudaden jarinsa yayiwa Dada da qannensa harda Baffansu tsaraba.
Kowa yaji dadin yanda ya gansu, Dada ce ta ringa masa fada akan ina ya samu kudi yayi wannan siyayya be boye mata ya sanar mata da duk abubuwan da yakeyi harda zancen Boko da sukeyi shida Yakubu ya kuma qara da fada mata gaskiyar dama sa
boda ya samu damar neman kudi Yakubu kuma yayi karatu yasa sukace zasu Makarantar Allon.
A wannan karon kafin su koma seda ta sanar da mahaifinsu gaskiyar komai gudun kar wata rana ya gane yace sun hada baki sun munafurceta, da fari ya ringa fada dan sosai yake Adawa da karatun Boko har yana cewa ba zasu koma Birnin ba se kuma daga baya basu san yanda akayi ya canza ra'ayi ba da kansa yayi musu shirin komawa ya kuma yi musu nasiha tareda gargadin su tsaya a turbar Allah karsu yarda masu jajayen kunnuwa su dorasu akan wata hanya sabanin wadda Addinin Islama ya dora mu akai.
Ya sake jawa Audu kunne sosai akan banbance tsakanin Halal da Haram tunda yana zuciyar nema baze daku she shi ba, abinda ya janyo masa sakkowa harya haqura zasu koma dinma bayan sunyi magana da Hashimu dansa na biyu shiya nuna masa Alfanun abinda su Audun sukeyi tunda baya kaucewa shari'a bane.
Yace masa "Baba idan ka dubi yanda rayuwa take tafiya a kullum abubuwa qara yi mana wahala sukeyi dan abinda muke nomawa ba wadatar mu yake yi ba balle har mu samu na siyarwa muyi sauran buqatu kuma ko a cikin karkarar nan idan ka duba masu fita fatauci Abokanan mu zakaga suna samun Abun rufin asiri har su taimaka mana muma, da ace tun muna qanana kamar su muma mun tashi da wannan tunanin qila da rayuwar ta mana sauqi amma yanzu tunda Allah yasa su sun himmatu zasuyi a barsu muyita rakasu da Addu'a Aminu ma da ze bisu suje can birnin yayi Bokon koya kama sana'a kamar Audu duk da hakan yayi".
To haka su Audu suka koma ba tareda Aminu ba dan yace ba zashi ba da yake Auta ne Goggo Fadi bata takura masa ba kuma shi kadai ya rage gabanta tunda duk an aurar da Maryo da Amina Mazan ma Hashimu da Lawan sunyi Aure.
Rayuwa taci gaba da garawa Audu da Yakubu a birni, iya wuya Audu neman kudi yakeyi yana kuma riqe da hudubar Mahaifansa akan ya tsaya ga halal karya kuskura yaci abinda Allah be halasta masa ba kuma da yake a lokacin duniya na zaune lafiya cuta da bata gari basuyi yawa ba shiyasa abun yazo masa a sauqaqe.
Tun yana Dako a kasuwa ko aikace aikace har ya fara kayi nayi, ze karbi kaya ya fita dasu ya siyar ya cire ribarsa har ta kai ya hada yar tireda yana kasa kayan koi gefe gida kuma ya ajiye Baro duk wani dan itace na marmari da ake yayi a lokaci ze saro ya ringa siyarwa yan kasuwar har mamakinsa suke ganinsa yaro qarami dukda yana da baragen girma amma zafin neman sa ba duk babbaba shiyasa yayi shura a bakin Asibiti babu wanda besan AUDU BECHI ba haka suke masa inkiya da garinsu.
Duk qarshen shekara suke zuwa gida kuma duk sanda zasu tafi haka ze hada tsaraba himili duk wanda ya shafe shi seya riqe masa wani abu ya kai masa dan badaga nan ba Audu akwai kyauta kuma a wannan yanayi Girma da Wahala suka fara kwantar da mahaifinsu dukda shekarunsa basu kai ace ya kwanta tun yanzu ba amma yanda rayuwar ta faro tun quruciya jiki yana wahalar data zarce abinda ze dauka shiya janyo masa ciwo yayi masa kwaf yau lafiya gobe babu haka yasa idan zasu je gida Audu ze siyi magungunan ya tafi masa dasu da irin mayukan zafi saboda qorafin ciwon jiki da yake yawanyi.
A wannan gantafalfala suka kammala Primary tareda Saukar alqur'ani ta biye wadda Audu dai ba zuwanta yake ba a sati befi ya leqa sau daya ba ita kanta Allon Karatun dare kadai yake zama Gwani yayi fadan yayi nasihar amma Audu ya toshe kunne, dadinta daya yana biya karatu daidai ya wanke Allonsa akan lokaci wannan yasa Gwani yake daga masa qafa Bokon ma idan ana jaraba zeje yayi kuma zeci ga turancin daya saka kansa ya iya radau dan ko Yakubu me qulafucin Bokon Albarka shiyasa Malaman suke ji dashi, Audu akwai rashin ji amma akwai kwakwalawar daukar Karatu.
Yakubu ya tafi makarantar kwana dan cigaba da karatun sa, burinsa ne ya zama Alqali Audu kuwa yace yayi sallama da Boko ya kama neman kudi kuma.
Shi yayiwa Yakubu duk wani shiri na tafiya makarantar, haka kuma yana kai masa ziyara idan anyi hutu Yakubun Bechi yake tafiya yayi hutunsa acan Audu kuma ana Kano ana ta fafutukar rayuwa.
Inda ya kafa yar tiredar tasa aikin fadada titi yabi ta gun dole ya tashi daga qarshe ya koma zuba kayan kolin nasa a Baro yayi ta zaga kasuwa yana waqa ta kiran customers yanda yake waqar abin dariya yake saka wasu siya badan ma sunyi niyya ba.
Yakubu yana shekara ta uku a makaranta lokacin kuma aka aurar da Bilki wadda take bin Audu, ba qaramar Bajinta Audu yayi a auran nan ba dan dama ya dade yana tanadi saboda mutuniyarsa ce ko irin fadan sako da sakon nan basa yi da akwai fahinta sosai a tsakaninsu a kuma Bikin Bilkin ya dabbaqa soyayyarsa ga Bara'atu wadda tayiwa Bilki babbar qawa.
Tun suna yan yara Audu yake sonta an dauka yarinta ce ashe shi har ransa ya riqe abun yanzun daya furta yana son ta da yawa wasa suka dauki abun saboda idan ka dubi a yanda akewa yara aure Bara'atu ta isa kaiwa daki dukda shekarunta sha biyu ne a sannan amma ga Bilki da take sa'arta an mata aure itama Audu kuwa yana shekara sha bakwai koda Maza suna saurin Aure a qauyen amma be isa ba tukunna, ga Yakubu me sha tara da Aminu me Ashirin da biyu nan basuyi aure ba bare Azo kansa haka dai ya ringa hurewa Bara'atu kunne da soyayyarsa seda ya tabbata ta mato ta yanda ko ya koma birni ba zata saurari wani ba zata jira shi kafin ya koma Birni ya bar Audu da suke hutun makaranta zasu shiga Aji hudu a sannan.